Wace rawa Matawalle zai taka a yunƙurin ceto ɗaliban Kebbi?

Asalin hoton, Bello Matawalle/X
Tun bayan umarnin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bai wa ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle na komawa jihar Kebbi domin taimaka wa yunƙurin ceton ɗaliban da ka sace, ƴan ƙasar ke ta magana kan irin da rawar da zai taka.
A ranar alhamis ne Shugaba Tinubu ya umarci Bello Matawalle ya koma jihar - da ke arewa maso yammacin Najeriya - domin sanya idanu kan ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi na ceto ɗaliban.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ministan zai isa jihar Kebbi a yau Juma'a b isa umarnin shugaban ƙasa.
Tun farko shugaba Tinubu ya aika mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima zuwa jihar domin jajanta wa iyayen ɗaliban tare da ganawa da al'umar yankin da kuma bayyana musu irin matakan da gwamnati ke ɗauka ]wajen kuɓutar da ɗaliban.
A farkon wannan mako ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga makarantar Sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar tare da sace ɗalibai 25.
Hukumomi sun ce biyu daga cikin ɗaliban sun kuɓuta daga hannun ƴan bindigar inda suka koma gida.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya zargi hukumomin Najeriya da gaza taɓuka komai yayin da "ake yi wa Kiristoci kisan gilla."
Sai dai bayanin da hukumomi suka fitar ya na sunayen ɗaliban ya nuna cewa dukkaninsu Musulmai ne.
Gwamnatin Najeriya ta dage kan cewa matsalar tsaro a ƙasar na shafar dukkanin al'ummar ƙasar ba tare da la'akari da addini ba.
Rawar da ministan zai taka

Asalin hoton, Bello Matawalle
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce Matawallen na da gogewar yaƙi da satar ɗalibai a makarantu kasancewar an sha sace ɗalibai a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara, tsakanin 2019 zuwa 2023.
Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun shugaba Tinubu ya shaida wa BBC cewa, idan ministan ya isa Kebbi zai yi aiki ne tare da sauran jami'an tsaron da suke can.
''Baya ga jami'na tsaron da ke jihar, Bello Matawalle zai kuma yi aiki tare da gwamatin jihar da dai sauran jami'an tsaron da suke can wajen wannan aiki na ganin an ceto waɗannan yara."
"Ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ma shugaban ƙasa ya umarci ministan tsaron wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara da ke maƙwabtaka da Kebbin da ya je can ɗin shi ne saboda yana da fahimta sosai a kan irin wannan aiki''.
Mallam Abdul'aziz ya ce bisa la'akari da abin da ya faru a lokacin da ya ke gwamnan Zamfara, lokacin da ƴanbindiga suka sace ɗalibai kusan 300 a makarantar kwana ta Kankara shi ne ya shiga ya fita da kuma taimakon Allah har aka samu aka saki ɗalibai ba tare da lokaci ba.
"Wannan fahimta da kuma ƙwarewar da ya ke da ita na irin wannan aiki shi ya sa shugaba Tinubu ya ba shi wannan umarni na zuwa jihar Kebbi don ceto wadannan dalibai," in ji Abdul'aziz Abdul'aziz.
Ƴanbindigar dai sun shiga makarantar ɗaliban ne da asubahin ranar Litinin 17 ga watan Nuwamba, lokacin da ɗaliban ke shirin tashi sallar asuba inda suka kashe wani mai gadi, tare da yin awon gaba da ƴan matan.
Bayanai sun ce maharan sun far wa makarantar ɗauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kafin daga bisani su tafi da ɗaliban.
Shugaban Ƙaramar hukumar Danko/Wasagu,inda makarantar ta ke, Hon. Hussaini Aliyu Bena ya ce maharan sun je makarantar ne a ƙafa ba a kan babura ba, kamar yadda suka saba kai hare-hare a yankunan.
Ya kuma danganta harin da yadda wasu al'umomin Zamfara da suka yi iyaka da ƙaramar hukumar suka yi sulhu da ƴanbindiga.
Iyayen ɗaliban makarantar Sakandiren Ƴanmata ta Maga - da ƴan bindiga suka sace - na cikin ɗimauta tun bayan sace ƴaƴan nasu.
Ɗaya daga cikin iyayen yaran, wanda BBC ta tattauna da shi ya bayyana baƙin cikin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan faruwar lamarin.











