Kukan da matata ke yi ya hana ni zama a gida - Mahaifin ɗalibar da aka sace

Wani mutum zaune

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Iyayen ɗaliban makarantar Sakandiren Ƴanmata ta Maga - da ƴan bindiga suka sace - na cikin ɗimauta tun bayan sace ƴaƴan nasu.

Da asubahin ranar Litinin ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka far wa makarantar kwanan da ke garin Maga na yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, inda suka sace wasu ɗaliban.

Hukumomi a jihar ta arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da sace ɗalibai 25 tare da kashe wani malami da kuma maigadin makarantar, a lokacin harin.

Wannan al'ummari ya jefa iyayen ɗaliban musamman waɗanda aka sace cikin ɗimauta da rashin sukuni sakamakon rashin sanin halin da ƴaƴan nasu ke ciki.

Ɗaya daga cikin iyayen, wanda BBC ta tattauna da shi ya bayyana baƙin cikin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan faruwar lamarin.

'Yadda labarin ya zo min'

Mahaifin - wanda muka sakaya sunansa ya ce - bayan sallar asuba ya samu labarin abin da ke faruwa.

''Bayan mun idar da sallar asuba, muna zaune cikin masallacin sai aka kira limaminmu a waya aka sanar da shi sace wasu ɗalibai a makarantar ƴanmata'', in ji shi.

Mutumin - wanda ke magana cikin murya ta kaɗuwa - ya ce tun daga nan jikinsa ya riƙa rawa ya kuma nufi makarantar domin sanin halin da ƴaƴansa biyu ke ciki.

Lambar makarantar

Asalin hoton, Mustapha Ibrahim/BBC

'Yadda aka sace ta'

Mahaifin ya ce a shekarar da ta gabata ya kai ƴar tasa makarantar, wadda a yanzu take aji biyu a makarantar, sai kuma ƙanwarta da ke aji ɗaya.

''Ƙanwar tata ta shaida min cewa suna kwance sai ɓarayin suka shiga ɗakin kwanan ɗalibai, daga nan sai su biyu suka ruga suka shiga banɗaki suka kulle ta ciki, wasu kuma suka shiga ƙarƙashin gadaje, domin neman wurin ɓuya''.

''Bayan sun kulle kansu a banɗaki, sai ƴanbindigar suka ce duk wadda ba ta fito daga inda ta ɓuya ba, idan suka buɗe za su harbe ta'', kamar yadda ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa bayan da ta ji wannan gargaɗi sai ta tsorata ta buɗe ƙofar banɗakin ta fita, ƙanwar tata kuwa ta ƙi fita.

''Daga nan ne suka tafi da ita, tare da sauran yaran da suka tara'', in ji mahaifin.

'Kukan mahaifiyarta ya hanani zaman gida'

Mahaifin ya ce tun bayan faruwar lamarin shi da mahaifiyar ƴar tasa sun kasa sukuni, sun ma rasa me yake musu daɗi.

''Wallahi mahaifiyarta da mun haɗa ido ba abin da take yi sai kuka, abin yana damu na', kamar yadda ya bayayan kafin ya ɓarke da kuka.

Bayan da wakilin BBC ya ba shi haƙuri, mahaifin yarinyar ya ce duka danginsa sun taru a gidan kuma ba abin da suke yi da sun kalle shi sai kuka.

Ya ci gaba da cewa yawan kukan da matarsa (mahaifiyar yarinyar) ke yi na hana shi zaman gidan nasa, saboda tausayi.

Wasu rububin takalma

Asalin hoton, KOLA SULAIMON/AFP via Getty Images)

'Ita ce ƴarmu ta fari'

Mahaifin ya ce ƴar tasa mai shekara 13, ita ce babba a cikin ƴaƴansa.

''Yarinyar ita ce ƴarmu ta fari, kuma duka cikin ƴaƴana babu mai kyawawan halayenta da haƙurinta da gaskiya'', in ji shi

Ya ƙara da cewa ƴar tasa yarinya ce mai sauƙin kai.

'Baƙin cikina ban san halin da take ciki ba'

Mahaifin - wanda ya ɓarke da kuka - ya ce tun da ya haifi yarinyar ba ta taɓa kwana a wani wuri ba, in ba makaranta ba, sai gida.

''To ni yanzu babban tashin hankali na shi ne an wayi gari ba ta hannuna, ban kuma san halin da take ciki ba'', kamar yadda ya bayyana cikin hawaye.

Ya ƙara da cewa ya kasa barci saboda irin halin ruɗanin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan sace yar tasa.