Yadda gushewar jemage ke janyo mutuwar yara a Amurka

Asalin hoton, SPL
Masu bincike a Amurka sun alakanta mutuwar yara fiye da 1300 ga karuwar amfani da magungunan kwari a arewacin Amurka.
Sun ce hakan ya biyo bayan rashin jemagun da aka yi a 2006.
Yawanci jemagun dai na maganin kwari da kansu ta hanyar cinye kudin cizo, to amma tun bayan lokacin da suka bace sakamakon wata kwayar cutar da ta yi musu illa, manoma suka fara neman maganin kwari don kare shukarsu daga illar kwarin.
Masu binciken sun ce yawancin magungunan kwarin da ake amfanin da su na gurbata ruwan sha,sannan kuma iskar da ake kadawa ta kara janyo mutuwar yara jarirai a cikin shekaru 10 saboda ta na kwaso warin maganin kwarin da ake sanyawa a gonaki.
Binciken ya nuna cewa iyaye matan da ke dauke da juna biyu na shakar iskar da ke kwaso magungunan kwarin wanda hakan illa ce a gare su, da ma abin da suke da shi.
A watan Yunin 2024, wani bincike ya nuna gushewar ungulu a Indiya ya haifar da mutuwar mutane da dama saboda babu tsuntsuwar wadda ke cinye rubabban nama da beraye da kuma sauran abubuwa makamantansu.
Binciken ya bayyana cewa ci gaba da samun karewar dabbobi da wasu nau'in kwari da tsuntsaye a sassan duniya na janyo wa mutane illa da dama wanda yawanci ba a sani ba.
A don haka binciken ya ce ya kamata a rinka kula da amfanin duk wata dabba ko tsuntsu ga dan’adam.













