Me ya sa Sheikh Gumi ya damu a sasanta da ƴan bindiga?

..
Lokacin karatu: Minti 3

A ƙarshen makon nan ne aka yi ta samun masu kiraye-kirayen cewa hukumomin tsaron Najeriya su kama fitaccen malamin addinin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi bisa zargin sa da masaniyar abubuwan da ƴan bindiga ke aikatawa.

Wannan dai ya biyo bayan sake nanata buƙatar sulhu da ƴan bindiga da Shehun malamin ya yi a ƙarshen makon.

Sai dai kuma Sheikh Gumi ya ce shi ba ya tsoron a kama shi saboda ganawar da yake yi da ƴan bindiga "a ƙoƙarin samar da tsaro a Arewacin Najeriya."

Gumi dai ya sha nanata buƙatar tattaunawa da ƴan bindiga da ya ce ita kaɗai ce hanyar warware matsalar, saɓanin amfani da ƙarfin tuwo a kansu.

Dalilin da ya sa na damu - Sheikh Gumi

..

Asalin hoton, Sheikh Gumi/Facebook

A shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya ce masu kiran a kama shi saboda ƙoƙarinsa na samar da sasanci "jahilci" ne ke damun su irin wanda ke damun ƴan bindiga.

"Da a ce suna ganin irin haɗarin da muke shiga domin mu sadu da waɗannan ƴan bindiga da yaba mana za su yi maimakon baƙanta mu."

Dangane kuma da dalilin da ya sa ya malamin yake yawan nuna damuwarsa da al'amarin ƴan bindiga ya ce saboda yadda matsalar ke cutar da Arewacin Najeriya.

"Mu ƴan arewa mu ne abin ya shafa kuma mu ne ake cutarwa domin an hana mu noma da korar wasu daga garuruwansu. Saboda haka irinmu mu zuba ido wannan abu na faruwa ba mu yi wa al'umma da gwamnati adalaci ba.

"Shi ya sa muke kutsawa cikin daji tare da ƴan gwamnati amma na gefe ba su san da gwamnati muke aiki ba. Wannan ne ya sa kamar muna da alaƙa da ƴan bindiga. Muna ƙoƙarin nuna musu kuskurensu ne sannan mu ilmantar da su tunda mun fahimci ba ma su da ilimin addini," in ji Gumi.

Matsayar Sheikh Gumi

..

Asalin hoton, Sheikh Gumi/Facebook

Bayanan hoto, Sheikh Gumi a daji tare da wasu ƴan bindiga yayin sulhu a shekarun baya.

Sakamakon yadda aka yi wa shehun malamin ca a ƙarshen mako, ya ƙara nanata tunanin da yake da shi wajen warware matsalar ƴan bidiga a arewacin Najeriya, inda ya wallafa wani ƙaramin sako a shafin nasa na Facebook.

"Hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen ta'addanci ita ce bai wa ƴan bindiga ilimi da sanya musu imani tare da fata mai kyau."

Sheikh Gumi ya kuma ƙara da cewa "wani kaso na tiriliyoyin da ake kashewa kan tsaron zai samar da waɗancan abubuwan."

Shawarwari huɗu ga Sheikh Gumi

Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce malaman addini suna da rawar da za su taka wajen wanzar da zaman lafiya to sai dai ya ce akwai kuskuren da malamin yake yi da ke janyo masa surutai da zarge-zarge.

" A cikin tsari da ake da shi a tsaro shi ne buƙatar sirranta al'amura saboda ba komai ba ne da za ka yi za ka fito ka faɗa saboda gudun tuggu da waɗanda ba sa son abin da kake yi. Wannan shi ne kuskuren malam na farko wato yadda yake fitowa kai tsaye yana ambatar ababen da yake yi."

Malam Kabiru ya lissafa wasu shawarwari da ya ce ya kamata Sheikh Gumi ya runguma domin samun nasara a ƙoƙarinsa na wanzar da zaman lafiya.

  • Yin abubuwa a cikin sirri
  • Samun yarjejeniya a rubuce: A duk lokacin da za a yi irin wannan yarjejeniya tsakaninsa da hukuma to ya tabbatar an yi komai a rubuce domin shiryawa abin da zai biyo baya.
  • Ka da ya karɓi kuɗi domin bai wa ƴan bindiga
  • Ya kamata malam ya rinƙa tuntuɓar masana harkar tsaro