Yadda ƴan Indiya ke sayar da rayukansu domin zuwa Amurka

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Soutik Biswas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a Indiya
- Lokacin karatu: Minti 7
A watan Oktoba, hukumar shige da fice da kuma ta kwastam a Amurka ta aika wani jirgi ɗauke da ƴan ƙasar Indiya zuwa gida, abin da ya ƙara irin yawan mutanen da ake mayar wa zuwa Indiya.
Wannan jirgin ba shi ne kaɗai ba - yana ɗaya daga cikin manyan jirage da suka ɗauki mutane a wannan shekara, kowanne ɗauke da fasinjoji 100. Jiragen na mayar da dandazon ƴan ci-ranin Indiya waɗanda ke zaune a Amurka ba bisa ka'ida ba.
A cewar jami'an Amurka, jirgi na baya-bayan nan ɗauke da mata da maza ya tsaya a Punjba, kusa da wuraren da yawancin ƴan ci-ranin suka fito.
A shekarar kuɗi ta Amurka ta 2024 wadda ta kare a watan Satumba, sama da ƴan Indiya 1,000 ne aka mayar zuwa gida at hanyar amfani da jiragen yawo, a cewar mataimakiyar sakatare a sashen kula da harkokin tsaro na cikin gida a Amurka, Royce Bernstein Murray.
"Ana ci gaba da fitar da ƴan Indiya daga Amurka zuwa gida a cikin shekaru da suka wuce, abin da ya yi iri ɗaya da wanda muka gani dangane da ƴan asalin Indiya a cikin shekaru da suka gabata," kamar yadda Ms Murray ta faɗa wa taron manema labarai.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da Amurka ke ƙara yawan ƴan ci-ranin Indiya da take mayar wa gida, fargaba na ƙaruwa kan yadda tsarin shige da fice na zaɓaɓɓen shugaba Donald Trump zai shafe su. Trump ya riga ya ɗauki alkawarin ƙorar ƴan ci-rani da ba a taɓa gani ba a tarihi.
Tun watan Oktoban 2020, jami'an hukumar kwastam da kuma tsare kan iyakoki a Amurka sun tsare kusan ƴan ci-rani 170,000 daga Indiya, waɗanda suke ƙoƙarin tsallaka kan iyaka ba bisa ka'ida ba a iyaka da ke arewaci da kuma kudanci.
"Duk da cewa sun yi kaɗan idan aka kwatanta su da Latin Amurka da kuma yankin Caribbean, ƴan ci-ranin Indiya sun kasance mafi girma a yankin yamma waɗanda jami'an na CPB suka gani a ciki shekara huɗu, a cewar wata cibiyar bincike a Washington.
Zuwa 2022, an yi kiyasin cewa ƴan ci-ranin da ke zama ba bisa ka'ida ba sun kai 725,000 a Amurka, abin da ya janyo suka zama na uku mafi girma bayan na Mexico da kuma El Salvador, a cewar sabbin alkaluma daga cibiyar bincike ta Pew.
Ƴan ci-rani da ke zama ba bisa ka'ida ba sun kai kashi 3 na ɗaukacin al'ummar Amurka kuma kashi 22 na waɗanda aka haifa a ƙasar ƴan asalin waje.
Idan muka dubi alkaluman, Mista Guerra Ms Puri sun bayyana abin da ya janyo ƙaruwa a yawan ƴan Indiya da ke ƙoƙarin tsallakawa ba bisa ka'ida ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ga ɗaya, ƴan ci-ranin masu abu a hannu ne. Sai dai duk da haka ba za su iya samun bizar yawon buɗe ido ko kuma ta ɗalibai zuwa Amurka, so tari saboda rashin isasshen ilimi ko kuma turanci mai kyau.
Maimakon haka, sun dogara ga wasu hukumomi da ke karɓar kuɗi da ya kai dala 100,000, wani lokacin kuma suna bin hanyoyi masu nisan zango domin kauce wa jami'an tsaron kan iyaka.
Domin samun damar zuwa Amurka, wasu da yawa na sayar da gonakinsu ko kuma cin bashi. Babu mamaki, alkaluma daga kotun hukumar shige da fice ta Amurka a 2024 ya nuna cewa yawancin ƴan ci-ranin Indiya maza ne, waɗanda ba su haura shekara 18-34 ba.
Na biyu, Canada da ke iyaka a arewaci ta zama hanya mafi sauki da ƴan Indiyan ke samun wurin shiga Amurka, inda bizar da ake bai wa baki ke kai kwanaki 76 kafin a samu (idan aka kwatanta da shekara ɗaya na samun bizar Amurka a Indiya).
Jami'an tsaron kan iyaka - da ke kula da jihar Vermont da kuma larduna a birnin New York da New Hampshire - sun fuskanci ƙaruwar shigar ƴan ci-ranin Indiya tun farkon wannan shekara, inda suka kai 2,715 a watan Yuni, kamar yadda masu bincike suka gano.
Tun da farko, ƴan ci-rani daga Indiya na shiga Amurka ne ta iyakar kudanci da Mexico mai cike da cunkoso zarcewa a El Salvador ko kuma Nicaragua.
Kafin watan Nuwamban bara, ƴan Indiya na samun bizar tafiye-tafiye kyauta zuwa El Salvador.

Asalin hoton, AFP
"Iyakar Amurka da Canada na da tsawo sosai kuma ba shi da tsaron da ya kamata idan aka dubi iyakar Amurka da Mexico. Kuma duk da cewa ba shi da isasshen tsaro, ƙungiyoyin ƴan bindiga ba su yi masa ƙawanya ba kamar yadda suka yi wa hanyar kudanci da kuma tsakiyar Amurka," in ji Mista Guerra da Ms Puri.
Na uku, yawancin ƴan ci-ranin da ke shiga Amurka daga Indiya sun fito ne daga mabiya addinin Sikh da suka fi rinjaye a jihar Punjab da kuma Haryana mai makwabtaka, inda ake ganin mutane da ke tsallakawa zuwa ƙasashen waje.
Ɗaya wurin kuma da suke fitowa shi ne jihar Gujarat, mahaifar Firaiministan Indiya Narendra Modi.
Punjab, wadda ke da yawan ƴan ci-rani, na fuskantar matsin tattalin arziki, ciki har da ƙaruwar rashin aikin yi da rashin kyawun amfanin gona da kuma safarar kwayoyi.
Tafiya ci-rani dai ba sabon abu bane a tsakanin ƴan Punjab, inda matasa da ke zaune a ƙauyuka ke hankoron ganin sun fita waje.
Wani bincike a baya-bayan nan da aka gudanar a Punjab, ya gano cewa kashi 56 da suka kasance ƴan shekara 18-28 sun tafi ci-rani, yawanci bayan kammala makarantar sakandari. Wasu da dama su suka ɗauki nauyin tafiyarsu yayin da wasu kuma suka ci bashi, daga baya suka riƙa aika wa iyalansu kuɗi a gida.
Akwai kuma ƙaruwar fargaba kan ƴan awaren Khalistan, wadda ke neman kafa ƙasa ta daban ta mabiya addinin Sikh.
"Wannan ya janyo tsoro daga wasu mabiya addinin Sikh a Indiya kan yiwuwar kame daga hukumomi ko ƴan siyasa. Wannan fargabar na iya ba da tabbataccen tushe na cin zali da zai ba su damar neman mafaka, ko da ba gaskiya bane, "in ji Ms Puri.

Amma tantance ainihin abubuwan da ke haifar da batun ci-rani yana da matukar wuya.
"Yayin da abubuwan karfafa gwiwa suka bambanta, damar tattalin arziki shi ne babban jigo, wanda shafukan sada zumunta ke karfafawa da kuma alfahari da samun 'yan uwa da ke zaune a Amurka," in ji Ms Puri.
Na huɗu, masu bincike sun gano wani canji a cikin kididdigar iyali na 'yan Indiya a kan iyakoki.
Wasu ƙarin iyalai na ƙokarin ketare iyaka. A cikin 2021, an tsare manya marasa aure da yawa a kan iyakokin biyu. Yanzu, rukunin iyalai sun kai kashi 16-18 na waɗanda aka tsare a iyakokin.
Wannan ya haifar da mummunan sakamako. A watan Janairun 2022, wani iyali mai mutum huɗu daga Indiya - wani ɓangare na rukunin mutane 11 daga Gujarat - sun mutu bayan daskarewa daga nisan kilomita 12 daga kan iyaka a Kanada yayin ƙoƙarin shiga Amurka.
Pablo Bose, masanin ƙaura da nazarin birane a Jami'ar Vermont, ya ce da yawan Indiyawa na ƙoƙarin tsallakawa zuwa Amurka ne saboda samun ƙarin abin dogaro da "shiga cikin biranen Amurka", musamman ma manya kamar New York ko Boston.

Asalin hoton, Getty Images
“Daga dukkan abubuwan da na sani da kuma tattaunawa da mutane da na yi, yawancin ƴan Indiya ba sa zama a wurare kamar Vermont ko New York, maimakon haka suna tafiya zuwa cikin birane da zarar suka samu damar haka," kamar yadda Mista Bose ya faɗa wa BBC. A can, ya ce suna samun yin aikatau da kuma aiki a shagunan sayar da abinci.
Alamu na nuna cewa abubuwa za su ƙara yin wuya nan ba da jimawa ba. Wani kwararren jami'in shige da fice Tom Homan, wanda zai jagoranci ɓangaren shige da fice na ƙasar Amurka idan Trump ya karɓi mulki a watan Janairu, ya ce za a fi mayar da hankali kan iyakar arewaci a Canada saboda ƴan ci-rani da ke shiga ba bisa ka'ida ba a yankin "babbar batun tsaro ne na ƙasa".
Ba a dai san me zai faru nan gaba ba. "Za a zuba ido don ganin ko ita ma Canada za ta saka irin wannan tsari domin hana mutane tafiya ci-rani zuwa Amurka daga iyakokinta. Idan haka ta faru, za mu yi tsammanin raguwar ƴan Indiya da ake tsarewa a iyakar," in ji Ms Puri.
Ko ma mai ya faru, dubban mutane daga Indiya da ke tafiya zuwa Amurka domin samun rayuwa mai kyau zai yi wuya ya ragu, duk da cewa hanyar da suke bi na ƙara zama mai haɗari.










