Waiwaye: Alƙawuran Tinubu ga ma'aikata, Ganduje shugaban APC

Kamar kowane mako, wannan maƙala na ɗauke da wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke yin bankwana da shi.

Zanga-zangar 'yan ƙwadago: Tasiri ko akasin haka?

Duk da raɗe-raɗin janyewa ko kuma fuskantar cikas kafin wayewar gari, 'yan ƙwadago a Najeriya sun yi nasarar gudanar da zanga-zangar da ta karaɗe faɗin ƙasar a ranar Laraba.

Babbar manufarsu ita ce nuna adawa da cire tallafin man fetur wanda suka ce shi ne ummul-aba'isin tsadar rayuwa da hauhawar farashin da ba a taɓa ganin irinsa ba cikin 'yan shekarun nan a Najeriya.

Ba a dai ga wani yunƙuri daga masu zanga-zangar na tunkarar fadar shugaban ƙasa da buƙatun da suka ce, su ne ke ci musu tuwo a ƙwarya ba, duk da yake a wasu jihohi, sun kai ƙorafi ga gwamnoni.

Ƙololuwar zanga-zangar shi ne lokacin da shugabannin ƙwadago suka jagoranci mambobinsu zuwa harabar Majalisar Dokoki ta Tarayya, lamarin da ya kai ga ja-in-jar da ta karya ƙofar shiga majalisa.

Tun a jajiberen wannan zanga-zanga, rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargaɗi ƙungiyoyin ƙwadagon da cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kai ga tashin hankali ba.

Alƙawuran da Tinubu ya yi na rage raɗaɗin cire tallafin mai

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ma'aikatan ƙasar alƙawarin cewa nan gaba kaɗan gwamnatinsa za ta ƙara musu albashi, kamar yadda ya bayyana cikin jawabinsa a yammacin Litinin.

Kazalika ya sake cin alwashin ɓullo da matakan sauƙaƙa wa 'yan ƙasa raɗaɗin da suke ji na cire tallafin man fetur, wanda ya ce "wasu mazambata ne ke amfana da shi".

"A cikin wata biyu, mun adana sama da naira tiriliyan ɗaya na tallafin mai da ake kashewa kan abin da babu riba kuma 'yan sumoga da mazambata ke amfana," kamar yadda ya bayyana.

Cikin jawabin da ya gabatar na minti 20 ta kafar talabijin ɗin gwamnatin ƙasar, Tinubu ya nemi 'yan Najeriya su ƙara haƙuri.

Cikin matakan da gwamnatin ta Tinubu ɗauka, akwai ba da umarnin rarraba tan 200,000 na hatsi a faɗin ƙasar don a sayar kan "sassauƙan farashi".

Sai dai jawabin shugaban bai taɓo batun soke tsauraran sharuɗɗa ba game da dokar bayar da bashin kuɗin karatu, wanda gwamnatinsa ta ba da sanarwa jim kaɗan kafin ya fara jawabin.

Abdullahi Ganduje ya zama shugaban APC

A ranar Alhamis jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugabanta na riƙo.

Hakan na zuwa ne bayan matsayar da aka cimma a taron shugabannin jam'iyyar da aka yi.

Da ma tun kafin tabbatar wa tsohon gwamnan na Kano da muƙamin, akwai rahotannin da ke cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya zaɓe shi domin karɓar muƙamin.

Ganduje ya karɓi muƙamin ne a lokacin da ake ganin jam'iyyar na fuskantar manyan ƙalubale.

Har yanzu ana ci gaba da raɗe-raɗi game da dalilan da suka sanya tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu ya ajiye muƙamin rana tsaka.

Amma bayanai masu ƙarfi sun tabbatar da cewa ya sauka ne sanadiyyar rashin jituwar da ke tsakaninsa da wasu jiga-jigan gwamnatin Shugaban Bola Ahmed Tinubu.

Cire sunana daga ministoci ƙaddara ce daga Allah - Maryam Shetty

Cikin wani dogon saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, Maryam Shetty ta ce ba za ta iya bayyana irin farin cikin da ta ji ba lokacin da ta ga sunanta cikin jerin mutanen da ake son nadawa a matsayin ministocin kasar.

A cewarta, hakan alama ce da ke nuna cewa a shirye Najeriya take wajen tabbatar da kyakkyawar makomar mata musamman matasa kamarta.

To sai dai Shetty ta ce ƙaddara ce ta yi tasiri wajen cire sunanta daga jerin sunayen.

Ta ce: ''Wasu na ganin hakan tamkar wani koma-baya ne a gare ni, amma ni a matsayina na Musulma na yarda da ƙaddara, na ɗauki hakan a matsayin ƙaddara daga Allah, wanda shi ke bayar da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so''.

Tinubu ya sanar da Majalisa aniyar tura dakarun Najeriya zuwa Nijar

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa majalisar dokokin Najeriya matsayar da ƙungiyar Ecowas ta cimma kan ɗaukar matakin soji a kan Nijar da kuma sauran takunkuman da aka ɗauka na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.

Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya sanar da saƙon shugaban ƙasar inda ya karanto kai-tsaye daga wasikar Shugaba Tinubu.

Wasikar na cewa: “Bayan abin takaicin da ya faru a Nijar inda aka hamɓarar da shugaban ƙasa, Ecowas a ƙarƙashin jagorancina ta yi Allah-wadai da juyin mulkin kuma ta amince da ɗaukar matakan dawo da Nijar kan turbar dimokuraɗiyya. A wani mataki na dawo da zaman lafiya a ƙasar Ecowas ta fitar da matsaya.

“Za a rufe duk iyakokin Nijar da ƙasashenmu da kuma sanya ido don tabbatar da cewa an yi biyayya ga matakin.

“Yanke wutar lantarkin da ake kaiwa Nijar da neman goyon bayan ƙasashen duniya wajen aiwatar da matsayar ƙungiyar Ecowas da kuma datse sufurin jirgin sama daga cikin Nijar da ma wanda zai shiga ƙasar.

“Rufe hanyoyin shigar da kaya Nijar daga Legas da kuma wayar da kan ƴan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta game da shirin ɗaukar matakin soji a kan sojojin Nijar ɗin.''

Tantance ministocin Tinubu

A ranar Laraba Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa ƙarin sunayen mutum 19 don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa.

Sunayen ƙari ne a kan waɗanda fadar shugaban ta aika a Litinin ɗin makon da ya gabata na mutum 28, inda jimillarsu ta zama 47.

A ranar Litinin da ta wuce sanatocin suka fara zaman tantance mutanen, inda zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ake ci gaba da aikin tantancewar.

Cikinsu akwai tsofaffin gwamnoni bakwai tara da mata bakwai.