Manyan ƙalubale huɗu da ke gaban Ganduje

    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

A ranar Alhamis jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugabanta na riƙo.

Hakan na zuwa ne bayan matsayar da aka cimma a taron shugabannin jam'iyyar da aka yi.

Da ma tun kafin tabbatar wa tsohon gwamnan na Kano da muƙamin, an shafe kwankai da dama ana raɗe-raɗin cewar shugaban ƙasar Bola Tinubu ya zaɓe shi domin karɓar muƙamin.

Ganduje ya karɓi muƙamin ne a lokacin da ake ganin jam'iyyar na fuskantar manyan ƙalubale.

Har yanzu ana ci gaba da raɗe-raɗi game da dalilan da suka sanya tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu ya ajiye muƙamin rana tsaka.

Amma bayanai masu ƙarfi sun tabbatar da cewa ya sauka ne sanadiyyar rashin jituwar da ke tsakaninsa da wasu jiga-jigan gwamnatin Shugaban Bola Ahmed Tinubu.

To amma waɗanne ƙalubale ne ake ganin za su fi girma a lokacin shugabancin Ganduje na jam'iyyar APC?

Rarrabuwar kan ƴaƴan jam'iyya

Rarrabuwar kan da ke a jam'iyyar ta APC na daga cikin abubuwan da ake ganin sun yi sanadin ajiye aikin Sanata Abdullahi Adamu.

Tun gabanin babban zaɓen ƙasar na 2023, kawunan ƴaƴan jam'iyyar sun rabu.

Ta kai ga cewa an zargi wasu ƴaƴan jam'iyyar da rashin goyon bayan Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake takarar kujerar shugaban ƙasar.

Wannan ɓaraka ta fito ƙarara bayan da wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar suka garzaya kotu domin nuna adawa da wasu daga cikin manufofin tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Sun yi zargin cewa an ɓullo da manufofin ne domin yin zagon ƙasa ga nasarar Bola Tinubu.

Wannan rarrabuwar kawuna ta kai har bayan zaɓen shugaban ƙasa.

A lokacin rabon muƙaman shugabancin Majalisar Dokokin Tarayya, an ambato tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu na cewa an raba muƙaman ne ba tare da masaniyar shugabancin jam'iyya ba.

Haka nan akwai wasu ƴaƴan jam'iyyar ta APC da ke ganin bai kamata a ɗauke muƙamin shugaban jam'iyyar daga yankin arewa ta tsakiyar ƙasar ba, inda daga nan ne tsohon shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya fito.

Saboda haka ne masana harkar siyasa kamar Farfesa Kamilu Fagge, malami a jami'ar Bayero da ke Kano, ke ganin cewa wannan na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da sabon shugaban na APC zai ci karo da su.

Kuma a cewar wasu masu sharhi, idan har Ganduje ya samu nasarar haɗa kan ƴab jam'iyyar mai mulkin Najeriya a daidai wannan lokaci, to tabbas za a iya cewa ya fara da ƙafar dama.

Dakushewar farin jinin jam'iyya

Farfesa Kamilu Fagge ya ce Ganduje "Ya zo a lokacin da shugaban ƙasa ya yi ƙuduri wanda ya ɓata suna da martabar jam'iyyar a idon talaka.

"Wato janye tallafin mai wanda ya jefa mutane cikin halin ha'ula'i, ga kuma talauci da yunwa da hauhawar farashi a cikin watanni biyu."

A jawabinsa lokacin da yake karɓar mulkin Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur.

Lamarin da ya janyo tashin farashin litar man fetur da na kayan masarufi a faɗin ƙasar.

Matakin ya sanya murnar al'ummar ƙasar ta koma ciki game da murnar samun sabuwar gwamnati, wadda suka yi fatan za ta kawo musu sauƙi daga matsin da suka faɗa ciki sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.

Ƙimar shugaban jam'iyya

Wani batu da farfesa Kamilu Fagge ya ce zai iya zama ƙalubale ga Abdullahi Ganduje wajen tafiyar da lamurran gwamnati shi ne tabon da yake da shi game da zargin cin hanci.

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet, ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum wanda ta yi zargin cewa Ganduje ne yake karɓar damin daloli daga hannun wani ɗan kwangila yana zubawa a aljihu.

Sai dai shugaban na jam'iyyar APC ya sha musanta batun.

Amma duk da haka lamarin ya ci gaba da zama wata babbar lam'a ga tsohon gwamnan.

Bayan saukarsa daga muƙamin gwamnan jihar Kano, Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen al'umma da yaƙi da rashawa ta jihar, ta sha alwashin ci gaba da binciken Ganduje kan bidiyon.

Sai dai ya samu umarnin kotu, wadda ta dakatar da hukumar daga ci gaba da binciken.

Siyasar kuɗi

Farfesa Fagge ya ce wani babban ƙalubale da sabon shugaban jam'iyyar zai fuskanta shi ne yadda ake amfani da kuɗi da kuma ƙarfa-ƙarfa wajen samun tikitin tsayawa takara.

A lokacin jawabin da ya yi bayan tabbatar masa da muƙamin, Ganduje ya ce zai yi ƙoƙarin yin adalci tsakanin jam'iyyar tare da tabbatar da ganin cewa kowa ɗaya ne.

Fagge ya ce "Shi kansa ana zargin cewa shugaban ƙasa ne ya yi ƙarfa-ƙarfar cewa dole sai an ba shi muƙamin, yayin da wasu ƴaƴan jam'iyyar ke ganin cewa kamata ya yi a bar muƙamin a yankin arewa ta tsakiya, inda nan shugaban jam'iyyar da ya sauka ya fito."

A Najeriya dai ana zargin jam'iyyun siyasa na ƙasar da yin ƙarfa-ƙarfa a tsakanin ƴanƴansu, musamman a lokutan tsayar da ƴan takara.

Ko Ganduje zai iya shawo kan matsalolin?

Makusantan sabon shugaban rikon na jam'iyyar ta APC Abdullahi Ganduje, na ganin shugaban zai iya tunkarar waɗannan ƙalubalen, ganin cewa yana da ƙwarewa.

A cewar Mukhtari Ishaq Yakasai, tsohon kwamishina a lokacin da gwamna Ganduje ke mulkin Kano, ya ce idan aka duba yadda gwamnan ya tafi da mulkin Kano tsawon shekaru takwas, da kuma mukamai da ya rike a lokuta daban- daban a ƙasar, ba zai zama wani abu mai wahala ba ga sabon shugaban na APC.

"Ganduje tsohon ɗan siyasa ne da ya jima ana damawa da shi a harkokin siyasa a Najeriya, don haka babu abin da zai gagare shi," a cewar Mukhtar Ishaq.

Ya ce abin da kawai za a yi shi ne a ba wa Ganduje lokaci.