Masu noman cocoa da wasan motsa jiki cikin hotunan Afirika na mako

.

Asalin hoton, TIM CLAYTON/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ƴar wasan motsa jiki Kaylia Nemour daga ƙasar Moroko yayin gasar wasanni ranar Litinin a Beljiyam.
.

Asalin hoton, ISSIFOU DJIBO/EPA

Bayanan hoto, Babur mai ƙafa uku ɗauke da masu zanga-zangar zaman dakarun Faransa a Nijar ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP

Bayanan hoto, Wani mai sayar da kankana a Cairo babban birnin ƙasar Masar.
.

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Shugaban Ƙasar Laberiya George Weah sun sa riga mai ɗauke da hotonsa yayin da mako ɗaya ya rage a gudanar da zabe a ƙasar.
.

Asalin hoton, Issouf Sanogo/AFP

Bayanan hoto, Masu sayar da Atamfofi a kasuwar Abidjan da ke Ƙasar Ivory Coast ranar Talata.
.

Asalin hoton, DANIEL IRUNGU/EP-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

Bayanan hoto, Mawaƙin Ƙasar Kwango Fally Ipupa ranar Asabar lokacin gasar Walker Town da aka gudanar a Nairobi babban birnin Ƙasar Kenya.
.

Asalin hoton, GIANLUIGI GUERCIA/AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan dambe na Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kwango ya na shirin gasar damben Afirika da za a fafata a Afirika ta Kudu ranar Talata.
.

Asalin hoton, Queila Fernandes/AFP

Bayanan hoto, Dandalin baza kolin zane-zane na Mansa Floating Hub a Cape Verde.
.

Asalin hoton, Jihed Abidellaoui/Reuters

Bayanan hoto, Mai sana'ar dafa abinci ta na markaɗa barkono a shagonta ranar Lahadi a Ƙasar Tunisiya.
.

Asalin hoton, Ange Aboa/Reuters

Bayanan hoto, Ranar Litinin lokacin da wani mai noman Cocoa ya ke shanya a birnin Daloa na Ƙasar Ivory Coast.