Liverpool ta sanar da daukar Slot a matakin sabon kociyanta

Arne Slot

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta sanar da daukar Arne Slot a matakin sabon kociyanta daga Feyenoord, wanda zai fara jan ragama a farkon watan Yuni.

Ƙungiyar dake Anfield ta biya ta Netherlands £9.4m, sauran kudin kunshin ƙwantiragin mai horarwa ranar Juma'a.

Mai shekara 45 zai maye gurbin Jurgen Kloop, wanda ya ja ragamar kungiyar kaka tara da daukar Premier League a 2020, bayan shekara 30 rabonta da shi.

Kloop ya fara aiki a Liverpool tun daga Oktoban 2015, ya bar kungiyar ranar Lahadi, bayan da ya buga wasan karshe da Wolverhampton.

Ɗan kasar Netherlands zai fara aiki da Liverpool ranar 1 ga watan Yuni da zarar ya samu takardar izinin shiga Ingila yin aiki.

Kociyan ya ja ragamar Feyenoord a 2022/23 ta lashe Eredivisie title, wadda a bana ta kare a mataki na biyu a teburi da daukar Dutch Cup.

An ce Liverpool ta dauki kociyan saboda salon yadda yake horar da tamaula ta kai hare-hare da yadda ya kware a bunkasa matasan ƴan kwallo.

Slot ya karbi aikin kociyan Feyenoord a 2021, wanda ya nuna sha'awar karbar aikin kociya a Premier League, tun bayan da aka alakanta shi da Tottenham a 2023.

Liverpool ta tuntubi Xabi Alonso, wanda ya ja ragamar Bayern Leverkusen ta lashe Bundesliga a karon farko, domin ya ja ragamarta.

Sai dai kuma kociyan mai shekara 42 dan kasar Sipaniya ya fayyace cewar ya zabi ci gaba da jan ragamar kungiyar dake buga Bundesliga.

Haka kuma an bayar da rahoton cewar Liverpool ta tuntubi mai horar da Lisbon, Ruben Amorin, domin maye gurbin Jurgen Kloop, wanda ya sanar zai bar Anfield a karshen kakar bana.