Ranar Yaki da Fataucin Mutane ta Duniya: ‘Na yi fargabar za a binne ni a teku’

Asalin hoton, Getty Images
"An ce mutum biyar ne suka mutu a wani kwale-kwale a baya-bayan saboda zazzaɓi da rashin lafiya da ke da nasaba da teku, kuma an jefa gawarwakinsu a cikin teku.”
"Daya daga cikinmu ya faɗa cikin mummunan rashin lafiya, amma babu magani a jirgin.
Wasu daga cikinmu sun zo da giya. Sai na sha giyar na bugu domin in daina jin tsoron mutuwa,” a cewar Shiva, wani mutumin Sri Lanka wanda aka yi fataucinsa zuwa Australia ta kwale-kwale ba bisa ƙa’ida a.
Wannan ya faru ne a shekarar 2012, shekara uku kacal biyo bayan nasarar da dakarun gwamnatin Sri Lanka ta samu nasara akan ‘yan tawayen Tamil Tiger a watan Mayun 2009, lamarin da ya kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka share shekara 30 ana yi.
"Mun wahala na tsawon shekaru 30. Hakan ya jawo mana talauci. Saboda haka, na samu matsalar dangana da shan giya,” Shiva ya gaya wa BBC.
“A lokacin ne wani abokina ya tambaye ni idan ina son zuwa Australiya tare da su ta kwale kwale,” a cewar mahaifin yara biyu ɗan asalin arewacin Sri Lanka.
Tabon yaƙi

Asalin hoton, Getty Images
Kamar Shiva, ‘yan kabilar Tamil daga arewaci da gabashin Sri Lanka sun wahala ba kawai a jikinsu, haka ma a ƙwaƙwalwar su sakamakon mummunan yaki, kuma suna neman mafita.
”A baya, mutane da yawa sun je Australiya ta kwale-kwale ba bisa ƙa’ida ba.
"Komai ya faru ta hanyar dillali ne wanda na hadu da shi ta hanyar wani abokina.
"Ya tambaye ni na biya rupee miliyan Daya ($8,000) kudin tafiyar baki ɗaya, sannan in fara biyan rabin miliyan rupe dala 4000 kenan.
Shiva ya ce ya hada kudin ne ta sayar da gwala-gwalan matarsa sannan ya ciwo bashi mai kudin ruwa da yawa.
Cibiyar fataucin mutane

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Birnin Negombo da ke yammacin Sri Lanka na ɗaya daga cikin cibiyoyin fataucin mutane a ƙasar.
Jude wani ɗan garin mai kwale-kwale ya gaya wa BBC cewa ya kai ɗaruruwan mutane Australiya da Italiya ba bisa ƙa’ida ba a shekara 30 da suka wuce.
Tafiya ɗaya ce daga Sri Lanka zuwa Australiya ta Tekun Indiya, sannan Italiya ta yi suna a tarihi saboda tana ba da damarmakin aiki.
Sannan mafi yawancin mazauna Negombo – wadda kuma ake kira ‘Little Rome’ ko ƙaramar Roma – duk mabiya darikar Katolika ne.
"Akwai wani lokaci a ƙarshen shekarun 1990, na kai mutum 130 Italiya ba bisa ƙa’ida ba a cikin wani kwale-kwale mai inji biyu,” Jude yana alfahari ya gaya wa BBC.
Ya ce masu fataucin mutane na amfani da jita-jita akan sauyin manufofi dangane da ‘yan gudun hijira kamar Australiya domin jawo hankulan mutane.
"Idan muka ji cewa kasashe sun saukaka takunkumi akan ‘yan gudun hijira kuma akwai dama,” yake cewa.
"Ba da jimawa ba, za mu zuba abinci da ruwa a cikin kwale-kwale sannan a cika shi da isasshen mai."
Bisa rahoton Majalisar Dinkin Duniya na 2020 a kan fataucin muane, a shekarar 2018 kashi 46 cikin 100 na wadanda aka gano an yi fataucin su mata ne, kashi 1 yara mata, kashi 20 maza, kashi 15 yara maza.
Amma ba Jude ba ne yake samo wa kansa Fasinja. Kuma ba shi ba ne yake tafiya da mutanen da yake fatauci.
"Dilalai ne suke samowa da kawo mana mutane. Muna cewa kamar rupees rabin miliyan (misalin dala 1,400) idan suka tambayi nawa ake biya.
"Su dillalan suna aje rabin miliyan na rupee a matsayin ladan aiki,” a cewar Jude.
"Waɗannan dillalan na haɗa mutane kamar goma zuwa 15 a duk fadin kasar.
"A haka za a hada kamar mutum 50,” ya ƙara. Jude ya bayyana cewa dillalai a wannan sana’a su ne su ka fi samun riba.
“Sannan za mu samu matuki, da mataimaka hudu ko biyar su taimaka masa. Sai muyi rijistar kwale kwalen da sunan matukin saboda kwale-kwalen ba za dawo ba, kuma baza a iya bin sawunsa ba.
"Ma’aikatan baki dayan su za su isa bakin gabar teku tare da wadanda aka yi fatauci.”
Wannan tafiya ce hanya daya, babu juyowa ko dawowa – ba fasinjojin kadai ba, har da ma’aikatan jirgin saboda su ma zasu nemi mafaka ne.
Burin samun rayuwa mai daɗi

Asalin hoton, Sri Lanka Navy
Jude ya ce yana kai kwanaki 25 zuwa 30 a isa tekun Italiya ta mashigar Suez a kan kwale-kwale. Tafiya zuwa Australia ya fi sauri, yana ɗaukar kamar kwana 10 zuwa 15.
Amma babu tabbas.
Shiva ya ce an tambaye shi ya biya ragowar cikon kudi – kamar dala 4000 – kafin ya hau kwale-kwalen da ragowar wasu mutum 60.
Duk da cewa yakin ya kare, ana tursasawa daruruwan ‘yan Tamil bacewa a arewacin Sri Lanka.
Masu gwagwarmayar kare hakkin bil adama da yawa sun fuskanci cin zarafi kuma an kashe ‘yan jaridu da dama a wannan lokaci.
Gwamnati na ci gaba da karyata duk wata alaƙa da sata ko ɓacewar mutane.
Kafin 2009, duka bangarorin biyu sun zargi juna da tafka tashin hankali, amma an cigaba da sace mutane tun kafin a ci ‘yan tawayen Tamil Tigers da yaki.
‘Ba wani abu don na mutu a kan kwale-kwale’

Asalin hoton, Getty Images
"Lura da yanayin Sri Lanka bayan yaki, ba wani abu don na mutu akan kwale-kwale,” a cewar Shiva.
Amma bayan share kwanaki akan teku, ya fara kewar yaranshi guda biyu da matar dake gida.
"Na kasa dena tunanin su,” yake tunawa.
Bayan share kwanaki 22, Shiva da wasu mutane sun isa tekun dake kusa da Australiya.
Masu neman mafaka da aka gano akan kwale-kwale a tekun kusa da Australia an shiga gabansu.
Sannan an tsare su a wurare daban-daban, a ciki har da waje a kasashen Nauru da Papua New Guiniea, da kuma tsuburin Christmas Island da ke karkashin ikon Australiya a Tekun Indiya.
Shiva ya ce an tsare su a tsuburin Christmas Island har sai alkali ya saurare su.
“Wasu daga cikin wadanda aka tsare da suka share watanni ko shekaru a sansani sun gaya mun cewa ko da na samu dama zuwa Australia.
"Ba zan iya kawo matata da yara na biyu ba. Ko da akwai damar, zai dauki shekaru masu yawa.”
Bayan kwanaki 30, shi da wasu mutane 13 aka mayar Sri Lanka saboda “ba su da kwararar hujjoji”.
Jude ya nuna cewa masu fataucin mutane sun dakatar da safarar mutane zuwa Italy baki daya tsaboda tsada da kuma takunkumai da aka saka wa ‘yan gudun hijira.
“A baya akwai saukin fataucin mutane zuwa Australiya, amma yanzu ya yi mutakar wahala,” ya faɗa cikin ƙorafi.
Marasa galihu da abun ya shafa
An tambaye shi ko ya yi nadamar karya doka da samun riba daga mutanen da ke cikin mawuyacin hali da ka iya saka su cikin hadari?
Sai ya ce “Ba ma jin babu dadi a lokacin da mutanen suka hau jirginmu saboda su suka yarda suka suka.
"Su suka jefa kawunansu a cikin haɗari domin inganta rayuwarsu” a cewar Jude.
"Za su isa gabar tekun ne ko za su kare a tsare wannan ba shi da muhimmanci ga mai kwale-kwalen.
"Sun san irin hadarin da tafiyar ke da shi kafin su hau hanya.“
Sai dai Jude yace yana jin babu dadi idan ya ga mata da yara suna cikin mawuyacin hali akan hanyar su na wannan tafiya.
Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta bayyana cewa akwai karin adadin mutane da yawa da ke kokarin zuwa Australia akan kwale-kwale a wannan shekara.
Kakakin rundunar Captain Indika de Silva ya bayyana wa BBC cewa a watan Yuli na 2022 mutane 864 ne suka yi kokarin zuwa Australiya ta kwale-kwale kuma duk an tsare su.
Sannan an kama jirage 15 din da suka yi amfani da su wajen tafiyar.
Bugu da ƙari an tsare mutanen Sri Lanka 137 wadanda suka isa yankin Australia a kwale-kwale guda hudu kuma an yi amfani da jiragen sama wajen mayar da su.
Rundunar ta ƙara ta tsare wasu kwale-kwale guda biyu da suka je Kanada a shekarar 2021 da 2022.
Captain de Silva ya bayyana cewa babu wani kwale-kwale da ke tafiya ba bisa ƙa’ida ba a lokacin annobar cutar korona.
Babu abinci, babu mai, babu magani

Asalin hoton, Getty Images
Shiva bai ƙara shan giya ba tun dawowar shi Sri Lanka, kuma a hankali ya biya duk bashin da ake bin sa bayan ya fara sabuwar sana’a.
Amma tattalin arzikin Sri Lanka na cikin tsaka mai wuya a wannan lokacin da asusun ajiyar kasar waje ya yi kasa, lamarin da ya sa gwamnati ta gagara shigar da mai ko magani kasar, yayin da farashin abinci ya tashi.
Akwai layukan motoci a gidajen mai masu tsawon mil da dama, yayin da direbobi suke kwana a cikin motocin suna tsawon sama da mako ɗaya domin sayen galolin mai kaɗan.
Adadin mutanen da suka tsere zuwa makwabciya Indiya daga arewacin Sri Lanka ya karu doomin matsalar tattalin arziki da kasar ke fama da shi, kuma yanzu haka Shiva yana zulumin rayuwarsa a nan gaba.
"Ji nake kamar na koma Australia saboda wannan yanayi na Sri Lanka.
"A baya sakamakon yaƙi, sai kuma yanzu saboda tattalin arziki. Babu abinci, babu mai, babu magani a ƙasarmu."











