Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda cutar kuturta ke yaɗuwa
Kuturta na cikin jerin cutukan da suka fi yawa a ƙasashemn da ke fama da zafi inda kuma ba a damu da yaɗuwarta ba.
Kuma duk da kokari da hukumomi da sauran ƙungiyoyi ke yi wajen yaƙar cutar, bayanai na cewa har yanzu ana fama da ita, kuma samun magani wani babban ƙalubale ne ga masu ɗauke da cutar
Masana na cewa kuturta har yanzu barazana ce ga duniya musamman ma Afirka da aka bayyana cutar ta fi yaɗuwa.
Alƙumma sun ce kimanin mutum dubu ɗari da saba'in da huɗu suka kamu da cutar a duniya, kuma daga ciki mutum dubu ashirin da ɗaya da ɗari tara da talatin da biyar ƴan Afirka ne.
Kuma alƙalumma sun ce Najeriya na cikin ƙasashen da kuturta ta fi ƙamari a Afirka.
Saboda girman cutar da kuma wayar da kan al'umma aka ware rana domin gangamin yaki da kuturta a duniya da ake gudanarwa duk 31 ga watan Janairu.
Hanyoyin yaɗuwar kuturta
Kwararru sun ce ana ɗaukar cutar ne daga mutum zuwa mutum saboda mai cutar zai iya yadawa ta hanyar tari da atishawa da numfashi.
Amma masanan sun ce kuturta na ɗaukar lokaci mai tsawo kafin ta bayyana.
Haka kuma kwararrun sun ce idan har aka gano mutum na dauke da cutar kuturta da wuri to ana iya warkewa.
Alamomin kuturta sun hada da sauyawar launin fata da kuma rufewa ido, kamar yadda Dr Ibrahim Aliyu Umar kwararran likitan tarin fuka da kuturta a Najeriya ya shaida wa BBC
Kodayake ya ce kuturta ba ta yaɗuwa cikin sauri, shi ya sa galibi mutane ba su san yadda take yaɗuwa ba.
Ya ce mutum na ganin ɗaya daga cikin alamomin sai ya yi gaggawar zuwa asibiti a duba a tabbatar da ko ya harbu da kuturta domin a magance ta da kare al'umma daga daukar cutar."
Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ɗaya daga cikin jihohin da ke yaƙi da cuta, amma wasu daga cikin masu larurar kuturta sun koka kan rashin samun maganin cutar, a daidai lokacin da kwararru ke cewa har yanzu da sauran cutar a cikin al’umma.
Wasu majinyatan cutar a asibitin Bela a jihar Kano sun shaidawa BBC cewa suna shan wahala kafin su samu magani.
Hukumomi sun ce suna gyaran asibitin masu dauke da cutar tare da bayar da magani kyauta.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya ce "An kusa kammala gyaran wannan asibiti, kowane daki an sanya masa fitulu, kuma mai girma gwamna na bayar da magani da abinci kyauta ga masu lalular kuturta."
Sai dai masu fama da cutar suka koka kan rashin samun magani kyauta kamar yadda a baya ake ba su.
"Ba a yi ma na taimakon magani, duk abin da ake kawo wa ba a raba wa kowa," in ji wani mai cutar kuturta a jihar Kano.
Shi ma wani da ke fama da cutar ya ce " yanzu ba mu samun magani ba kamar can baya ba, yanzu haka akwai maganin Naira dubu 12 da aka rubuta mun amman na kasa saye saboda ba ni da kuɗi."
Bayanai na cewa an fi alakanta ciwon kuturta da gado, amma masana na cewa duk da ana gadar cutar ana kuma daukarta, kuma idan ba a dauki mataki da wuri ba, cutar tana iya cinye jijijiyar da ke kai sakon motsi wato moto nerve ko jijiyar da ke sa mutum ya ji ya taba abu wato sensesury nerve, abin da ke sa hannu ko kafa su lalace.