Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ta sauya rayuwa saboda ziyarar da ta kai matattarar kutare
A cikin jerin wasiku daga marubutan Afirka, Adaobi Tricia Nwaubani ta yi rubutu kan wata mata wadda rayuwarta ta sauya bayan ta gamu da larurar fata sannan daga bisani ta ziyarci wata matattarar kutare a Najeriya.
Iby Ikotidem, ta kasance mai son jin dadin rayuwa da zuwa walima irin ta Turawa. Tana matukar son kwalliya da kyale-kyale, tana kuma da yawan kawaye, ga yawan shirya walima a jihar New Jersey ta Amurka, inda take zaune tare da mijinta da 'ya'yanta biyu fiye da shekara 28.
Ta ce: "Na kasance mai kayatarwa a wuraren biki."
Amma duk wanann ya zo karshe jim kadan bayan ta fara samun matsala a fatarta ta gwiwa shekara 12 da ta wuce.
Da farko ba ta damu ba saboda abin da ya fito mata a kan gwiwarta ba shi da yawa, amma daga bisani abin ya dinga karuwa da bazuwa zuwa sassan jikinta in banda fuskarta.
Bayan gwaje-gwaje da aka yi mata, an gano ta kamu da wani nau'in karzuwa, wanda yake sa kwayoyin halitta a jikin fata su kumbura kuma fatar mutum ta dinga wani ɓawo-ɓawo, ga kaikayi da kuma bushewa.
Duk da tana rufe jikinta da dogon siket da riga mai dogon hannu saboda kar a rika kallonta, yanayin da take ciki kan sa ko da ta fita sai an kalleta.
A wasu lokuta, idan ta tashi daga kan kujera sai mutane su yi ta mamaki a kan yadda aka samu kura a kai da ma kasan wajen da ta zauna saboda zubar bawon karzuwar da ta fito mata a jikinta.
"Na tsani na kalli kaina, madubi ya zame mani babban makiyi," in ji ta.
Ba a jima ba aka fara tsangwamar ta.
Mrs Ikotidiem ta ce ta tuna wani abu da ya faru a lokacin da aka gayyace ta wajen wata walima a gidan kawarta. An ajiye mata katifa a dandaryar kasa a wani ɗakin karkashin kasa, yayin da sauran mahalarta walimar aka ba su dakuna a bene.
Ta ce: "A ranar na zauna na sha kuka saboda ɓacin rai".
Ba a jima ba Mrs Ikotidiem ta kebe kanta daga shiga jama'a, sannan ta aske gashin kanta, ta fita hayyacinta har sai 'yarta mai shekara 12 ta fada mata cewa "Haba mahaifiyata abar alfaharina kar ki bari wannan larurar ta sanyaya miki gwiw.''
Daga nan ne Mrs Ikotidiem ta dawo hayyacinta ta kawar da tunanin kashe kanta da take yi.
Bayan shekara da kamuwa da larurar, sai aka gayyaci 'ya'yanta su bi wata tawagar matasa a Amurka zuwa jiharsu ta asali a Najeriya wato Akwa Ibom domin gudanar da wani aikin taimako.
Ɗanta mai suna Anthony a lokacin yana da shekara 15, ya roki mahaifiyarsu da ta raka su, ta amince.
Sun ziyarci gidajen marayu da dama inda suka dinga bayar da taimako. Bayan sun dawo masauki a wani otal suna zaune suna cin abinci da safe, sai ga wata abokiyar karatun Mrs Ikotidiem, ta yabe ta sosai a kan yadda suka dinga bayar da taimako a gidajen marayu - saboda an nuna a gidajen talabijin na jihar.
A nan ne kawarta ta bukaci da ko za su je wata matattarar kutare a jihar domin ba su taimako.
Sai Mrs Ikotidiem ta ce, kai har yanzu akwai kuturta a Najeriya? Wannan shi ne lokacin da ta fara sanin cewa lallai akwai kuturta a duniya.
Duk da kasancewar ana kokari wajen kawar da kuturta a Najeriya, har yanzu akwai wadanda suke da ita inda ake samun mutum 3,500 a duk shekara da ke kamuwa da ita a cewar hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC.
Ana iya maganin wannan cuta idan har aka gano ta da wuri, amma idan aka bari ta jima a jikin mutum takan haddasa lalacewar wasu wurare a jikin mutum kamar kafa da hannu, wani lokaci har makanta take haifarwa.
Wasu iyaye sun yi fargaba da suka ji cewa Mrs Ikotidiem za ta je asibitin kutare na Ekpene Obom, amma wannan ziyara ta sauya mata rayuwa.
Kamar sauran asibitocin kutare a Najeriya, asibitin kutare na Ekpene Obom ma na samar da wajen zama ga masu larurar wadanda ba za su iya komawa gida ba saboda tsangwama.
Ko da sun warke bayan an yi musu maganin cutar inda ake daukar wata 6 zuwa 12, sukan kasance a wajen tare da iyalansu har ma 'ya'yansu su dinga zuwa makaranta a harabar wajen.
Mrs Ikotidem ta fada wa mazauna wajen da ma marasa lafiyar cewa ta fahimci irin halin da suke ciki.
Ta ce: "Na san yadda mutum ke ji idan aka yi watsi da shi ko kuma ake kallon sa".
A yanzu Mrs Ikotidem ta shafe fiye da shekara 10 tana kula da masu larurar kuturta.
Ta bude gidauniya mai suna Hope's Door, inda take kula da masu larurar kuturta a asibiti uku a kudanci da kuma arewacin Najeriya.
Bayan duk taimakon da take yi, takan samar da takalmi na musamman da kujerar guragu ga masu matsalar. Takan kuma aika da kayayyakin karatu ga 'ya'yan masu lalurar, tana gyara musu muhallai.
Duk da dan tallafin da asibitocin kutare ke samu daga gwamnati, yawancin irin wadannan asibitoci a Najeriya na dogara ne da taimakon da suke samu daga kungiyoyin agaji na kasashen waje.
"Idan suna da wata matsala, sukan kira ni," a cewar Mrs Ikotidem.
Ta sayar da sarkokinta ne da farko inda ta fara kai tallafi ga irin wadannan asibitoci, daga bisani sai ta hada wani taron tara gudunmuwa daga kawayenta, a nan ne ta tara kudade masu yawa.
A yanzu abin da take son yi shi ne taimaka wa wadanda ke zaune a matattarar kutaren ta yadda za su zamo masu dogaro da kansu inda za ta ba su kayayyakin aikin noma don noman gonakinsu.