Ƴan Najeriya sun maƙale a Dubai

Asalin hoton, Presidency
Wasu ‘yan Najeriya da ke zaune a Hadadiyar Daular Larabawa wato Dubai sun koka kan yadda hukumomin daular suka ƙi sabunta masu bizar zama a ƙasar da kuma aiki, lamarin da suka ce ya jefa su cikin ƙunci.
Mutanen sun ce lamarin ya sa sun yi asarar dukiyoyinsu tare da rasa ayyukansu a Dubai.
Wasu daga cikin yan Najeiryar da ke zaune a hadaɗiyar daular Larabawan sun ce ɗarruruwan ‘yan Najeirya ne dai suka rasa ayyukansu yayin da ake kyamar daukar ‘yan ƙasar aiki, ko sabunta masa takardar bizar zama a ƙasar.
Ɗaya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya ce dukkan wani mai fasfon Najeriya da bizarsa ta ƙare ba ya iya sake samun aiki, "Gwamnati ta hana mu sabunta bizarmu,hakan ya fi komai damunmu saboda ko da babu sana'a idan akwai biza za ka shiga ka fita duk lokacin da kake buƙata."
Haka zalika shi ma wani da ke sana’ar shirya tafiye tafiye ya bayayana wa BBC cewa hakan ya shafi kasuwancinsu, lamarin da ya kai su rufe ofishoshinsu.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin ministan harkokin ƙasashen wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar kan wannan batu amma hakan ya ci tura sakamakon rashin dawo da amsar gajeren sakon da muka aika masa, da kuma kiran wayar da aka yi masa.
A baya bayan nan dai wasu daga cikin jaridun Najeriya sun ruwaito ministan harkokin wajen na Najeriya, na bayar da tabbaci ga yan Najeriyar da ke Hadaɗiyar Daular Larabawan ya cewar an kusa cimma matsaya kan lamarin.
Tun a 2021 ne gwamntin Najeriya da ta Haɗaɗiyar Daular Larabawa suka shiga takun sakar diflomasiyya kan rabon harkar sufurin jirgin sama da haramta wa ‘yan Najeriya zuwa ƙasar.
Dukkan ƙasashen biyun sun yi ta kwan-gaba kwan-baya tun lokacin cutar korona inda suka yi ta samun saɓani kan wasu ƙa'idojin tafiye-tafiye.
Ko a watan Satunbar bara sai da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai wata ziyara Daular a yunkurin ganin an sami daidaito kan saɓanin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Sannan ya sake komawa a watan Disambar bara don halartar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya haɗu da hukumomin Hadadiyar Daular Larabawan kan sabanin da ya ki ci ya ƙi cinyewa.










