PSG za ta yi gogayya da Man Utd kan Neves, Rabiot na da zaɓin ƙungiyoyi uku

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain na shirin gogayya da Manchester United a neman sayen matashin ɗan wasan tsakiya na Benfica, Joao Neves, mai shekara 19 wanda kuma ke tawagar Portugal (Le10Sport )
Barcelona ta cimma yarjejeniya ta baka da ɗan gaban Athletic Bilbao kuma ɗan Sifaniya Nico Williams, mai shekara 21. (Sport - in Spanish), external
Manchester United ta zaku ta kammala maganar cinikin ɗan bayan Bayern Munich, Matthijs de Ligt, na Netherlands da zarar an kammala gasar cin kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024. (Bild )
Arsenal ta yarda da buƙatar da Lazio ta gabatar mata ta ba ta aron ɗan bayanta Nuno Tavares na Portugal, tare da yarjejeniyar sayensa a tsakanin fam miliyan 6 zuwa 7. (Mirror)
Chelsea ba ta da niyyar neman sayen ɗan gaban RB Leipzig Dani Olmo na Sifaniya, wanda farashinsa yake a kan fam miliyan 50 a kwantiraginsa ga duk me so. (Sky Sports)
Jacob Greaves, ya kammala gwajin lafiyarsa a Ipswich Town, yayin da yake shirin barin Hull City. (Sky Sports)
Liverpool, ko Bayern Munich ko Real Madrid, ɗaya daga cikinsu za ta kasance ƙungiyar da ɗan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 29 zai tafi bayan da kwantiraginsa da Juventus ya ƙare a watan da ya wuce. (Calciomercato)
Marseille na sha'awar ɗan gaban Arsenal Eddie Nketiah na Ingila. (Footmercato)
Bayern Munich na son sayen ɗan gaban Netherlands Xavi Simons, mai shekara 21, daga Paris St-Germain. (Sky Sports)
Monaco ta yi watsi da tayin Yuro miliyan 30 (£25.5m) daga Nottingham Forest, a kan ɗan wasanta na tsakiya Youssouf Fofana, na Faransa, mai shekara 25, wanda tuni ya cimma yarjejeniya da AC Milan. (Fabrizio Romano)
Nan da ƴan sa'o'i ɗan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, zai kammala tafiyarsa Bayern Munich daga Fulham. (Sky Germany)










