An ci tarar Eto'o dala 200,000 amma ya tsallake rijiya da baya

A

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika ta ci tarar shugaban Hukumar kwallon ƙafa ta Kamaru Samuel Eto'o dala $200,000 saboda karya dokar hukumar.

Sai dai ya tsallake rijiya da baya, saboda rashin samin cikakkiyar hujja kan zargin da ake yi masa na sayan wasanni.

A watan Agustan bara ne, CAF ta fara bincike na Eto'o bayan samun ƙorafe-ƙorafe a rubuce daga wasu masu ruwa da tsaki a faggen kwallon kafa a ƙasar.

Daga baya kwamitin hukunta laifuka ya gano tsohon dan wasan wanda ya lashe kyautar dan wasan Afrika sai hudu ya karya wasu ƙa'idojin da aka kafa na sanya hannu kan wata kwantaragin zama wakilin kamfanin caca na 1XBET.

Lauyan Eto'o ya ce za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Kamfanin 1XBET ne ke ɗaukar nauyin manyan gasar kwallon kafa ta maza da mata a Kamaru, yayin da dokar FIFA ta bayyana cewa duk mutumin da ke da alaƙa da ita bai kamata a ga hannunsa ba cikin lamuran caca.

A watan jiya na Yuli ne wata kungiya da kananan kuloblika ta gabatar da bukatar Eto'o ya ajiye mukaminsa, suna bayyana damuwarsu kan alaƙar dan wasan mai shekara 43 da kamfanin caca na 1XBET.