INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a Adamawa

Asalin hoton, INEC
Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa.
Cikin wata sanarwa da babban jami'inta kan yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na ƙasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa - REC ya ɗauka na sanar da wanda ya lashe zaɓe haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.
Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa ba.
Hukumar INEC ta gayyaci duka jami'anta da ke lura da zaben gwamna a jihar Adamawa, su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaɓen gwamnan jihar Adamawa ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.
Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jam'iyyar PDP shi ne ke kan gaba bisa alkaluman da hukumar INEC ta sanar kawo yanzu, yayin da Aishatu Dahiru Binani ta jam'iyyar APC take bi masa a yawan ƙuri'u.
Yadda aka wayi gari

Asalin hoton, Facebook/Fintiri/Binani
An wayi gari a jihar Adamawa cikin wani yanayi na dakon sakamako da ruɗani.
Tun da farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ɗage aikin tattara sakamakon zaɓe a ranar Asabar, bayan karɓar sakamakon zaɓen cike-giɓi da aka yi cikin wasu tashoshin zaɓe na ƙananan hukumomin jihar 20.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar Asabar da daddare, jami'in sanar da sakamakon zaɓe, ya bayyana sakamakon da aka samu a ƙananan hukumomi guda goma.
Daga bisani kuma ya ɗage aikin karɓar sakamakon zuwa ƙarfe 11 na safe a ranar Lahadi.
Sai dai da misalin karfe 10 na safe, sai babban jami'in INEC wato REC Barrister Hudu Ari, ya shiga zauren tattara sakamakon zaben a Yola tare da rakiyar 'yan sanda, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen.
Bai dai yi bayani filla-filla na sakamakon da kowacce jam'iyya ta samu da kuma yadda aka ci zaɓen ba.
Wannan matakin ya sa INEC ta ce aikin da jami'inta ya yi haramtacce ne.
Ga jerin ƙananan hukumomin da aka karɓi sakamakon zaɓe da INEC ta sanar a zauren tattara sakamakon zaɓen a Yola:
Ƙaramar hukumar Demsa
APC: 43
PDP 124
Ƙaramar hukumar Hong
APC: 361
PDP: 1056
Ƙaramar hukumar Shelleng
APC: 223
PDP: 299
Ƙaramar hukumar Song
APC: 558
PDP: 411
Ƙaramar hukumar Ganye
APC: 176
PDP: 309
Ƙaramar hukumar Jada
APC: 145
PDP: 271
Ƙaramar hukumar Lamurde
APC: 285
PDP: 580
Ƙaramar hukumar Yola ta Arewa
APC: 368
PDP: 357
Ƙaramar hukumar Yola ta Kudu
APC: 797
PDP: 678
Ƙaramar hukumar Maiha
APC:172
PDP:207










