Likitoci sun kaɗu da yawaitar fyaɗe a Khartoum

Yadda mata ke neman abin kaiwa bakin salati a Sudan yayin da kasar ke fama da rikici

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mata da dama a Sudan na cikin tasku tun bayan barkewar yaki a kasar

Muryar wata likita mace da ke rayuwa a yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita a Sudan tana rawa.

Ta saki wani saƙon murya ne ga sashen Larabci na BBC ta hanyar WhatsApp.

A wani shirin rediyo na musamman da ake kira Li Sudan Salam, da ke nufin "gaisuwa da kuma "zaman lafiya ga Sudan".

An dai ƙaddamar da shirin ne bayan ɓarkewar tashin hankalin da ya kaure tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF a ranar 15 ga watan Afrilu.

Ɗaruruwan mutane ne suka mutu kana sama da mutane miliyan guda rikicin ya tilasta wa ficewa daga gidajensu a faɗin ƙasar.

Shirin rediyon ya samu saƙonni masu yawa game da yadda aka ci zarafin mata da 'yan mata sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ƙasar ta afka.

Abu ne mai wahala a iya tantance adadin mutanen da rikicin ya shafa, sai dai likitoci sun ce akwai rahotanni da dama da ba a bayyana su ba.

"Mun samu damar tattaunawa da wasu mata uku waɗanda aka yi wa fyaɗe kuma muna ta kokarin samar da yadda za a duba lafiyarsu, sai dai har yanzu akwai wasu matan biyu da muka gaza samun su," a cewar wani likita a ɗaya daga cikin asibitoci ƙalilan da ke aiki a Bahri, ɗaya daga cikin garuruwan da suka haɗa da Khartoum, babban birnin Sudan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Salima Is'haq, daraktar sashen yaƙi da cin zarafin mata ta gwamnatin Sudan, ta ce mafi yawan matsalolin cin zarafin mata an same su ne a garin Bahri, inda aka fuskanci yaƙi mafi muni.

"Shekarun ƴan matan da suka kawo mana ƙorafi sun kama daga 12 zuwa 18," in ji likitar, ta bayyana cikin murya mai ban tausayi.

"Amma adadin rahotannin da muka samu ba su kai haƙiƙanin adadin da suka faru ba. Ba su wuce kashi 2 bisa 100 na haƙiƙanin abin da ya faru ba."

Duk da lalacewar yanayin gwamnatin ƙasar, malama Salima ta ce ta yi bakin ƙoƙarinta.

Ta jagoranci aikin samar da kayan kiwon lafiya da tallafin yadda za a kwantar da hankulan mutanen da lamarin ya shafa ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyin sa-kai da masu samar da tallafi, amma duk da haka an gaza samun da dama daga cikin waɗanda suka tsira.

"A halin yanzu, yanayin ya yi matukar tsananta a Khartoum; komai ya taɓarɓare.

Yanzu mun fara mayar da hankali kan batun wayar da kai game da yadda za a dinga gabatar da bayanan mutanen da aka muzguna mawa domin ba su taimako, in ji likitar."

Sannan, ana yawan samun katsewar hanyoyin intanet da yawan ɗaukewar wutar lantarki.

Mutane da dama na fadi tashin neman yadda kulawar likitocin tun bayan barkewar rikicin Sudan a 15 ga wata Afrilu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Majinyata a Sudan na cikin matsanancin hali sakamakon barkewar rikicin kasar

A birnin Khartoum, shida daga cikin asibitoci 88 ne ke aiki.

Saƙonni da dama da shirin gidan rediyon ya karɓa sun yi tsokaci ne game da matsanancin halin da marasa lafiya masu fama da cutar ƙoda, waɗanda ke buƙatar a yi musu wankin ƙoda a kullum suka shiga inda ba sa samun damar kulawa.

"A yanzu babu maganin. Ni kaina na gaza samar wa wani ɗan uwana da ke fama da matsalar ƙodar," a cewar dakta Najlaa.

"Abin takaici, na gamu da wani marar lafiyar da ke fama da cutar a wani ɗakin magani, kuma ya ba ni wasu daga cikin magungunansa. Mu na buƙatar taimako daga kowane ɓangare domin samun kulawa."

Kuma ga leburori da ke rayuwa a yanayin hannu-baka hannu-kwarya, lamarin ya yi muni matuƙa.

"Muna ɗan tallafawa da wasu ƴan kuɗaɗe, amma yanzu sun ma ƙare.

Babu wasu hanyoyin samun guraben aiki. Ina da ƴaƴa, da kuma mahaifiyata, sannan ga 'yan uwana da suke rayuwa tare da ni.

Na kashe dukkan kuɗaɗen da na adana," in ji Mubarak.

Ya ce makwabtansa ne ke tallafa masa da dan kalacin da aka samu amma a yanzu a kullum lamarin ƙara rincaɓewa yake yi.

"Yadda suke amincewa da shirin BBC rediyo na sashen Larabci wani al'amari ne da ya yi matukar taɓa min zuciya," a cewar Mays Baqi, ɗaya daga cikin masu tsara shirin.

"Duk da irin wahalhalun da ake fuskanta a ɓangaren sadarwa, 'yan ƙasar Sudan da dama suna bayar da cikakkun bayanan da ke shafar rayuwarsu saboda sun yi amanna za mu saurare su kuma mu gabatar da labaransu bisa gaskiya."

An rufe sashen Larabci na BBC a farkon wannan shekarar saboda taƙaita kashe kuɗaɗe, amma an ci gaba da gudanar da ayyuka bayan da aka samu ɓarkewar yaƙi.

Ana gabatar da shirin Li Sudan Salam ne sau biyu a kullum na rabin sa'a a gajeren zango kuma ana iya samun shirin a shafin intanet sashen Larabci rediyon BBC.