Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mun kafa ƙungiya don kare haƙƙin tagwaye a Najeriya'
Tagwaye a arewacin Najeriya sun ce sun taru a garin Kaduna da zimmar kafa ƙungiyar da za ta dinga kare haƙƙinsu a ƙasa baki ɗaya.
Ƙididdiga daga Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna cewa a kowace haihuwa 1,000 za a iya samun tagwaye 12.
"Ba ma jin daɗin yadda za ka an auri Hassana an kai ta wani wuri, ita ma Hussaina a kai ta wani wuri daban," in ji shugaban ƙungiyar Hassan Tijjani Salihu.