Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da masana suka ce kan sayen bindiga 7,000 da gwamnatin Zamfara za ta bai wa 'yan sintiri
Masana harkar tsaro a Najeriya sun bayyana matakin gwamnatin Zamfara na samar da bindiga 7,000 ga ƴan sa-kai domin ƙarfafa musu gwiwar yaƙi da ƴan bindigar da ke addabar jihar a matsayin abin yabawa saboda tsaron al'umma hakki ne na kowa.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro a kasar Group Captain Sadiq Garba mai ritaya ya shaida wa BBC cewa babu laifi a dauki irin wannan matakin saboda sau da yawa ana samun koke-koke cewa jami'an tsaro ba su da isassun kayan aiki.
"Idan gwamnatocin jihohi ko gwamnoni suka kara musu don su ma su ba da tasu gudummawa kuma zai kara karsashi kuma za su nuna cewa suna godiya da abin da sojoji da jami'an tsaron su ke yi."
A cewarsa, an kai matakin da ya kamata kowa ya ba da tasa gudummawar domin tabbatar da cikakken tsaro amma "duk wani taimako da za a yi ya zama taimako na kayan aiki, taimako na kudi hannu da hannu yana da nashi nakasun."
Masanin ya ce akwai bukatar mahukunta su yi tsarin da zai taimaka wajen tantance mutanen da za a horar tare da danka masu makami…ka da a karshe su dauki kara da kiyashi ko su yi kitso da kwarkwata.
"Idan aka ce za a zabi mutanen gari a basu bindiga, sai a yi kaffa-kaffa a ga cewa ba a ba batagari bindiga ba, saboda idan ka ba batagari bindiga shi kuma maimakon ka nemi gyaran targade za ka nemo karaya - saboda za ka samu mutumin da shi kuma ka bashi damar cin zarafin mutane."
Ya ce mutane wani lokaci "suna kuskure sai suga kamar yaron da ya gagara ko yaro da aka san da kwaya toh irin shi za a je a dauka a irin wannan aiki - toh a gaskiya idan ka yi irin wannan ka daukowa kanka wata rigimar."
Bayanai na cewa matasa da dama daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a Najeriya sun yanke shawarar sadaukar da kansu domin kare al'umominsu.
Sai dai masana na ganin akwai bukatar hukumomi su yi wani tsari na musamman na yadda za a yi da mutanen da aka koya musu sarrafa makami irin bindiga bayan kura ta lafa - wato ko a juya su zuwa cikakkun jami'an tsaro…ko kuma a sama musu wata madogara saboda a cewarsu rashin yin hakan na iya zama matsala.