Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilinmu na raba wa ƴan sintiri bindiga 7,000 – Gwamnatin Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta tabbatar da ƙudirinta na samar da kimanin bindiga 7,000 domin bai wa wasu ƴan sintiri da za ta zaƙulo daga cikin al'umma don aiwatar da wani tsari da ta kira "Carrot and Stick Approach" don fatattakar ƴan bindigar da suka ƙi miƙa wuya.
Mai bai wa gwamnan Zamfara shawara kan harkokin yaɗa labarai, Zailani Baffa ne ya bayyana hakan ga BBC inda ya ce matakin da ake kai yanzu a wannan tsarin shi ne za'a ci gaba da yaƙar waɗanda suka bijriewa sulhu, kamar yadda gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin a zafafa yaƙarsu.
A cewarsa, matakin zai shafi kowane yanki da ƙauyukan da ke da matasa, da sarakunansu suka amince mutanen kirki ne, (Shugabannin Ƙananan hukumomi) za su ba da amincewarsu.
"Gwamnati za ta taimaka musu su samu makamai daga hannun ƴan sanda irin makaman da gwamnatin tarayya ta yadda waɗanda ba irinsu ƴan sanda ko sojoji ke amfani da su ba."
Ya ce ko a ƴan watannin baya-bayan gwamnatinsa ta sanar da burinta na bai wa ƴan jihar da kuma waɗanda ke zaune a jihar damar neman lasisin riƙe bindiga domin kare kansu daga hare-haren masu tayar da zaune tsaye.
A cewar babban dalilin da ya sa aka dauki matakin shi ne ƙarancin jami'an tsaro a ƙasar da za su kare al'ummar kowane yakin na ƙasar.
"Wani lokacin za a samu ƴan ta'addar sun shiga ƙauye da bindiga saboda babu mai bindiga ko ɗaya -su ci karensu ba babbaka, su yi wa mata fyaɗe su, su kwashi dukiya da magunguna a kantin sayar da magani."
Malam Zailani ya bayyana cewa matakin baya-bayan nan ɗaya ne daga cikin matakan da gwamnatinsu take ɗauka "farkon zuwan Gwamna matakin sulhu ya fara ɗauka - da ƴan ta'adda da ƴan sa-kai wato ƴan banga kowa ya ajiye makamansa, waɗanda aka kama su kuma aka ce sai an karɓi fansa a sake su a zauna lafiya."
Ba rashin tasirin matakan da muka ɗauka ba ne ya sa muka sauya salo...
Malam Zailani ya yi iƙirarin cewa ko kadan "ba za mu ce (matakan) ba su yi tasiri ba don mun samu zaman lafiya a jihar Zamfara cikin wata taran farko na Matawalle wanda kuma kowa ya san an koma kasuwa, manoma sun koma kasuwanci, jama'a sun koma hawa kan titi suna yawonsu," ya ce.
"Kuma an yi ta sakin waɗanda aka kamasu ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
"Ya ƙara da cewa matakin farko kafin bai wa ƴan sintirin bindiga shi ne za a miƙa sunayen matasan ga ƴan sanda waɗanda aka tantance su domin kare al'ummarsu kafin sojoji da ƴan sanda su taimaka musu."
Ya jaddada cewa matakin zai tsorata ƴan bindigar saboda "idan suka san akwai masu riƙe da bindiga za su ji tsoron shigowa kuma ko sun shigo za a yi ɓata-kashi kafin ƴan sanda da sojoji su iso."