Zamfara: Nasarorin da ƴan sandan jihar suka ce sun samu cikin wata daya

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, ta bayyana irin nasarorin da ta samu cikin wata ɗaya ta fuskar yaƙi da yan fashin dajin da suka addabi jihar.

Rundunar ta ce ta ƙwato shanu kimanin 70 daga ɓarayin, bayan da jami'anta suka daƙile wani hari da ƴan fashin suka kai kan Kauyen Tudun Masu.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Ayuba Elkana ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai da ya kira don bayanin nasarorin da ya ce sun samu wajen yaki da ƴan fashin cikin makonni uku zuwa hudu da suka gabata.

Ya ce tuni aka gano wasu 60 daga cikin shanun 69 kuma aka mayar da su ga masu su, yayin da aka mika sauran tara ga kwamitin gwamnatin jihar mai tattara dabbobin satar da aka gano.

Sai dai rundunar ƴan sandan ba ta bayyana ƴan sandan da aka kashe ba a artabu da ƴan bindiga da kuma yawan mutanen da ƴan bindigar suka kashe cikin wata ɗaya.

Nasarar da ƴan sanda suka ce sun samu

Kwamishinan ƴan sandan Zamfara ya ce ƙarin wasu muhimman nasarori da rundunar ta samu a tsawon wannan lokaci sun haɗa da gano wasu motoci da bindigogi ƙirar AK47 yayin gwabzawa da yan bindigar a ƙaramar hukumar Maradun ranar 14 ga watan Disamba,

Ta ce ta kuma yi nasarar daƙile wani hari da ƴan fashin suka so kai wa ƙauyen Ruggar Tudu da ke karamar hukumar Bungudu, har ma aka ceto wasu mutum uku da suka so yin awon gaba da su ciki har da jaririya ƴar wata uku da haihuwa, lamarin da ya faru a ranar 15 ga wannan wata.

Sanarwar ta ce a wannan rana ne kuma jami'anta suka samu nasarar kwato ƙarin wasu bindigogi hudu kirar AK47, da gurneti guda ɗaya, da kuma ƙarin wasu manyan bindigogi ciki har da ƙirar GPM, a ci gaba da luguden wuta da ake yi a maɓoyar ƴan bindigar a sassan Shinkafi da Maradun.

Ta kuma ce jami'anta sun kai wa yan bindigar wani harin kwanton ɓauna a dajin Maradun bayan samun sahihan bayanan cewa suna da maɓoya a kauyen Bayan Ruwa, kuma an samu nasarar gano bindigogi ƙirar AK47 guda takwas a tare da su.

Har wa yau rundunar ta kara da cewa jami'anta sun daƙile wani hari da ƴan bindigar suka shirya kai wa wasu garuruwa a ƙananan hukumomin Musawa da ƙauyen Keta a Tsafe, da har ma aka gano wasu bindigogin ƙirar AK47 a can ma a ranar 18 ga watan na jiya.

Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya dai na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, musamman hare-haren ƴan bindiga ɓarayin daji masu kashewa da satar mutane domin kuɗin fansa.

Matsalar ta bazu zuwa jihohin Katsina da Kaduna da Sokoto da jihar Neja.

Kuma duk da iƙirarin da hukumomi da jami'an tsaro ke yi na murƙushe su da kuma matakai da suke ɗauka amma ƴan bindigar na ci gaba da kai hare-hare kan al'umma.