'Akwai matattu cikin motoci da muka kasa yi wa sutura a hanyar Shinkafi '

Wasu rahotannin da BBC ke samu masu daga yankin Shinkafi na jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa jama'ar yankin sun sake afkawa cikin wani mawuyacin hali saboda 'yan fashin daji sun datse wata babbar hanya na tsawon kwanaki. 

Wasu shaidun da BBC ta yi magana da su sun ce hare-haren 'yan bindigar kan matafiya da mazauna ƙauyukan da ke kan hanyar Shinkafi zuwa Gusau sun ƙaru matuƙa.

Wasu mazauna yankin sun ce wasu miyagu 'yan bindiga na tare motoci da satar mutane domin karbar kudin fansa, da kuma sanya mu su harjin amfanin gonar da suka shuka na cikin abubuwa na ukuba da al'umomin Shinkafi ke fuskanta.

Ga abin da wani mazaunin yankin ke cewa: "Tun ranar Talata hanyar nan baki dayanta ba ta hannun hukumomin kasar nan. Daga Talata da Laraba da Alhamis har zuwa Juma'a haka lamarin yake".

Ya kara da cewa tun ranar Talata wasu barayin daji suka tare hanyar: "Ranar Talata an kone mota ta kai hudu kuma an kwashi mutane, haka ma ranakun Laraba da Alhamis."

Ya ce munin lamarin ya kai ga babu wanda ke iya bin hanyar domin irin barnar da barayin dajin ke kai wa.

"Ta kai ga ranar Alhamis, akwai wasu mutanen da suka mutu a cikin motoci amma har yanzu an kasa samun yadda za a je a dauke su kuma a yi musu jana'iza."

Wasu rahotannin da BBC ta samu na cewa barayin dajin na jibga wa mazauna yankin na Shinkafi harajin amfanin gonar da suka shuka.

"Ta kai yanzu idan babu kudi, sai barayin su ce a tara mu su buhuhuwan gero ko wake na adadin kudin da suka aza wa mazauna garin."

Saboda kamarin da matsalar rashin tsaron ta kai, matafiya daga birane kamar Sokoto sun koma bi ta wata hanya mai tsawo da nisa domin kaucewa gamuwa da barayin daji.

Daga Gusau babban birnin jihar Zamfara kuwa, an daina lodin kaya da fasinjoji da zarra yamma ta yi, lamarin da yasa daruruwan fasinjoji ke rasa ta yi a tashar mota, har tana kai ga suna kwana a tashar har sai gari ya waye ko sa sami wasu motocin da za su bi hanyar.