Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙayatattun hotunan auren Yariman Jordan da Rajwa Al Saif
An daura auren Yarima Hussein mai jiran gado na kasar Jordan tare da amaryarsa Miss Rajwa Al Saif a fadar Zahran da ke babban birnin ƙasar Amman a ranar Alhamis.
Baƙi sama da100 ne suka kalli yadda ƙanin yariman, yarima Hashem bin Abdullah, ya raka surukarsa wajen daura auren.
An yaɗa daurin auren Yarima mai jiran gado mai shekaru 28 da Miss Rajwa Al Saif mai shekaru 29 a kasar Saudiyya. An daura musu aure ne a irin biki na addinin musulunci.
'Yan gidan sarauta daga wurare daban-daban na duniya sun halarci taron, ciki har da Yariman Burtaniya da Gimbiyar Wales. Haka kuma akwai Uwargidan Shugaban Amurka Jill Biden da 'yarta Ashley Biden.
Duk hotuna suna ƙarƙashin haƙƙin mallaka.