Me ya rage wa Sheikh Abduljabar bayan yanke masa hukuncin kisa?

Tun bayan sanar da hukuncin rataya kan fitaccen malamin Islama Sheikh Abduljabar Nasir Kabara da wata Kotun Shari'ar Musulunci ta yi a Kano, kusan abin da ake tattaunawa shi ne mene ne abu na gaba bayan yanke hukuncin.
A wannan Alhamis din babbar kotun Shari'ar Musulunci a Kano ta samu Sheikh Abduljabar da laifin yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.
An yanke hukuncin ne bayan da Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.
Kotun ta ce bayan dogon nazari kan abubuwan suka wakana a gabanta bisa dogaro da hujjojin litattafan Musulunci da Hadisai ne, aka yanke masa hukuncin.
Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai na zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa'azinsa.
Sai dai kafin yanke hukuncin a jawabinsa na ƙarshe, Sheikh Abduljabar ya yi ikirarin cewa lauyan da ya nemi afuwa a madadinsa bai san shi ba kuma bai taɓa ganinsa ba.
An dai shafe sama da shekara guda ana dambarwa da kai komo kan wannan shari’a kafin a kai wannan matsayi a yanzu.
To ko mene ne abu na gaba da ya rage wa Sheikh Abduljabar? Usman Mai Keke Lauya ne mai zaman kansa a jihar Kano, kuma ya shaida wa BBC cewa zaɓi biyu suka ragewa malamin a wannan gaɓar.
'Daukaka ƙara ko zaman jiran aiwatar da hukunci'

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Barista Usman ya ce bisa tanadin dokoki da kundin tsarin mulki na Najeriya duk wani wanda aka yanke wa hukunci na da damar ɗaukaka kara zuwa kotu ta gaba domin ƙalubalantar shari'ar bisa hujojji masu ƙarfi.
Sai dai kuma ana iya aiwatar da hakan bisa wasu kwanaki da aka tanada, kuma da zarar mutum ya wuce waɗannan kwanaki babu batun ɗaukaka ƙara, sai kuma jiran zartar da hukunci.
Amma kuma abu na biyu idan ya ɗaukaka kara bisa wasu dalilai da zai ambata, kotu za ta dubi waɗannan dalilai da kuma yadda aka gudanar da shari'ar.
Idan an tabbatar an sauka daga kan layi ko akasin haka ana iya gyaran fuska kan shari'ar.
Amma kuma idan kotu ba ta gamsu da hujojji ko dalilai ko bayanai da aka gabatar ba, to za ta sake jaddada hukuncin farko.
Sannan lauyan ya ce malamin yana da damar roƙon kotu ta ƙara masa lokacin daukaka ƙara, idan kuma har ya zauna jinkiri har kwanaki suka cika shikenan.
"Ita kotu aikinta sauraron kowanne ɓangare ya faɗi ra'ayinsa, idan kotu ta yanke irin wannan hukunci kuma da ya shafi rai, gwamna ke da iko na ƙarshe.
"Domin idan alkali ya yanke hukuncin rataya dole sai gwamna ya sanya hannu kafin a yi wannan hukunci, ba wai kawai kai-tsaye za a aikata ba," in ji Barista Usman.
Barista Usman ya ce in dai aka cike waɗannan ƙa'idoji to babu wani laifi da ya saɓawa kundin tsari ko dokokin ƙasa.
End of Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa
Me Abduljabbar ya ce?
BBC ta yi kokarin ji ta bakin lauyoyin Abduljabbar amma hakan bai samu ba.
Sai dai tun kafin a je ga yanke hukunci, Sheikh Abduljabar Nasir Kabara ya ce bai aikata laifi ba, don haka ba ya nadama.
Ya kuma buƙaci a gaggauta yanke masa hukunci.
Waiwaye

Asalin hoton, Others
Tun a watan Yulin 2021 ne aka fara wannan shari’a ta zargin ɓatanci kan Sheikh Abduljabbar bayan gudanar da muƙabala tsakanin Malamin da sauran Malaman Jihar Kano, bisa bukatarsa ta ƙalubalantarsu kan da'awarsa wadda suke ganin ba daidai yake yi ba.
An yi wa Malamin tambayoyi da dama amma ya gaza amsawa, inda yake ta nanata cewa lokacin da ake ba shi domin ya yi bayanin da'awarsa sun yi masa kaɗan.
Haka dai aka kammala wannan muƙabala ba tare da ya yi bayanin da ya gamsar da malaman da ya nemi zaman muƙabalar da su ba.
Daga baya ya fitar da wani bidiyo wanda a ciki ya nemi afuwar mabiyansa da duk wanda abin ya ɓata masa yana cewa duk abin da yake yi yana yin sa ne domin kare mutuncin janibin Annabi Muhammad.
Kafin mukabalar a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 ne majalisar zartarwar jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar, saboda furta kalaman da ta ce na tunzura mutane ne.
A wancan lokacin gwamnatin ta shaida wa BBC cewa ta yi nazari kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, ciki har daga manyan malamai da hukumomin tsaro, kan kalaman da malamin ke furtawa, shi ya sa ta dauki wannan mataki.
Tun a wancan lokaci ne gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike a kan wadannan zarge-zarge.
Shi dai Malamin ya yi zargin cewa gwamnatin Kano ba ta yi masa adalci ba wajen daukar matakin ba tare da an ji daga nasa bangaren ba.











