'Ba na son na haifi ƴaƴa saboda tsoron sauyin yanayi'

- Marubuci, Navin Singh Khadka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Muhalli ta BBC, a shirin Mata 100 na BBC
Ana yawan wayar da kai game da sauyin yanayi a ƙasashen da suka fi cigaba, amma kuma "damuwa kan yanayi" ko kuma "climate anxiety" a Turance na saka wasu ma'aurata su ƙi haifar yara.
Julia Borges' ta damu da yadda matsalar sauyin yanayi ta ta'azzara a farko-farkon annobar korona, lokacin da ita da sauran mutane ke cikin dokar kulle.
"Na fara hango garinmu da jami'armu a cikin ruwa tsamo-tsamo," in ji mai shekara 23 ɗin, wadda ke karanta harkar noma da injiniyanci a garin Recife na arewacin Brazil.
"Na fara samun damuwa, har ma na fara jin zan iya rabuwa da rayuwata, saboda ban san yadda zan yi da lamarin ba gaba ɗaya."
Kwas ɗin da na yi kan sauyin yanayi ya ɗan taimaka - ta ƙara saka mata ƙaimi na buƙatar da ake da ita na magance matsalar. Nan da nan ta fahimci cewa bai kamata ta haifi jariri ba.
"Ba zan iya kula da rayuwar wani mutum daban ba yadda ya kamata ta hanyar kawo shi ya zama nauyi ga wannan duniyar da dama cike take da abubuwa," a cewar Julia.
A 2022, wata tawaga daga jami'ar Nottingham University ta tambayi manyan mutane a ƙasashe 11 kan ko damuwar da suke da ita game da sauyin yanayi za ta iya hana su haihuwar yara, ko kuma ta sa sun yi da-na-sanin haihuwarsu.
Waɗanda suka ce ba su taɓa jin wannan tunanin ba - ko sau ɗaya ko kuma a lokuta da yawa - sun ƙunshi kashi 27 cikin 100 a Japan da kuma 74 a Indiya. Za a wallafa rahoton binciken a shekara mai zuwa.
Wani rahoton da aka wallafa a mujallar The Lancet kan binciken da aka yi a 2021 kan mutum 10,000 da ke sa shekaru 16 zuwa 25, ya gano cewa sama da kashi 40 na mutanen da suka amsa tambaya a Australia, da Brazil, da Indiya, da Philippines sun ce sauyin yanayi ya sa suna ɗari-ɗarin haihuwar yara. A Faransa, da Portugal, da Birtaniya, da Amurka adadin mutanen ya kama ne tsakanin kashi 30 zuwa 40.
A Najeriya kuwa adadin mutanen kashi 23 ne cikin 100.
Haka nan, sharhi kan waasu binciken 13 da aka gudanar tsakanin 2012 zuwa 2022, da aka wallafa a watan nan a jami'ar University College London, ya gano cewa fargaba game da sauyin yanayi na da alaƙa ƙarara da ƙin haihuwar yara da yawa.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hakan na faruwa ne saboda faragabar da mutane ke da ita cewa tasirin sauyin yanayi zai iya shafar rayuwar yaran nasu, ko kuma kamar Julia, suna ganin yawan yaran zai iya ɗora wa duniya ƙarin nauyi.
Amma kuma wasu binciken da aka yi a Habasha da Zambiya sun nuna cewa mafi yawan mutane na ganin "iyalan da ba su da yawa sun fi samun damar taiamaka wa junansu idan wata annobar muhalli ta faru".
A 2019, mawaƙiya Miley Cyrus ta ce ba za ta haihu ba saboda yanayin da duniya ke ciki, ita kuma 'yar majalisar dokokin Amurka Alexandria Ocasio-Cortez ta tambaya a Instagram ko abu ne mai kyau a haifi yara a wannan duniyar da take fama da sauyin yanayi.
Yanzu irin wannan muhawarar na ci gaba a ƙasashen da ke kan gaba a matsalar sauyin yanayin.
Matsalar Julia ta ƙaru ne a watan Mayun 2022, lokacin da guguwa ta afka wa Recife wadda ta haddasa ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa, abin da ya jawo mutuwar mutum 120 a yankin.
"Kwana uku kacal kafin a fara ruwan sama, na yi wa yara lacca na wata ƙungiya game da rikicin sauyin yanayi. A wajen, nan ne inda ya fi ko'ina fuskantar matsala saboda ambaliya," in ji ta.
"Abin ya girgiza ni sosai ta yadda za mu dinga tunanin yara nan gaba idan na yanzu suna cikin haɗari?"

Asalin hoton, Getty Images
Shristi Singh Shrestha, wata 'yar Nepal mai kare haƙƙin dabbobi, ta kai wa 'yan uwanta ziyara a ƙauye, kuma ta sha mamaki lokacin da ta ga yadda mutane ke zama da yunwa saboda fari.
Dukkan amfanin gonarsu ya bushe kuma ba su iya samun ruwa ba har bayan sun haƙa rami mai tsawon ƙafa 200. A wani ƙauye maƙwabtansu kuma, ambaliya ta share garin.

Shristi mai shekara 40 na cikin damuwa kan sauyin yanayi tun kafin yanzu. Sjekara takwas da suka wuce, ta sha kallon jaririyarta cikin damuwa da tunanin duniyar da za ta samu kanta idan ta girma.
"Fahimtar yadda duniyar nan ke aiki, da yadda sauyin yanayi ke lalata rayuwar dabbobi da yara - wannan abu na saka ni kuka kullum. Lamarin ba ya yi min daɗi," in ji ta.
Daga nan kuma sai ta ci alwashin ba za ta sake haihuwa ba.
Mene ne climate anxiety? (damuwa kan sauyin yanayi)
Daga Caroline Hickman ta Jami'ar Bath
Climate anxiety, ko eco-anxiety - duka dai damuwa kan muhalli ko sauyin yanayi - damuwa ce da muke ji maras matsala idan muka kalli abin da ke faruwa da duniyarmu. Muna fuskantar haɗari cikin sauri saboda sauyin yanayi. Kuma hakan kan sa mu ji damuwa ko fargaba kan rayuwarmu da ta yaranmu a nan gaba.
Ba wai damuwa ba ce kawai, akwai kuma ɓacin rai, da tsananin damuwa, da ɗebe haso, da fushi, da ɗimuwa. Wani zubin mukan ji ɗan ƙwarin gwiwa, amma hakan abu ne mai wuya ya ɗore saboda muna dosar inda bai kamata ba kuma ba mu ɗaukar wani matakin kirki don rage kaifin matsalar yanayin.
Ita kuwa Ayomide Olude mai shekara 24, wadda ke aiki da wata ƙungiyar agaji a Najeriya, fim ɗin da ta ɗauka a wani ƙauye da kusa da ruwa a shekarar da ta gabata ya ƙara mata ƙwarin gwiwar tsanar haihuwa.
Mazauna Folu, kilomita 100 daga birnin Legas, sun nuna mata wani dandalin shaƙatawa a gefen ruwa, wanda a yanzu kusan baki ɗayansa ya nutse a ruwa.
"Idan ana igiyar ruwa yanzu ruwan na kaiwa cikin gari sosai, saboda haka yanzu mutane ke barin gidajensu," in ji Ayomide. "An samu sabbin gine-gine a nan sosai, amma yanzu kuna iya ganin gidajen da mutane suka gudu suka bari kuma wasu ɓangarori na ƙauyen na cikin ruwa yanzu."
Masunta sun faɗa mata cewa sana'arsu na cikin haɗari yanzu saboda igiyar ruwa na ƙara ƙarfi.

Kamar Julia ta Brazil, ita ma tana fuskantar matsai daga al'umma da kuma danginta cewa lallai ta haihu, amma ta ce babu abin da zai sa ta sauya ra'ayi.
"Ran iyayena a ɓace yake, kuma ba mu yin maganar sosai. Ina ƙoƙarin kauce wa tunanin lamarin duk da cewa ni ma ba na jin daɗin abu."
Ita kuwa Shristi, tana fama ne da 'yan uwanta da ke yawan tambayarta wai yaushe za ta haifi ɗanta na biyu.
Amma dukkan mutanen uku sun ce abokan zamansu na goyon bayan matakin da suka ɗauka.
Hanyoyin kula da kai
- Shiga cikin mutanen da ke da tunani irin naku saboda ku samu mutanen da za ku dinga yin hirar.
- Koyi yadda za ku dinga saita tunaninku saboda kada abin ya yi muku yawa. Kasancewa kuna sane da lamarin a kodayaushe kan taimaka. Haka ma duk wani abu da zai inganta kaifin tunani.
- Sai kuma damar sauya damuwa kan yanayi zuwa ɗaukar mataki kan yanayin. Ya kamata mu ji ƙwarin gwiwar cewa mun damu da muhallinmu!
Caroline Hickman, Jami'ar Bath
Julia ta bi wannan sawun. Ta taimaka wajen zana tasawirar wuraren da suka fi shiga haɗarin ambaliya, da zaftarewar ƙasa, kuma take aiki da wata ƙungiya da ke ilimantar da mutane kan yanayi da muhalli.
"Abin da ya taimake ni wajen kawar da wannan damuwar ita ce zama wakiliyar kawo sauyi a unguwarmu," in ji ta.
Duk da haka dai, damuwar tata na nan.
"Har yanzu ina jin wannan rashin ƙwarin gwiwar, amma ina ci gaba da magance ta tare da mai ba ni shawara - kuma yin magana a kan lamarin yana taimakawa."
Ƙarin rahoto daga Paula Adamo Idoeta












