'Ƴan bindiga na ƙona amfanin gonarmu kuma su ƙwace wanda muka girbe'

Asalin hoton, @ALMUSTAPHA.TUBALINMAGAMI
Al’ummar kauyen Gwaram da ke karamar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara, sun koka kan yadda suke fama da hare-haren 'ƴan bindiga ba dare ba rana, wanda baya ga garkuwa da su, ta kai suna ƙona amfanin gonar da suke nomawa.
Mazauna garin sun ce ‘yan bindigar kan tattara abincin da suka noma ne su cinna masa wuta. Wannan lamari dai na barazanar haifar da yunwa a wasu sassan Najeriya sakamakon kalubalen tsaro da manoma ke fuskanta.
Sun ce wannan sabon matakin kona gonakin jama’a da ba a riga an girbe amfanin gona ba, ya kuma saɓa ma tsarin ƙona daji da aka sani a ƙasar Hausa,. Lamarin dai ya jefa manoman cikin tashin hankali.
Daya a daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya shaidawa BBC cewa " Halin da ake ciki 'ƴan bindiga ne ke kunna wa daji wuta, idan ka sare dawarka baka riga ka kwashe ba, za ta ƙone, idan kuma ka sare ta ka ɗaɗɗaure to sai su zo su ƙwace su tafi da ita baka kuma ganin ta."
Manomin ya ce jami'an tsaro na yin iyakar yin su, kawai dai abin nan da hausa kan ec idan dambu yayi yawa ba ya jin mai ne, saboda akwai dazuzzuka dake kusa da mu kuma duk ɓarawon da aka koro daga jihar Kebbi nan ya ke tahowa, haka wadanda aka koro daga Katsina nan suke taruwa.
"Gwamnati tasan da wajen amman duk lokacin da aka tashi shiga dajin ba a kai wa garesu, sai dai a dawo a ce mana anyi aiki, to mu bamu gane kan wannan lamari ba, muna kira ga gwamnatin jiha idan ba ta iya wa ta kai kukan ta wajen gwamnatin tarayya" in ji manomin.
Shima wani manomin da ya nemi BBC ta sakaya sunansa daga garin na Gwaram, ya ce maharan sun addabi makwabtan garuruwan zagaye da su, kazalika ‘yan bindigar ba su da wani nisan a zo a gani da gari.
"Ƴan bindigar sun sanya harajin naira miliyan 20 ga wasu ƙauyuka kusa da mu kuma an basu, abin da hakan ke nufi shine waɗannan garuwa duk sun koma ƙarƙashin ƴan bindiga saboda tare da su suke rayuwa, don hakan duk wanda bai bayar da nashi harajin ba zai fuskanci hukunci," Cewar manomin.
"Inda suke rayuwa ana kawo amsu siminti suna gine-gine kuma aƙalla sun tara buhunnan hatsi sama da 1,000." in ji Manomi
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya shaida wa BBC cewa jami’an tsaron jihar na bibiyar batun, kuma za su tuntube mu daga baya.
Yanayin da ‘yan bindiga suka jefa jihohin arewa maso yamma da wasu sassan Najeriya, ciki har da Zamfarar, ya kawo babban tarnaki a sha’anin noma a Najeriya, abinda ke barazanar aukuwar yunwa da talauci muddin ba ayi wa tufkar hanci ba.











