'Muna rayuwa cikin zulumi sakamakon hare-haren ƴan bindiga'

Al’ummar garin Kidandan, da ke ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, sun koka kan yadda ‘yan bindiga suka hana su sukuni, sakamakon hare-haren da suke kai musu da kuma karbar haraji kafin zuwa gona.
Sun ce sun shafe tsawon watani 'yan bindgar na kai musu hare-hare wanda a wasu lokutan sukan hallaka mutane.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce a yanzu ‘yan bindiga kan ci karensu babu babbaka ba tare da jami’an tsaro sun taka musu birki ba, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.
“Wani lokaci idan suka zo, za su yi harbe-harbe da daddare kawai su fita, wani lokacin idan sun samu sa’a sukan ajiye baburansu a bayan gari, su shigo cikin gari su dauki mutane,” in ji shi.
End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
Mazaunin yankin ya ce ko a baya-bayan nan sai da suka dauki wani matashi wanda yake wa kasa hidima wanda ya mallaki shagon kemis. Ya ce al'amarin ya sa mutane na rayuwa cikin zulumi.
"Mutane ba sa iya barci duk da cewa akwai jami'an tsaro amma ana ganin 'yan bindigar da tsakar rana kuma ba ka da halin da za ka ce za ka kai musu farmaki saboda reshe zai iya juyewa da mujiya,”
"Sannan ba ka isa kana da gona a cikin gari, ka ce za ka je gyara amfanin gonarka ba, matukar ba ka samu daya daga cikin wakilansu ba na cikin gari ka damƙa masa na goro, sannan ya ba ka dama ya tura mutanensu a je a ba ka tsaro har ku je a samu abin da ake so na amfanin gona" in ji shi.
Shi ma dai wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa suna cikin matsananciyar damuwa:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ko dare ya yi za su shigo su dauki mutum, dole mutane su bar gari a irin wannan yanayi saboda akwai wani kauye da kashi biyu na yawan al'ummar wurin sun tashi", in ji shi.
Mazauna yankin sun ce fatansu shi ne mahukutan za su turo da karin jami'an tsaro zuwa Giwa domin a bai wa mutanen garin tsaro.
Rundunar ‘yansanda a jihar Kaduna ta danganta matsalar tsaro da ake fuskanta a Giwa a kan rashin samun bayanan sirri daga mazauna yankin a kan lokaci.
ASP Mansir Hasan shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna:
"Ba ma samun bayanan sirri da wuri, wani zubin har sai lokacin da mutanen suka shigo, za a gan su za su yi wasu abubuwa har sai lokacin da suka yi kokarin daukar mataki ko na hari daga al'umma daga wannan lokacin ne za ka ga an ba mu wannan bayanan sirri", in ji shi.
ASP Hasan ya ce ko a baya-bayan nan sun zauna da mahukantan yankin da suka hada da shugaban karamar hukumar ta Giwa da 'yan majalisunsu inda suka tattauna a kan irin matakin da ya kamata a kara dauka domin tabbatar da tsaro a yankin.











