Bincike ya gano gagarumin cin zarafin yara da naƙasassu a New Zealand

Asalin hoton, AP
Wani babban bincike mai zaman kansa da aka gudanar a New Zealand ya gano cewa an ci zarafin yara da matasa da masu naƙasa har dubu ɗari biyu a cibiyoyin kula da su na gwamnati da kuma na coci-coci tun daga shekarar 1950 zuwa 2019.
Rahoton wanda aka fitar a ranar Laraba, ya nuna cewa hukumomin da kuma majami’un sun gaza karewa ko dakatarwa ko kuma yarda ma da aikata wannan ta’ada, duk da cewa sun san ana aikata hakan.
Rahoton ya nuna cewa cin zarafin da aka yi wa waɗannan yara da matasa da masu naƙasa waɗanda aka danƙa su a hannun cibiyoyin na hukuma da kuma na addini, inda ake sa ran za su ba su kulawar da ta dace, tamkar an yi gudun gara ne aka tarar da zago, inda ya bayyana cewa cin zarafin da aka yi musu ya wuce tunani, kuma abu ne da ba za a taɓa lamunta da shi ba.
Masu binciken sun tattauna da waɗanda aka yi wa fyaɗe, wasu aka yi musu taure don kada su haihu da waɗanda aka riƙa ganawa azaba da lantarki.
Rahoton ya gano cewa mutanen da wannan lamari ya fi shafa su ne ‘yan asalin ƙabilar Maori da mutane masu naƙasa.
Binciken ya nuna cewa ba wai kawai wasu daidaikun mutane ne ba ne kadai suka aikata laifin har da hannun hukumomin da coci-cocin, kuma sannan hukumomi da shugabannin da ke da ikon hana wa sun gaza daukar mataki, kuma hatta zuwa yau din nan abin da ci gaba da wakana kamar yadda rahoton ya nuna, wanda ya wajaba a taka wa lamarin birki daga yanzu.
Firaministan kasar ta New Zealand Christopher Luxon, ya nuna takaicinsa ga lamarin yana mai cewa kasar da ya kamata ta kare mutanen ta kula da su, sai kuma ya kasance ita ce ta ci zarafin nasu.
Ya ce wannan lokaci ne na alhini kuma bakar rana ce a tarihin kasar. Ya kara da cewa kamata ya yi a ce kasar ta tashi tsaye ta hana wannan abu tun a can baya amma abin takaicin ba ta yi ba, amma ya ce su a yanzu lalle za su yi hakan.
Binciken ya gano yadda aka rinka boye masu cin zarafin ana sauya musu wuraren aiki tsawon wadannan shekaru, musamman ma idan malamai ne ko shugabanni na coci.
Binciken na tsawon shekara shida ya biyo bayan irinsa da aka gudanar na tsawon shekara ashirin a fadin duniya, wanda ya kunshi irin yadda wasu kasashe suka yi fama da irin wannan ta’ada ta cin zarafin yara da aka raba su da iyalai ko iyayensu aka kuma danka su a hannun hukuma da cibiyoyi na addini.
Firaministan ya ce ya yi wuri yanzu a ma kiyasta makudan kudaden da gwamnati za ta biya na diyya a kan cin zarafin kudaden da ake ganin za su iya kai wa ga biliyoyin dala











