Babu inda Messi zai tafi, za a goga kafaɗa Man City da Liverpool kan Musiala

Arsenal na duba yiwuwar auko an wasan Brazil mai shekara 22 da ke taka leda a Fluminense, Andre a watan Janairu mai zuwa. (Fichajes - in Spanish)

Manchester City na duba yiwuwar shiga cinikin an wasan Jamus da Bayern Munich Jamal Musiala, za ta yi gogayya da Liverpool da ta daɗe tana nuna muradinta kan ɗan kwallon mai shekara 20. (Football Insider)

Ɗan wasan Inter Miami da Argentina Lionel Messi mai shekara 36 ba ya tunanin tafiya wata ƙungiya aro a yanzu, har sai an fara sabuwar kakar wasa da Amurka da za a fara a watan Fabirairu, duk da cewa ana ganin Barcelona zai tafi. (Fabrizio Romano)

Har yanzu Chelsea na saka idanu kan ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen tsakaninsa da Napoli, lokacin da wasu labarai ke cewa ɗan wasan mai shekara 24 ya amince komawa Liverpool.(TeamTalk)

Idan Har Real Madrid na son ɗaukar dan bayan Bayern Munich da Canada Alphanso Davies to sai ta biya kimanin fan miliyan 40 kan ɗan wasan mai shekara 22. (Bild)

Rangers ta ce nata son tayin da ya kai fan miliyan biyar kafin ta sayar da ɗan wasanta na Ingila Jack Butland mai shekara 30. (TeamTalk)

Da yiwuwar ɗan wasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne mai shekara 31 ya ki sabunta kwataraginsa da Manchester City idan raunin da yaji ya ƙara tsanani. (Football Insider)

Ƙungiyar Fluminense na shirin ɗaukar ɗan bayan Chelsea Thiago Silva mai shekara 39, yayin da ake jita-jitar ɗan wasan Brazil ɗin zai bar Stamford Bridge a ƙarshen wannan kakar.(Fichajes - in Spanish)