Ana zargin wata budurwa da kashe mahaifiyar saurayinta da adda

Hukumomi a Kamaru na zargin wata budurwa da hannu a kashe mahaifiyar saurayinta.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin a garin Fongo-Ndeng da ke yammacin kasar.

Budurwar, Mabel, ta kashe matar, Ma'a Cecilia, mai shekara 64, ne ta hanyar sare mata wuya da adda.

Dattijuwar dai ita ce take nema wa danta auren budurwar, inda kafin a shirya komai, ta dauko ta ta kai ta gidanta suna zaune tare.

Zuwa wurin boka

Sai dai tun bayan nan, budurwar ta yi ta korafin rashin samun barci da daddare, lamarin da ya sa ta je wurin wani boka domin neman mafita.

Bayanai sun ce bokan ya shaida mata cewa hakan alamu ne na maita.

Rahotanni dai sun ce bokan ne ya ba ta shawarar kashe dattijuwar.

Bayan nan, ba ta yi wata-wata ba sai ta faki ido da daddare ta kashe Ma'a Cecilia lokacin da take barci - daga nan ta zare addar da ke hannunta ta sara wuyanta.

Daga bisani kuma sai ta daddatsa sauran sassan jikinta.

A halin yanzu dai budurwar na hannun jami'an tsaro bayan cafke ta da suka yi da zargin kashe dattijuwar.

Bincike ya gano cewa tana dauke da juna biyu na wata biyar.