Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ta sassara gawa ta zuba a cikin akwati domin biyan bashi
'Yan sanda a birnin Yaounde na Kamaru sun kama wata mata a otel dauke da sassan jikin mutum a cikin akwati.
Matar da aka bayyana sunanta da Desire Beyanga an kamata ne a wani otel din Yaounde - Otel Mendzang da ke unguwar Biyem-Assi a karamar hukumar yaounde ta 6 - lokacin da take faman jan babban akwatin da ta loda sassan jikin matar da ake zargin ta kashe.
Dubun Desire ta cika ne bayan ta nuna alamun rashin gaskiya abin da ya sa ma'aikatan otel din bincikar me take dauke da shi, nan take kuma aka ga sassan jikin mutum ne.
Wannan batu ya daga hankalu tare da tuhumar matar domin amsa tambayoyin jami'an tsaro.
Desire ta ziyarci otel dinne tare da wata 'yar uwar mijinta Marie France Mbeya mai shekara 57, hannusu dauke da kwalaben giya, inda su ka nemi a ba su daki.
Yadda ta aikata kisan
A cikin bayananta lokacin da jami'an tsaro ke tuhumarta, Desire ta faɗa mu su cewa jim kadan bayan shigarsu ɗakin otel din kowa dauke da kwalbar giya a hannu, kawai sai ta ɗaga na hannunta ta bugawa 'yar uwar mijinata da kuma soka mata kwalabe.
Ta shaida wa jami'an 'yan sanda cewa ta aikata hakan ne saboda tsananin bashi da ke wuyanta, sannan ta shiga wata kungiya a garinsu inda ta ci bashi har na miliyan hudu a garin mijinta.
Sai dai shekara hudu babu halin biyan bashi, shi ne mijinta ya bukaci su koma birnin Yaounde tare da yaranta su zauna a wajen wani ɗan uwansa.
Desire ta ce bayan komawarsu birnin, wata rana sai ta haɗu da wani mutum a shafin Facebook, kuma suka rinka zantawa.
Bayan sun shaƙu sosai da mutumin na Facebook, sai ta shaida masa irin matsalolinta, shi kuma sai ya yi mata alƙawarin ba ta miliyan biyar idan har za ta iya kai masa gawar mutum.
Hakan ya sa ta je ta kashe 'yar uwar mijinnata da sassara gawarta tare da shirya sassan jikin a cikin akwati a otel din da ta aikata kisan.
Gano ta da jami'ai su ka yi
Dubunta ta cika lokacin da take kokarin fita da akwatin, ganin tana ta fama da nauyinsa.
Ma'aikatan otel din sun shiga zarginta bayan kin amsa tayinsu na daukar ma ta akwatin, nan ne suka shiga zargi da tambayar me a cikin akwatin.
Da fari ta yi musu karyar cewa kayan abinci ne, amma yanayinta ya sa suka tilasta buɗe akwatin, wanda a nan ne suka ga sassan jikin mutum.