Masu neman mafaka, 'yan ci-rani, ko 'yan gudun hijira?

migrants

Asalin hoton, Getty Images

Cikin shekara 20 da suka wuce, ƙaura tsakanin mutane ta kai wani mataki mai babba. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), mutum miliyan 281 sun zauna a ƙasar da ba tasu ta asali ba, ƙarin miliyan 173 a kan na shekarar 2000.

Waɗannan alƙaluman sun kai kusan yawan kashi 3.6 cikin 100 na al'ummar duniya.

Sai dai yadda muke magana kan ƙaurar da mutane ke yi a tsakanin ƙasashe abu ne mai ɗan rikitarwa.

Zuwa yanzu kun ji sunaye iri-iri kamar: baƙin-haure, 'yan gudun hijira, masu neman mafaka, 'yan cirani.

Amma ko a akwai hanya mafi dacewa da za mu iya kiran su? Charlotte Taylor babbar malama ce Cibiyar Baƙin-Haure ta Jami'ar Sussex. Ta yi rubutu kan yadda kafofin yaɗa labarai ke kiran mutanen da ke tsallaka iyakoki. Ta taimaka mana wajen fayyace waɗannan sunaye da muke ta ji.

Baƙin-Haure

migrant woman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Baƙon-haure shi ne mutumin da zai bar wani wuri ya koma wani don yin aiki ko neman rayuwa mafi inganci

Ana yawan siffanta mutane da wannan suna. Baƙon-haure shi ne mutumin da zai bar wani wuri ya koma wani don yin aiki ko neman rayuwa mafi inganci. Saboda haka idan kuna zaune a Birtaniya misali, kuma sai kuka yanke shawarar komawa Sifaniya ddon neman aiki na tsawon wasu watanni, za a iya kiran ku baƙin-haure. Charlotte Taylor ta ce kalmar baƙin-haure a yanzu ba ta da wata sarƙaƙiya, "sai dai kuma ba za ta ci gaba da zama a haka ba. Suna sauyawa a tsawon lokaci". Inda abin yake ɗan rikitarwa shi ne baƙin-haure na siyasa. Wannan na faruwa ne idan mutum ya bar inda yake don ya guje wa wata gwamnati - kamar ta Taliban (a Afghanistan). Charlotte na da 'yar damuwa game da kalmomin da ake alaƙantawa da yin ƙaura kamar a ce: guguwa, ambaliya, kwararar baƙin-haure." Ta yi imanin cewa amfani da irin waɗannan kalamai za su sa mutanen da ke zaune a wata ƙasa da baƙin-haure ke zuwa za su dinga jin cewa baƙin "ba mutane ne suka haife su ba".

'Yan Ci-rani

'Yan cirani su ne mutanen da ke komawa zama a wata ƙasa dindindin - a nan wasu 'yan ciranin Italiya ne a Brazil ke rawar gargajiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan cirani su ne mutanen da ke komawa zama a wata ƙasa dindindin - a nan wasu 'yan ciranin Italiya ne a Brazil ke rawar gargajiya

Wannan na nufin idan mutum ya koma wata ƙasar waje da zama na dindindin. Ba lallai an tilasta musu barin tasu ƙasar ba, zai iya zama don raɗin kansu. Akwai bambanci tsakanin halastattun 'yan cirani da kuma cirani ta ɓarauniyar hanya, bisa kowane irin dalili ne ya sa suka yi ƙaura. Akan bar ɗan cirani ta halastacciyar hanya ya shiga wata ƙasa a hukumance da takardun da suka dace, shi kuma ɗan cirani ta ɓarauniyar hanya ba a batrin sa. Charlotte Taylor ta ce kafofin yaɗa labarai kan yi magana kan shige da fice ba wai cirani ba, wanda ke nufin mutum ya bar ƙasarsa da yake zaune zuwa wata. "Yanzu ana kallon su a matsayin abubuwa mabambanta. Mutane ma ba sa gane alaƙarsu."

'Yan Gudun Hijira

migrant boat

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akan tilasta wa 'yan gudun hijira barin ƙasashensu bisa matsalolin da ba za su iya magancewa ba

Ɗan gudun hijira shi ne mutumin da aka tilasta wa barin ƙasarsa don ya tsere wa yaƙi, ko zalinci, ko kuma wata annoba. "Wannan matsayi na da ya sha bamban sosai," a cewar Dr Charlotte Taylor. "Daga lokacin da ka aminta cewa wani mutum ɗan gudun hijira ne to ka amince ke nan cewa yana da wani haƙƙi. "An tilasta musu shiga halin da suke ciki saboda ba yadda suka iya."

Mai neman mafaka

Wani gungun mutane da aka ceto a Tekun Baharrum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani gungun mutane da aka ceto a Tekun Baharrum

Mutumin da ake kira ɗan gudun hijira zai iya zama dukkan abubuwan nan da muka bayyana a sama, duk da cewa suna neman kariya ne a wata ƙasa daban. Sun ƙunshi mutanen da ke yin hatsabibancin shiga ƙasashe ta ruwa ko kuma ta dandariyar ƙasa. Kalmar "mai neman mafaka" ce Charlotte ta fi natsuwa da ita a irin wannan yanayin. "Idan mutum na neman mafaka, mafaka yake nema." Sai dai 'yan siyasa da wasu kafofin yaɗa labarai a wasu ƙasashe na nuna shakku kan haƙƙin neman mafaka da wasu ke yi. "Na yi matuƙar mamaki da ganin ana bambanta tsakanin masu neman mafaka na gaskiya da na gangan. Za a iya hana su amma maganar [neman] gaskiya ce."