Me ya sa masana’antu ke rufewa a Najeriya?

Ƙofar wani kamfani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya ce ƙasa mafi girman tattalin arziki da yawan al'umma a nahiyar Afirka
    • Marubuci, Habiba Adamu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Najeriya kasa ce da ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afrika, wadda ake yi wa kirarin uwa ma-ba-da mama, sai dai fannin masana’antunta na ci gaba fuskantar koma-baya.

Baya ga arzikin al’umma, kasar ta kasance mai arzikin ma’adanai da yalwar fadin kasa.

Kazalika, ita ce kan gaba wajen hako danyen mai a nahiyar, sannan ta kasance daga cikin manyan kasashe goma da ke hako danyen mai a duniya dake cikin kungiyar OPEC.

Wasu alkaluman hukumar da ke sa ido kan rijiyoyin mai dake cikin teku ta kasar, NUPRC sun nuna cewa a watan Nuwambar shekarar 2023, kasar na hako gangar danyen mai sama da miliyan 1.2 a kullum, adadin da ya haura na shekarun baya.

A bangaren tattalin arziki ma kasar na kan gaba a nahiyar Afirka, musamman kasancewar ta kwashe shekaru tana dogaro da mai a matsayin babbar hanyar samun kudaden shigarta.

Sai dai wannan hanya ta fara zama babbar matsala, musamman a shekarun baya-bayan nan.

Wani bangaren da hukumomi ke ganin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar shi ne bunkasa fannin masana’antu, musamman kanana da matsakaitansu.

Amma hakan na ci gaba da zama babban kalubale, inda masana’antun ke ci gaba da mutuwa maimakon farfadowa.

Matatar man fetur a Najeriya

Asalin hoton, Getty IMages

Bayanan hoto, Najeriya ce kan gaba wajen haƙo ɗanyen man fetur a Afirka - ta haƙo ganga miliyan 1.2 a watan Nuwamba na 2023
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Makamashi jigo ne a wajen tafiyar da masana’antu, sai dai karancin wutar lantarki na ci gaba da yi wa masana’antun kasar kafar-ungulu.

Rashin wutar ya sa kamfanoni da dama rungumar amfani da man dizil wajen gudanar da ayyukansu na yau da kulum.

A cewar mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu na cibiyar hada-hadar kasuwanci ta jihar Kano da ke arewacin kasar, Alhaji Sani Hussaini Saleh, lantarki ce makamashi mafi sauki a wurin 'yan kasuwa.

“Wutar lantarki ce makamashin da ya fi sauki ga masana’antu, amma kamfanoni sun dogara ne da man dizel saboda karancin wutar. Amma tsadar dizel din ya sa a halin yanzu, kamar a jihar Kano masana’antu, musamman kanana da masu matsakaicin karfi, na rufewa saboda babu fita dan sun yi amfani da dizil,” in ji Alhaji Sani.

Ya kara da cewa kananan masana’antun sai sun jira an samu wuta kafin su sarrafa kaya, kuma hakan na shafar yawan abin da suke samarwa da kuma rage tsawon lakacin yin aiki.

"Kwanci-tashi wannan lamari ya kai ga durkushewar masana’antu da dama."

Wani ma'aikaci na kulle ƙofa

Asalin hoton, Getty Images

Man dizel da kudin ruwa

A cewar wani shirin samar da wutar lantarki a Afrika, karkashin hukjumar tallafa wa kasashe masu tasowa ta Amurka, USAID, Najeriya na da arzikin mai da iskar gas da ruwa da kuma zafin ranar da za ta iya samar da megawatt 12,522 na wutar lantarki.

Sai dai kusan a kullum Najeriyar na samar da megawatt da bai wuce 4,000 ba kawai, adadin da ya yi kadan matuka ga al’ummarta kusan miliyan 200.

Haka kuma, masu masana’antun na ci gaba da kokawa kan tsadar shi kansa man dizel din, wanda farashinsa ya rubanya tun bayan da gwamnatin Bola Tinubu ta janye tallafin mai a watan Mayun shekarar 2023.

A cewar mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antun, rashin kasuwa na daga cikin manyan dalilan da ke kawo durkushewar kamfanoni a kasar.

“A halin da ake ciki yanzu, babu kudi a hannun mutane, kuma idan kayan da kake sarrafawa ba su da dangantaka da abinci, kuma suka zama ba na dole ba ne wajen amfanin mutane, sai ya zama kasuwar ta ragu," a cewarsa.

"Hakan ya sa dole kamfani ya rage abin da yake samarwa, don ba zai dinga yin kayan da zai ta ajiyarsu ba a saya ba.”

Wata matsalar da take da nasaba da kudi kuma ita ce ta yawan kudin ruwa da bankunan kasuwanci ke sanya wa masana’antun kasar.

Alhaji Sani ya ce "rashin isasshen jari a bangaren masu masana’antu babbar matsala ce, kuma idan sun je bankunan ana saka musu kudin ruwan da ya kai kashi 24 zuwa 28 cikin 100. Idan ba dan kasuwa ba yaushe masana’anta za ta sarrafa abu har ta sayar ta samu riba kuma ta biya wadannan kudaden”.

A cewarsa, wasu manufofin da gwamnatin kasar ke aiwatarwa sun taimaka wajen durkushewar masana’antu.

“Misali, idan gwamnati ta amince da shigo da shinkafar waje kuma ta zo ta fi ta cikin gida sauki, dole masu yin ta gida su rufe. Kamar a jihar Kano, shigo da atamfofi da sauran kayana sakawa daga waje sun durkusar da masana’antun tufafi da dama a jihar.”

Sai dai ya ce lokaci bai kure ba don akwai matakan da za a iya dauka saboda kawar da matsalar rufewar masana’antu a kasar tare da bunkasa fannin.

“Na farko shi ne samar da wutar lantarki wadatacciya kamar yadda ake samu ba-dare-ba-rana a wasu kasashen nahiyar Afirka, kamar Masar, zai taimaka gaya. Ko kuma ya zama an bai wa fannin masana’antu fifiko wajen ba su wutar lantarki."

Haka kuma, “sanya tallafi a kan man dizel mataki ne da shi ma zai taimaka wa masana’antu”.

“Rage kudin ruwa zuwa kasa da kashi 10 cikin100 da bankuna ke bayarwa, babbar hanya ce da za ta tallafa wa masana’antu, wajen samun isassun kudaden gudanar da ayyukansu.” A cewar Alhaji Sani.

Masana tattalin arziki na ganin inganta fannin masana’antu wani babban jigo ne wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan Najeriya da ke fama da matsalar zaman kashe wando.

Hakan kuma zai taimaka wajen tsamo miliyoyin iyalai daga kangin talaucin da suke ciki a kasar.