Sadio Mane ya ji rauni daf da za a fara Gasar Cin Kofin Duniya

Sadio Mane

Asalin hoton, Getty Images

Sadio Mane ya ji rauni a wasan Bundesliga da Bayern Munich ta doke Werder Bremen 6-1 ranar Talata a wasan mako na 14.

Likitoci za su auna girman raunin da dan kwallon tawagar Senegal ya ji, ya kuma fita daga fili a lokacin Bayern na cin 2-1.

Da wannan sakamakon Bayern ta koma ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Jamus da tazarar maki hudu.

Bayern Munich ta sauya Mane wanda ya fadi a cikin fili a minti na 15 da Leroy Sane.

Ya ji raunin ne kasa da kwana 13 da tawagar Senaegal za ta fara wasan farko a Qatar da Netherlands.

Kociyan Bayern Munich, Julian Nagelsmann ya ce ''Likitoci za su auna girman raunin da ya yi.''

Tsohon dan wasan Liverpool ya wuce kai tsaye dakin da 'yan wasa ke canja kaya, domin a kara duba shi, bayan da aka sauya shi a karawar.

Mane kashin bayan Senegal ne, wadda ta lashe kofin Afirka, za ta fara wasa da Netherlands ranar 21 ga watan Nuwamba, sannan ta kara da Qatar da Ecuador.

Kwallon da Mane ya ci Masar a fenariti ne ya bai wa Senegal damar lashe kofin gasar nahiyar Afirka a Kamaru a 2022 na farko a tarihi.

Mataimakin kociyan Bayern, Dino Toppmoller ya ce dan wasan bai ji girman raunin da mutane ke kwatantawa ba, amma sai an auna shi za a fayyace komai.