WHO ta samar da hanyoyin magance matsalar haihuwa

Lokacin karatu: Minti 2

A karon farko Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta fitar da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar haihuwa.

WHO, ta ce hanya ta farko ita ce zuwa asibiti domin gano ko akwai wata matsala daga wajen ma'aurata domin a magance ta, to amma duk da haka ta yi gargaɗin cewa dole ne a ringa la'akari da lafiyar ƙwaƙwalwar mata da yanayin zamantakewarsu.

Hukumar Lafiya ta Duniyar, ta ce a cikin mata shida da suka isa haihuwa, ana samun mace guda da ke ta faɗi tashin ganin ta samu juna biyu.

Ta ce wannan matsala ba wai ga mata ta tsaya ba, har ma da mazan, to amma a mafi yawancin lokuta an fi ɗora matsalar haihuwar ga mata.

WHO ta ce, kashi ɗaya bisa uku na masu fama da matsalar haihuwa na fuskantar cin zarafi a gidajen auren saboda gaza samun juna biyu.

Hukumar ta ce, mutane ba sa la'akari da cewa wasu matan basu da damar samun zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu, kuma wannan ya dangantaka ne daga yanayin kowacce kasa.

WHO, ta ce idan kuma ma'aurata suka ce za su je asibiti domin ayi musu dashe, kudin fa, don yana da tsada kuma ba kowa ne ke da halin biya ba.

A don haka Hukumar Lafiya ta Duniyar ta jero abubuwa da dama da ya kamata mutane su nesanta kansu daga su idan suna su su haihu, kuma ba wai kawai mata ba, har ma da zaman.

Ta ce, idan ma'aurata na son haihuwa, kuma a cikinsu wanda ke shan taba to ya kamata ya daina.

Haka shan barasa ba, idan akwai mai yi a cikin ma'aurata to ya daina.

Haka sha kwayoyi ma yana daga cikin abubuwan da ya kamata a daina.

Sai kuma sha maguunguna barkatai ba tare da izinin likita ba.

Da dai sauran abubuwan da hukumar ta lissafa.

Abubuwa da dama ne dai ke janyo matsalar rashin haihuwa a tsakanin mata, inda binciken kimiyya ma ya gano cewa gurbatar muhalli ma na janyo matsalar haihuwa a tsakanin maza.

Haka kuma akwai nau'ukan abinci da za su iya taimaka wa ma'aurata samun haihuwa.