Chelsea ta ce Palmer ba na sayarwa ba ne, Onana zai koma Inter Milan

Lokacin karatu: Minti 2

Brighton ta ƙi amincewa da tayin da Nottingham Forest ta yi wa ɗan wasan baya na Ingila mai shekaru 34 Lewis Dunk. (Sky Sports)

Chelsea ba za ta amince a taba mata ɗan wasanta na tsakiya Cole Palmer, mai shekaru 23 ba, yayin da ake alakanta shi da Manchester United, kuma tana ɗaukar ɗan wasan Ingila, wanda ke da kwantiragi har zuwa 2033, a matsayin muhimmin ɗan wasa a nan gaba na ƙungiyar. (Sky Sports)

Amma ana sa ran ɗan wasan gaba na Chelsea din Raheem Sterling zai bar kungiyar kafin lokacin rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta bana, inda ɓangarorin biyu ke tattaunawa kan tashin tsohon ɗan wasan na Ingila mai shekaru 31. (Fabrizio Romano)

West Ham na neman yarjejeniyar aro ga mai tsaron gidan Tottenham na Czech Antonin Kinsky, mai shekaru 22, da kuma mai tsaron baya na Chelsea Axel Disasi, mai shekaru 27, amma Hammers za su mayar da ɗan wasan baya na Brazil Igor Julio, mai shekaru 27, zuwa Brighton don taimakawa wajen cimma yarjejeniyar biyu. (Guardian)

Wakilan mai tsaron gidan Manchester United Andre Onana mai shekaru 29, wanda ke zaman aro a Trabzonspor, sun yi tattaunawa game da komawar dan wasan na Kamaru zuwa tsohuwar kungiyarsa Inter Milan a lokacin bazara. (Mail)

Wolves na tattaunawa don sayen dan wasan tsakiya na Ingila mai shekaru 25 Angel Gomes a matsayin aro daga kungiyar Marseille ta Faransa. (Talksport)

Burnley na tattaunawa da West Ham kan sayen dan wasan tsakiya na Ingila mai shekaru 31 James Ward-Prowse a matsayin aro. (Telegraph)

Sunderland ta yi watsi da rahotannin cewa za a iya barin dan wasan gaba na Spain mai shekaru 20 Eliezer Mayenda ya koma Paris FC. (The I paper)