Kun san abin da ya sa tekun Masar ke cin baƙi duk shekara?

A duk bazara gomman mutane ne ke mutuwa a yankin Ajami na tekun Iskandiriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A duk bazara gomman mutane ne ke mutuwa a yankin Ajami na tekun Iskandiriya
    • Marubuci, Omaima Majdi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • Lokacin karatu: Minti 5

A wajen karshen watan da ya gabata wani mummunan lamari ya faru a bakin tekun Abu Tlat da ke yankin Al-Ajami, a yammacin birnin Iskandiriya na kasar Masar, inda dalibai mata shida da wani dalibin namiji daya suka mutu wasu kuma suka jikkata.

Lamarin ya faru ne a lokacin da tawagar dalibai daga jihar Sohag a daya daga cikin makaratun koyar da aikin otal suka je wajen atisaye.

Bayanai sun nuna cewa igiyar teku ce ta ja daliban yayin da masu lura da su a lokacin suka kasa yin komai su cece su.

Yasser Abdul Majeed, mahaifin Fares, daya daga cikin daliban da ruwan ya ci, ya ce : ''Ina duba Facebook kawai sai na ga labarin abin da ya faru daya daga cikin abokan karatunsu ya sa labarin, daga nan sai na kira shi, inda ya gaya min cewa ai ya rasu.''

Daya daga cikin abokan Fares, wanda yana daga cikin wadanda suka tsira a hadarin na teku, Hani Rashad Abdul Aziz, ya ce: ''Sun dauke mu daga masaukinmu inda suka kai mu bakin teku da karfe takwas na safe suka ce mu shiga teku. Lokacin da muka shiga sai muka ga matan na nutsewa a ruwa, dalibai da dama sun yi kokarin cetonsu. Mun nemi taimako amma ba wanda ya zo, su kuma masu lura da mu na makaranta ba wanda ya iya ruwa ko aikin ceto.''

Mahaifin Fares da dan'uwansa na karbar ta'aziyya
Bayanan hoto, Mahaifin Fares da dan'uwansa na karbar ta'aziyya

Daga bayanin da Hani ya yi, Fares ya yi kokari ya ceci 'yan mata shida kafin igiyar teku ta yi ciki da shi.

Najla Hassan, mai shekara 18, daya daga cikin 'yan matan da suka tsira daga tekun ta yi bayanin yadda lamarin ya faru: "Da farko an gaya mana cewa za mu je bakin tekun ne mu dan gwada, amma ba sai mun shiga can cikin ruwan ba, to amma tuni mun shiga. Wasu daga cikin 'yan matan sun zauna a baki-baki ruwan na jan su ciki. Mun gargadi masu kula da mu a kan abin nan, amma suka ce ai yanzu za a fita. Haka ruwa ya ja su ba wanda ya iya cetonsu. Ni a haka na yi kokari na fice.

Mahaifin Fares ya ce dansa yaro ne mai kokari sosai a makarantar da yake ta karatun aikin likita da jinya.

Wuraren shakatawa na yawan bude-idanu da yashi da igiyar ruwa

Igiyar ruwa na sauyawa sakamakon sauya gabar teku da mutane ke yi
Bayanan hoto, Igiyar ruwa na sauyawa sakamakon sauya gabar teku da mutane ke yi

Gwamnatin Iskandiriya ta ce an fara bincike kan abin da ya janyo hadarin, tare da duba matakan da aka dauka na kiyaye hadura a lokacin ziyarar daliban.

Hukumar birnin ta ce bakin tekun na Ab Talat ba waje ne da ya kamata a je wanka ko wasa ba a wani lokaci saboda hadarin da ke tattare da wajen na karfin igiyar ruwa.

Hukumomin birnin a karon farko tsawon lokaci sun sa an rufe wuraren wasa na bakin teku na biranen Iskandiriya da Alamein da Baltim, saboda irin ayyukan da mazauna kauyukan bakin tekun ke yi na sauya yanayin bakin ruwan wanda hakan yake sauya yanayin igiyar ruwa.

Abin da hukumomi ke gargadi da a daina yi saboda akwai bukatar samun izini da shawarar kwararru a kan hakan.

A lokuta da dama hukumar hasashen yanayi na fitar da sanarwa inda ake roko da jama'a da masu yawon bude idanu su yi hankali da zuwa bakin teku, saboda haukan da ruwan ke yi a wasu lokutan.

Teku na fushi ta cinye yankuna da ke kusa da ita

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da yadda ake yawan samun hadarin da teku ke cin mutane, gwamnan jihar Iskandiriya Manjo Janar Ahmed Khaled, ya ce yawan hadarin ya ragu a wannan shekarar da kashi 70 cikin dari idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ya ce an samu raguwar ne sakamakon matakai da ake dauka da kuma horo da ake kara bai wa masu aikin ceto.

Daga irin wadannan matakan wadanda suka shafi yaki da sauyin yanayi da gwamnatin Masar ta fara a 2019, tana kokarin samar da kariya ga mazauna yankunan bakin teku da ke kwari.

Haka kuma hukumomi na samar da hanyoyin sa-ido da nazarin sauyin yawan ruwan teku da kuma yadda yake cin yankunan bakin ruwan.

Wani binciken da Israa Al-Masri na Jami'ar Iskandiriya ya yi ya nuna cewa yankin gabar teku ( tsakanin Hyena da Ras al-Hikma) da ruwa ke cinyewa a duk shekara tsakanin 1990 zuwa 2020, yana da yawa.

Girman ya yi yawa sosai idan aka kwatanta da wanda rahoton Bnkin Duniya ya bayar a kan yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Yamma.

Rahoton ya nuna cewa gabar tekun Bahar Rum ta Masar na rasa kusan kafa digo uku (0.328084 ko 10cm), inda ruwa ke cinyewa a duk shekara tsakanin 1984 da 2016.

Sauyin yanayi ma na janyo sauyi a yadda bakin teku yake

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sauyin yanayi ma na janyo sauyi a yadda bakin teku yake

Shugaban majalisar tabbatar da ayyukan raya kasa na Masar, Imad El-Din Adly, ya yi nuni da cewa sauyin yanayi da karuwar ruwan teku da ake dangantawa da dumamar yanayi, da yawan ruwan sama da sauyin yanayin zafi da sanyi da ake gani sosai, duka wadannan na janyo sauyi a yanayin bakin teku.

Haka kuma duka wadannan abubuwan da sa ruwa ya cinye yankunan da ke gaba cikin sauri, wanda kuma ba a ganin hakan a da, a cewar shugaban.

Jami'in na ganin rashin wayar da kan masu yawon bude idanu ya kara hadarin mutuwa a ruwa, musamman ma idan ba su kiyaye da gargadin masu kula da bakin tekun ba.

Ta yaya za mu yi maganin fushin teku?

Kwararre a kan harkar teku Sabri Al-Jundi ya gabatar da wasu shawarwari ta yadda za a kiyaye hadari tare da kare lafiyar masu yawon bude idanu a bakin teku, kamar hakan:

1- A rika bayar da horo lokaci zuwa lokaci ga dukkanin masu ninkaya

2- Samar da kayayyaki na zamani na aikin ceto

3 - Kada a dogara ga masu nutso ko ninkaya mutane kadai

4- A tabbatar da cewa mutane na bin dokokin hukuma da ke kula da bakin tekun

5- Kada a je bakin teku ranar da igiyar ruwa ke da karfi ( teku ke hauka)

6- Ma'aikatar kula da albarkatun ruwa ta rika nazai tare da bayyana wa jama'a wuraren bakin teku da ke da hadari.

7- A sanya abubuwan da za su hana mutane shiga wurin da ke da hadari.