Yadda ƴanfashi ke 'cin karensu babu babbaka' a yankin Bukuyum

Ƴan bindiga

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 4

Jami'ai a yankin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce ƴanbindiga sun halaka mutum fiye da goma da raunata wasu da a dama a wani hari da suka kai a wasu ƙauyuka da ke yankin.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba lokacin da 'yanbindigar suka yi wa mutane kwanton bauna.

Hon Hamisu A. Faru ɗan majalisar jiha a Zamfara da ke wakiltar yankin ya shaida wa BBC cewa maharan sun kai hari ne a ƙauyen Adafka tare da yin garkuwa da mutane.

''Kawo yanzu ban san adadin mutanen da suka tafi da su ba'', kamar yadda ya bayyana.

Ya ce jami'an tsaron da ke garin tare da haɗin gwiwar askarawan Zamfara da ƴan sa kai sun bi sawun ƴanbindigar, lamarin da ya sa maharan suka yi musu kwanton ɓauna, inda suka halaka da dama da cikinsu.

''Lamarin da ya sa sukab kashe mana mutum 12 tare da raunata wasu da dama da tuni aka garzaya da su asibiti'', a cewar Hon Faru.

Ɗanmajalisar ya ce al'ummar yankin na cin halin fargaba da kaɗuwa sakamakon halin da suke ciki, na fuskantar hari a kowane lokaci.

''Mun sha faɗin cewa yankin Bukkuyum babu zaman lafiya, mutane suna cikin fargaba, mata da maza koyashe sai turuwar fishewa daga yankunansu suke yi saboda matsalar tsaro,'' in ji shi.

Mutane na jana'iza

Matakan da majalisar jihar ke fatan ɗauka

Dan majalisar ya ce abin da majalisar jihar ke fata daga hukumomin sojin ƙasar shi ne a kai wa ƴanfashin hari cikin sansanoninsu da ke dajin Gando da ƴarjiji da Mazaaro, kamar yadda a baya a ka kai hari kan sansanonin ƴanbidigar a dazukan Zurmi da Tsafe.

Haka kuma Hon. Faru ya ce mataki na biyu da majalisar jihar ke fata shi ne jami'an tsaro sanya shingayen binciken jami'an tsaro tun daga Mayinci har zuwa garin Gummi.

Ɗan majalisar ya ce a kan hanyar ne kwanakin baya aka sace mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum - wanda har yanzu yana hannun ƴanbindigar.

''Gani suke ba za a iya yin komai ba shi ya sa suke cin karensu babu babbaka a hanyar, yanzu haka da rana tsaka ko da safe suna fitowa su kai hari'', in ji shi.

Koken Majalisar Wakilai kan Bukkuyum

Majalisar wakilai

Asalin hoton, NASS

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A makonnin da suka gabata ne Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi gwamnatin ƙasar ta ɗauki ƙarin matakan tsare rayuka da dukiyoyin mazauna ƙauyukan ƙaramar hukumar ta Bukkuyum.

Bukkuyum na da nisan kilomita kusan 176 daga Gusau babban burnin Zamfara.

Ɗanmajalisa mai wakiltar Gummi/Bukkuyum, Sulaiman Abubakar Gumi, shi ne ya gabatar da ƙudiri a gaban majalisar, inda a ciki ya bayyana girman matsalar.

Majalisar ta kuma bayyana irin matakan da suke ganin ya kamata a ɗauka domin kare rayuka.

Daftarin ƙudirin da BBC ta gani ya nuna cewa a ranar 21 ga watan Janairun 2025 'yanfashin daji sun kai hari tare da ƙona motocin soja biyu.

Kafin haka, a ranar 19 ga watan na Janairu 'yanfashin suka kashe wani matashi, sannan suka yi garkuwa da mutum bakwai a garin Nasarawa Burƙullu.

Sun kuma sace mata 29 da maza takwas a ƙauyen Kamaru duka a ƙaramar hukumar ta Bukkuyum.

Haka ma a ranar 9 ga watan Janairu ƴanfashin sun kashe jami'an tsaron sa kai na jihar, CPG a kan titin Gurusu zuwa Nasarawa Burƙullu a lokacin da suka yi musu kwantan ɓauna.

Sannan a ranar 6 ga watan na Janairu, gomman ƴanfashin dajin haye kan babura suka farmaki garin Gana na yankin karamar hukumar, tare da sace mutum 50 galibinsu mata da ƙananan yara da kuma tsoffi, bayan da suka kashe wasu tare da lalata dukiyoyi, sannan suka cinna wa ƙauyen wuta.

Bayanan majalisar sun ce wata bakwai kafin harin ranar 6 ga watan Janairu, mazauna gundumar Gana sun yi yarjejeniyar zaman lafiya da ƴanbindigar, inda suka biya miliyoyin naira a matsayin haraji domin amun damar noma gonakinsu.

Bayanai daga yankin sun nuna cewa ƴan fashin dajin na ɓoye a dazukan da ke tsakanin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Anka, sannan sun fara kai hari gundumar Adabka a Bukkuyum makonni kafin su kai harin na ranar 6 ga wata a gundumar Gana.

Rundunar tsaron haɗin gwiwa ta samu nasarar daƙile harin kodayake ta rasa jami'inta guda, kamar yadda bayanan majalisar suka nuna.

Matakan da Majalisa wakilai ta nemi a ɗauka

Majalisa

Asalin hoton, NASS

Ta buƙaci ma'aikatar bayar da tallafi da magance aukuwar bala'o'i ta samar da kayan agaji ga al'umomin da suka rasa muhallansu a yankunan da lamarin ya shafa a ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Haka kuma majalisar ta buƙaci babban hafsan tsaron ƙasar da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, ya gaggauta samar da sansanonin soji a yankunan Yashi da Ruwan Jema da kuma Kyaram, domin magance matsalar tsaro a yankunan.

Sannan majalisar ta yaba wa sojojin ƙasar, kan ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙar ƴanfashin a jihar Zamfara da yankin arewa maso yammaci da ma ƙasar baki ɗaya.

Daga ƙarshe majalisar ta ɗora wa kwamitocin tsaro da na soji da na bayar da agajin gaggawa da na kare aukuwar bala'o'i da na kula da ƴangudun jihira su tabbatar da aiwatar da waɗannan matakai.