Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta soke fiye da kashi 80 na shirye shiryen hukumar USAID
An soke mafi yawancin shirye-shiryen Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka (USAID) baya makwanni shida ana gudanar da bincike, kamar yadda sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya sanar.
A shafinsa na X, Rubio ya ce shirye shirye ne da aka kashe wa ''biliyoyin dala a hanyoyin'' da suka yi wa muradun Amurka illa
A yanzu ma'aikatar kula da harkokin waje ta ƙasar ce za ta riƙa kula da kashi 18 na shirye shiryen da suka rage.
Ƙungiyoyin agaji a sassan duniya sun yi gargaɗin cewa matakin da ake ta cece-ku-ce a kai na kawo ƙarshen shirye-shiryen bayar da agajin da Amurka ta daɗe tana yi ya haifar da mummunan sakamako a duniya, wanda zai iya jefa rayuka cikin hatsari.
Gwamnatin Trump ta sha bayyanawa ƙarara cewa tana son kuɗaden da ake kashewa a ƙetare su yi daidai da tsarinta na " Amurka ce a gaba'' watau ''America First".
Jim kaɗan bayan Trump ya koma fadar White House a ranar 20 ga watan Janairu, aka sa dubban ma'aikatan hukumar ta USAID yin hutu, kuma waɗanda ke aiki a ƙasashen waje su koma gida .
Me ya sa Trump ke son a rufe Hukumar USAID?
A cikin wani umarni da ya sanya wa hannu a ranarsa ta farko kan mulki, Trump ya kuma matsa da dakatar da tallafin da ake ba ƙasashen waje tare da ba da umarnin sake duba ayyukan USAID a ƙasashen ƙetare, ƙarƙashin jagorancin Elon Musk da ma'aikatar kula da inganci ayyuikan gwamnati watau DOGE.
An kuma soke dubban kwangilolin samar da ababen more rayuwa da ci gaba , kuma a ƙarshe an kori dubban ma'aikata.
A sakon da ya walafa a shafin X, Rubio ya ce bayan binciken da aka yi, Amurka " a hukumance" ta kawo ƙarshen ayyuka kusan 5,200 daga cikin shirye-shiryen USAID 6,200.
Rubio ya ƙara da cewa "A cikin tattaunawar da Majalisa, muna da aniyyar barin sauran kashi 18% na shirye-shiryen .... don gudanar da su yadda ya kamata a ƙarƙashin kulawar Ma'aikatar Harkokin Wajen."
Ƴan jam'iyyar Democrat da ƙungiyoyin jin ƙai daban-daban sun bayyana rufe shirye-shiryen USAID - waɗanda Majalisar dokokin ƙasar ke ɗaukar nauyinta - a matsayin lamarin da ya saɓawa doka, wanda ya haifar da ƙararraki da dama.
An dai ɗorawa Hukumar ta USAID nauyin ayyuka iri-iri a faɗin duniya, tun daga gano yunwa zuwa rigakafin cutar shan inna da kuma samar da gidajen dafa abinci cikin gaggawa a yankunan da ake fama da rikici.
Tuni dakatar da tallafin tare da kawo ƙarshen shirye shiryen suka soma tasiri
A Sudan, alal misali, dakatar da agajin jin ƙai ta haifar da rufe wuraren dafa abinci na jama'a sama da 1,100 da aka kafa domin taimakawa waɗanda yaƙin basasar ƙasar ya rutsa da su.
An kiyasta cewa kusan mutane miliyan biyu ne abin ya shafa.
A Oman, matan Afghanistan da dama da suka tsere daga gwamnatin Taliban don neman ilimi mai zurfi a yanzu suna fuskantar komawa bayan an dakatar da tallafin karatu da USAID ke ba su .
A wani misali kuma , asibitin farko da ke kula da masu sauya jinsi a Indiya ya rufe rasansa a garuruwa uku bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da tallafin da ake ba shi.