Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu cutar HIV na kokawa kan rufe USAID
Mike Elvis Tusubira, wani direban tasi ɗan ƙasar Uganda, ya kasance yana rayuwa da cutar HIV tun 2022, lokacin da gwaji ya nuna yana ɗauke da ita.
A wajensa - Hukumar ba da agaji ga kasashen duniya ta Amurka, USAID, ta zamo alheri ga mutum miliyan 1.4 da ke rayuwa da HIV a Uganda. Ya ce a tsawon watanni uku masu zuwa, "lamarin zai kasance mutuwa ko rayuwa".
"Dakatar da dukkan ayyukan USAID ya shafe ni matuka. Ban san me zan yi gaba ba. Me zai faru da ni?"in ji shi.
"Likita na ya faɗa min cewa ya bar asibitin da nake zuwa. Me zai faru da yarona da kuma abokiyar zama ta?".
"Ina cikin damuwa kan makomata. Kuma babu makomar ma a zahiri. Saboda babu gidajen tsauro, babu magunguna, babu kwaroron-roba, babu komai ba."
Gwaji ya nuna matar Mike ba ta ɗauke da HIV - kuma tana amfani da wani magani da ke rage barazanar kamuwa da cutar.
Tun da aka dakatar da ayyukan hukumar ta USAID, shi da abokiyar zamansa sun kasance ba su samun magani kamar a baya. Rashin tabbas ya janyo dangantakarsu ta fara samun matsala.
Uganda na cikin ƙasashe goma na farko a Afrika da ke karɓar tallafi daga USAID. A cewar bayanan gwamnatin Amurka, ƙasar ta samu tallafin kiwon lafiya dala miliyan 295 daga hukumar a cikin shekarar kuɗi ta 2023—inda ta zo matsayi na uku bayan Tanzaniya da ta samu dala miliyan 337, sai kuma Najeriya dala miliyan 368.
Ɓangaren kiwon lafiya a Uganda ya dogara sosai kan tallafi da ake bai wa ƙasar.
USAID tana tallafawa shirye-shiryen ƙasar kan kiwon lafiya da ya kunshi na HIV da zazzaɓin cizon sauro da tarin fuka da kuma kuturta. Haka kuma tana ba da tallafin ayyukan kula da lafiyar mata da yara da taimakon lafiya na gaggawa.
Uganda na samun taimako daga ƙasashen waje a ɓangaren HIV da ya kai kashi 70.
Ma'aikatan lafiya da abin ya shafa
Dubban ma'aikatan lafiya ne dakatar da tallafin da USAID ke yi ya shafa.
Shamirah, ma'aikaciyar asibiti ce tare da wata ƙungiya mai suna Reach Out Mbuya (ROM)— wata ƙungiyar da ke ba da tallafin lafiya ga mutanen da ke ɗauke da HIV a Uganda.
Ta kasance a cibiyar Kiwon lafiya ta Kisenyi, wadda ke taimakawa ɗimbin mutane a Kampala.
A kiyasi, tana duba majinyata kusan 200 masu ɗauke da cutar HIV da tarin fuka a kullum. Amma bayan umarnin dakatar da aikin USAID, dukkan ma'aikatan kiwon lafiya na ƙungiyar ta ROM sun rasa ayyukansu.
Lamarin ya janyo yanzu sashen tarin fuka na asibitin ya tsaya cik. Haka kuma an kai ga rufe sashen kula da marayu da marasa galihu—wanda USAID ke tallafawa.
"Muna jira tsawon kwanaki 90. Don haka, ban shirya wa wannan hutun dole ba," in ji ta.
"Abin ya kasance ba za to ba tsammani, ba mu da isasshen lokacin da za mu shirya. Ba mu samu lokacin miƙa komai a wurin ba. Kawai muka daina aiki."
Martanin gwamnatin Uganda
Ma'aikatar lafiya ta Uganda ta ce tana binciken hanyoyin da za a haɗa muhimman ayyuka a cikin harkokin kiwon lafiya na yau da kullum domin rage cikas ɗin da za a samu.
"Saboda haka, ma'aikatan da ke da niyyar ci gaba da aiki a matsayin sa-kai har sai mun daidaita da gwamnatin Amurka, ana buƙatarsu da su tuntuɓi daraktocin asibitoci ko kuma ofishina," in ji wata sanarwa daga sakatariyar dindindin a ma'aikatar lafiya ta ƙasar, Dr. Diana Atwine.
Fargaba a Malawi
An tsayar da ayyukan USAID a gaba ɗayan yankin kudanci a Malawi.
An rufe kofofi, motoci na yashe babu wani aiki a asibitin Macro Mzuzu, wanda ya kasance babban asibiti da ke ba da kulawa kan cutar HIV a yankin arewacin ƙasar.
A cewar Eddah Simfukwe Banda, wata mazauniyar Malawi, wadda ta dogara da asibitin da ake yi mata maganin cutar HIV, ta ce asibitin ya kasance babu kowa tun bayan da aka ba da umarnin dakatar da aiki.
Ko da bayan ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ba da izini a ranar 28 ga Janairu na isar da magungunan HIV kamar ARV, yawancin asibitocin sun kasance a rufe.
Aikin rarraba magunguna ya kasance babban kalubale, ganin cewa babu ƙwararrun ma'aikata da za su iya tsara ayyukan USAID.
Ko da a wuraren da aka ba da izinin ci gaba da ayyuka, yawancin ayyukan kwangiloli sun kasance cikin ruɗani. Ma'aikatan lafiya ba su da tabbacin abin da za su iya yi da kuma wanda ba za su iya ba.
Gwamnatin Trump na shirin rage ma'aikatan USAID da fiye da kashi 90 cikin ɗari.
Atul Gawande, tsohon jami'in hukumar ta USAID, ya wallafa a shafin X cewa, za a rage ma'aikatan hukumar daga 14,000 zuwa 294—inda ma'aikata 12 kacal za a tura Afrika.
Sama da ƙungiyoyi masu zaman kansu 30 ne lamarin na dakatar da tallafin USAID ya shafa.
Malawi ta samu dala miliyan 154 daga kasafin ɓangaren lafiya na hukumar ta USAID a shekarar 2023, wanda hakan ya sa ta kasance kasa ta 10 mafi girma a nahiyar Afrika da ta samu irin tallafin.
Ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin mafi talauci da kuma ta fi dogaro da agaji a duniya.
A cewar Bankin Duniya, Malawi na da tarin matsaloli - da suka kunshi fari na tsawon lokaci, da guguwa da kuma ƙarancin saukar ruwan sama .
Waɗannan matsaloli sun ƙara saka ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar cikin mawuyacin hali.
Eddah Simfukwe Banda, tana cikin damuwa game da makomarta—da ta kanwarta mijinta, wadda ita ma ta dogara da magungunan da ake ba da tallafinsu.
"A matsayinmu na mutanen da ke kan maganin ART muna da zaɓi da yawa. Dole ne mu yi addu'a a matsayin ƴan Malawi. Waɗanda suka yi imani kuma suka dogara ga Allah cewa muna da Allah wanda yake buɗe kofa idan an rufe ta, "in ji ta.
An tilasta wa wata ƙungiyar lafiya mai suna Right to Care, da ke samun tallafi daga USAID, dakatar da muhimman ayyukanta, ciki har da shirye-shiryen wayar da kai ga masu neman jinsi ɗaya a arewacin Malawi.
Wani jami'in ƙungiyar ya kwatanta asibitin da suke kula da cewa ya zama tamkar kufai, babu kowa inda likitoci kalilan ne ke zagayawa.
Rashin makoma mai kyau
Hukumar yaƙi da cutar HIV ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce makomar ƙasashe ba abu ne mai kyau ba.
A 2023, an samu mutum 630,000 da suka mutu sakamakon cutar HIV/AIDS a faɗin duniya sannan miliyan 1.5 suka kamu da cutar.
Yayin da ake samun raguwar alkaluman masu kamuwa da cutar a ƙasashe da lamarin ya fi shafa, dakatar da tallafin USAID zai janyo wannan nasara da aka samu ta zama a banza.
"Idan ka ɗauke wannan tallafi da gwamnatin Amurka ke bayar wa, muna tsammanin za a iya samun ƙarin mutum miliyan 6.3 da za su mutu sakamakon HIV a cikin shekaru biyar masu zuwa," a cewar babban darektan hukumar UNAIDS yayin tattaunawa da BBC.
"Za a samu sabbin mutum miliyan 8.7 da za su kamu da cutar, da kuma ƙarin marayu miliyan 3.4 sakamon HIV. Ba na son a ɗauke ni kamar wani mai shaci-faɗi, amma ya zama dole in ba da waɗannan alkaluma saboda mun hango za su iya afkuwa."
Wani abin damuwa ga kwararru a ɓangaren lafiya shi ne rashin amfanin magani. A cewar ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF), duk wani jinkiri da aka samu a maganin HIV, hakan zai janyo babban barazana.
"Duk wani cikas a kula da masu ɗauke da HIV zai iya janyo barazana," a cewar Tom Ellman, darektan sashen magani na MSF a kudancin Afrika.
"Mutane su kasance suna shan magungunan HIV a kowace rana - idan ba haka ba lamarin zai janyo barazana har ta kai ga mutuwa."
Ita ma Byanyima ta nuna irin wannan damuwa.
"Wani mutum ɗauke da HIV ya kwatanta lamarin da yanayin mutuwa. Don Allah ku yi wa gwamnatin Amurka magana. Wannan lamarin yana da haɗari ga rayuwarmu. Idan ban samu magani na a wata mai zuwa ba da kuma na gaba, wani tsawon lokaci zan ɗauka ina rayuwa?'"
Shin Afrika za ta iye cike giɓin?
A tsawon gomman shekaru, Amurka ta kasance babbar mai hulɗa da ƙasashen Afrika a ɓangaren lafiya.
Tun bayan kaddamar da shirin Pepfar, shirin da ke taimakon nahiyar Afirka wajen yaƙi da cutar HIV a 2003, shirin ya ceto rayuka sama da miliyan 25.
"A bara, USAID ta ce ta ba da tallafin dala biliyan takwas ga Afrika. Kashi 73 na tallafi ya tafi ɓangaren kiwon lafiya," a cewar babban darektan hukumar takaita yaɗuwar cutuka ta Amurka (CDC), Jean Kaseya a tattaunawarsa da BBC a wani shiri ranar 29 ga watan Janairu.
Ƙwararru a ɓangaren kiwon lafiya sun yi gargaɗin cewa maye gurbin wannan tallafi zai kasance abu ne mai wahala.
Gwamnatocin Afrika sun yi hoɓɓasa wajen rage dogara ga agaji da suke samu. A yanzu Kenya na ba da tallafin kusan kashi 60 na ɓangaren yaƙi da HIV a ƙasar. Afrika ta Kudu kuma kashi 80.
Amma ga ƙasashe da ba su da karfi, tarin basussuka da bala'o'in sauyin yanayi da kuma matsalar tattalin arziki, sun janyo matsala wajen yaƙi da cutar.
Shugaban ɓangaren lafiya na Amref a Afrika, Dr Githinji Gitahi, ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki nan take ba, yanayin lafiya a duniya na cikin babban barazana.
"Wannan zai buƙaci gwamnatocin Afrika da kuma hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afrika (CDC) su ƙara yawan tallafi da suke bayar wa, wanda da wuya duba da irin tarin basussuka da ƙasashen ke ciki," in ji shi.
"Yayin da ake ƙara samun faruwar abubuwa kama daga sauyin yanayi da rikice-rikice," wannan duniya za ta ci gaba da yin tangal-tangal da kuma zama cikin rashin tabbas - ba ga Afrika kaɗai ba, amma ga kowaye."