Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta ce tana bincike kan zargin USAID da tallafa wa Boko Haram
Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya ce akwai cikakken shirin sanya ido da bibiya wajen gano gaskiyar ko tallafin da Amurka ke bayarwa na kai wa ga wurin da aka nufa.
A wata sanarwa da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, Amurkar ta yi alawadai da ayyukan ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta'adda a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Sanarwar da ƙara da cewa a "2013 ne dai Amurka ta ayyana ƙungiyar Boko Haram a matsayin ƙungiyar ƴanta'adda, inda ta rufe duk waɗansu kadarorin da ƙoƙorinta na neman gidauniya da kuma gurfanar da mambobinta tare da hana su tafiye-tafiye zuwa Amurka."
Ofishin Amurkar ya kuma ce ƙasar Amurka na ci gaba da aiki tare da Najeriya da sauran ƙasashen Afirka wajen yaƙar ayyukan ta'addanci.
Mene ne zargin da ake yi wa USAID?
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai wani ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya bayyana cewa hukumar raya ƙasashe ta Amurka ,USAID ce ke samar wa ƙungiyoyin ta'adda da suka haɗa da Boko Haram kuɗaɗe.
Mista Perry wanda ya yi batun lokacin wani sauraron rahoton kwamitin majalisar a kan yadda hukumomin gwamnatin Amurka ke aiwatar da ayyuka da sarrafa kuɗaɗe tun bayan da shugaba Donald Trump ya ce bai ga amfanin hukumar ba.
Wannan ne ya sa wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin Najeriya ɗaukar matakin gabatar da ƙudiri a gaban majalisar dokokin ƙasar.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta gudanar da bincike kan iƙirarin da wani dan majalisar dokokin Amurka ya yi na cewa hukumar USAID da gwamnatin Trump ta rufe ta tallafawa kungiyoyin ta'addanci da suka hada har da Boko Haram a ƙasar.
Ndume ya ce ba batu ba ne da ya kamata gwamnatin Najeriya ta naɗe hannunta, la'akari da girman barnar Boko Haram a jihar Borno.
Ya ce zai gabatar da kudiri kan binciken zargin dan majalisar dokokin na Amurka.
"In an tashi binciken za mu yi tambayoyi, saboda haka zamu bincika domin mu ƴan Najeriya da abun ya shafa ya kamata mu sa ido don a san matakan da za a dauka, saboda ba ƙaramin barna Boko Haram suka yi mana ba," In ji Ndume.
Sanata Ndume ya yi zargin cewa USAID ba ta aiki tare da hukumomin da ya kamata ta yi aiki tare da su a Najeriya, lamarin da ya ke dasa ayar tambaya, "Ba sa bari jami'an tsaronmu su snaya ido kan abubuwan da suke yi ballantana su bada shawara.
Hukumar bada agaji ta Amurka, USAID an kirkire ta a shekarun 1960 domin taimaka wa ayyukan agaji a madadin gwamnatin Amurka a kowanne yanki na duniya.