Me ya kamata a yi don farfaɗo da darajar naira da ke ci gaba da karyewa?

Asalin hoton, CBN
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
'Yan Najeriya da masana tattalin arzikizi na ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda darajar kuɗin ƙasar wato naira ke ci gaba da faɗuwa babu ƙaƙƙautawa.
A baya-bayan nan darajar nairar ta yi mummunan faɗuwa da aka jima ba a ga irinta ba, wani abu da ke ƙara alamta irin koma-bayan tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
A cikin makon nan, sai da dalar Amurka guda ta kai naira 1,710 a kasuwar bayan fage, yayin da ka sayar da dalar a kan naira 1,660 a bankunan ƙasar.
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan Bankin Duniya ya lissafa naira cikin kuɗaɗen da darajarsu ta fi faɗuwa a yankin kudu da hamadar saharar Afirka a 2024.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta sha ɗaukar matakai daban-daban domin farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar.
A baya babban bankin ƙasar, CBN ya yi alƙawarin cewar zai bai wa 'yan kasuwar canji dala a farashi mai sauki, a wani yunƙuri na farfaɗo da darajar nairar.
Haka kuma hukumar EFCC mai yaƙi da almundahana a ƙasar ta riƙa kai samame a baya kan 'yan kasuwar canji a biranen Abuja da Kano da Legas da ta su ke haifar da karyewar darajar kuɗin ƙasar.
To amma bisa ga dukkan alamu ire-iren waɗannan matakai ba su yi tasiri ba, domin kuwa har yanzu kullum darajar naira sai ƙara narkewa take yi.
Abin da ke haifar da ƙaruwar matsalar

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana tattalin arziki sun bayyana wasu dalilai da suke ganin a matsayin waɗanda suka hana ruwa gudu dangane da farfaɗowar darajar naira.
Farfesa Muhammad Muttaka Usman, malami ne a fannin tattalin arziki a jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya ce matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka ba sa kawo wani sauyi dangane da farfaɗo da darajar nairar.
Masanin ya ce babban abin da ke ƙara haifar da faɗuwar darajar naira shi ne rashin sarrafa kayyakin da take sayarwa a ƙasashen waje.
''Kowace ƙasa kuɗin na yin daraja ne idan tana sarrarafa kayayakin da take fitarwa domin sayarwa a kasuwannin duniya, wannan shi ne dalilin da zai sa a buƙaci ƙuɗin ƙasar domin a sayi wanna kaya da take sarrafawa'', in masanin tattalin arzikin.
Ya ƙara da cewa ''idan ka lura a cikin wannan lokaci Najeriya ta shiga wani yanayi da da ba ta iya fitar da komai, mafi yawan masana'antunta sun durƙushe ta yadda ba sa iya sarrafa komai''.
A nasa ɓangare, Dakta Bashir Muhammad Achida malama a jami'an Usaman Danfodio da ke Sokoto ya ce buƙatar kayyakin ƙasashen waje da ke yawan ƙaruwa tsakanin 'yan Najeriya shi ke ƙara haifar da karyewar darajar naira.
''A duk lokacin da aka tashi sayo irin waɗanna kayayyaki dole sai an canja naira zuwa kuɗaɗen ƙasar da ake son sayo kayayyakin, kuma hakan ko shakka babu yana kara haifar da karyewar darajar naira'', in ji Dakta Achida.
Ya ƙara da cewa ''yanzu a Najeriya idan ka lura mafi yawan abubuwan da muke amfani da su abubuwa ne ake sarrafawa daga ƙasashen waje, kama daga makamashi da sutura da man girki da na'urori da sauran abubuwan amfanin yau da kullum, duk daga ƙetare muke sayo su. To don haka dole ne darajar kuɗinmu ta ci gaba da zubewa''.
Wani abu da da ke ƙara haifar da karyewar darajar naira a cewar Farfesa Muttaqa shi ne ƙarin kuɗin ruwa da babbankin bankin Najeriya, CBN ke yawaita yi.
''Karin kuɗin ruwa ma sai dai ma ya hana zuwan masu zuba jari cikin ƙasar, saboda yawancin kuɗin da ke Najeriya ba a cikin bankuna suke ba. Ana ƙarin kuɗin ruwa ne don mutane su riƙa kawo kudinsu bankuna, amma yawanci ba ahaka abin yake ba a Najeriya'', in ji masanin tattalin arzikin.

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Achida ya kuma cewa wani ƙarin dalilin shi ne yawaitar kewayawar kuɗi a cikin ƙasar.
Ya ce idan gwamnati na yawan fitar da kuɗi suna yawan zagayawa a cikin kasa, to kuɗin za su yi yawa a cikin ƙasa, ta yadda yawansu zai fi yawan buƙatun da ake da su a cikin ƙasar, lamarin da masanin ya ce zai sa mutum ya biya kudi masu yawa domin a yi masa wani aiki ko a ba shi wani kaya.
''Hakan zai sa farashi ya yi sama, kuma zai sa darajar kuɗin ya karye'', kamar yadda ya yi bayani.
Abu na gaba kamar yadda Farfesa Muttaƙa ya yi bayani shi ne koma bayan tattalin arzki da Najeriya ke fuskanta.
Malamin jami'ar ya ce inda ƙasar na da ingataccen tattalin arziki to hakan zai sa mutane masu zuba jari su riƙa zuwa ƙasar domin kawo kuɗinsu don zuba jari da nufin samun riba.
''To a nan ma idan ka duba rashin tabbas da tattalin arzikin ƙasar ke fuskanta ga matsalar tsaro, duk sun taimaka wajen hana masu zuba jari zuwa ƙasar, domin kawo kudinsu'', in ji shi.
Me ya kamata gwamnati ta yi?

Asalin hoton, .
Farfesa Muttaƙa ya ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙarin inganta masana'antun ƙasar, ta yadda za su riƙa aiki tare da sassara kayyakin da 'yan ƙasar ke buƙata ba saiu sun sayo su daga ƙasashen ƙetare ba.
''Wannan kuwa za a cimma shi ne ta hanyar samar da wadatacciyar wutar lantarki, tare da inganta harkokin tsaron ƙasa ta yadda masu zuba jari daga ketare za su iya zuwa su zuba jarinsu ba tare da wata fargaba ba'', in ji shi.
Dakta Achida ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali wajen sarrafa albarkatun ƙasar da Allah ya hore wa ƙasar kamar man fetur da sauran ma'adinan da ƙasar ke da su domin ta riƙa sayar da su zuwa ƙasashen ƙetare.
''Idan ta yi hakan to tabbas darajar naira za ta inganta, saboda dole za a riƙa buƙatar nairar daga ƙasashen waje domin sayen kayyakinmu, wanda hakan kuma zai taimaka wajen inganta darajar kuɗin'', in ji malamin jami'ar.
Farfesa Muttaƙa ya ce dole ne gwamnati ta ɗauki matakan rage shigo da kayyakin bu katu daga ƙasashen waje, a mayar da hankali wajen alkinta wanda ake da shi a ƙasar.
Ya ce akwai buƙatar gwamnati da babban bankin ƙasar su ƙara samar da wasu tsare-tsaren da za su inganta darajar naira, ganin cewa matakan da ake ɗauka yanzu na fama da ƙalubale daban-daban.
Dakta Achida ya ce wani abu da ya kamata gwamnati da CBN su yi shi ne ɓullo da wani tsari ta yadda duk wanda ke buƙatar chanjin kuɗin ƙasar waje, to a samu wata takarda da zai cike bayanansa da dalilin da ya sa yake son chanji da kuma abin da zai yi da shi.
''A wasu ƙasashen, idan kana son kuɗin wata ƙasa, to dole ka bi wasu matakai irin waɗannan, amma mu a Najeriya an bar abu sakaka, ko canjin nawa kake so, za ka iya samu a duk lokacin da kake so kuwa'', in ji shi.
Wani abu da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don farfaɗo da darajar naira a cewar Dakta Achida shi ne ta ƙulla yarjejeniya da ƙasashen da take sayo wasu kayyaki, ta yadda suma za su riƙa sayen abubuwan da suke buƙata daga Najeriya.
''Idan muna sayen wani abu a wata ƙasa, sai mu cimma yarjejeniya da ita, kan ita abin da take buƙata daga ƙetra, idan muna da shi, to sai mu ma mu riƙa sayar mata da shi.''
''Wannan abu ne da dokokin kasuwanci na duniya suka tanada, wato bani gishiri in ba ka manda, kuma tabbas hakan zai inganta tattalin arzikinmu tare da farfaɗo da darajar kuɗin ƙasarmu'', a cewar masanin tattalin arzikin.











