Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal da Man U da Chelsea na rububin Stankovic, Pochettino zai koma Tottenham
Tottenham ta nuna sha'awar daukar dan wasan gaba na Chelsea Christian Pulisic, mai shekaru 27, wanda bayanai ke cewa a shirye yake ya koma Ingila daga AC Milan a wannan bazarar. (Teamtalk)
Spurs na kokarin neman koci na wucin gadi kafin su sake nada kocin Amurka Mauricio Pochettino bayan gasar cin kofin duniya ta bana. (Sun)
Paris St-Germain ta shirya fafatawa da kungiyoyin Premier League Chelsea, da Manchester United da Tottenham kan dan wasan tsakiya na Kamaru Carlos Baleba mai shekaru 22 na Brighton. (Fichajes)
Manchester United na da kwarin guiwar cewa dan wasan baya na Ingila Harry Maguire, mai shekaru 32, zai tsawaita kwantiraginsa a Old Trafford, bayan karshen wannan kakar wasa. (Teamtalk)
Newcastle United za ta ba da fifiko ga siyan ɗan wasan gaba a lokacin bazara, inda ƙungiyar ta riga ta nemi sayar da Nick Woltemade ɗan ƙasar Jamus mai shekaru 23 bayan siyansa a watan Agusta. (Football Insider)
Dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski, mai shekaru 37, zai jira ya yanke shawara kan makomarsa bayan zaɓen sabon shugaban kungiyar da za a yi a watan Maris. AC Milan, Atletico Madrid, da Chicago Fire, da Fenerbahce da wasu a Saudi Arabia na nemansa. (Mundo Deportivo)
Manchester United, Arsenal, Chelsea da Tottenham suna cikin kungiyoyin Premier da ke sa ido sosai kan dan wasan tsakiya na Club Brugge da Serbia Aleksandar Stankovic, mai shekaru 20. (Teamtalk)
Ana sa ran Manchester United za ta tura wakilan kulob din don kallon dan wasan baya na Faransa Pierre Kalulu mai shekaru 25 na Juventus lokacin da kungiyarsa za ta fafata da Inter Milan ranar Asabar. (Tuttosport)
Manchester United na bin diddigin dan wasan baya na Gambia da Tromso Abubacarr Sedi Kinteh, mai shekaru 19, da kuma dan wasan baya na tsakiya na Valencia Hugo Fernandez, mai shekaru 18. (Mail)