Stones zai bar Man City, Tottenham na son Rudiger

Lokacin karatu: Minti 1

Bayern Munich na son ɗauko golan Brighton mai shekara 23 Bart Verbruggen a wannan baraza. (Talksport)

Chelsea za ta yi hamayya da Bayern kan Verbruggen kuma za ta iya biyan farashin fam miliyan 50 na golan ɗan ƙasar Netherlands. (Teamtalk)

Ɗanwasan baya na Manchester City da Ingila John Stones na shirin barin ƙungiyar a wannan bazara idan kwangilar shi ta kawo ƙarshe, kuma Bayern Munich ta nuna tana son ɗanwasan mai shekara 31. (Caught Offside)

Atletico Madrid na son ɗauko ɗanwasan baya na Chelsea da Spain mai shekara 27 Marc Cucurella. (Fichajes - in Spanish)

Aston Villa na son ɗanwasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Morgan Gibbs-White, amma Forest za ta nemi fam miliyan 65. (TeamTalk)

Borussia Dortmund za ta sabunta kwangilar Nico Schlotterbeck na Jamus yayin da Real Madrid ke farautar ɗanwasan mai shekara 26. (Bild - in German)

Tottenham za ta karɓo ɗanwasan Real Madrid da Jamus Antonio Rudiger a matsayin madadin ɗanwasan bayan Argentina Cristian Romero idan ya koma Bernabeu. (Fichajes - in Spanish)

Tsohon kocin Marseille Roberto de Zerbi yana nazari kan yiyuwar karɓar aikin horar da Tottenham, duk da alaƙanta shi da Manchester United. (TeamTalk)

Juventus da Inter Milan na hamayya kan golan Tottenham da Italiya mai shekara 29 Guglielmo Vicario. (Gazzetta - in Italian)

Manchester United ce kan gaba a hamayyar sayen ɗanwasan gaba na Everton da Senegal mai shekara 25 Iliman Ndiaye. (Teamtalk)