Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe wannan masoyin Manchester United ɗin zai yi aski?
- Marubuci, Elizabeth Conway
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Football reporter
- Lokacin karatu: Minti 4
Wani ƙaramin abu da ya fara kuma ya sanar a shafin sada zumunta, bayan kwana 493, yanzu ya zama wani gagarumin abu da shi kansa bai yi tsammani ba.
A ranar 5 ga watan Oktoban 2024 ne Frank Ilett ya wallafa wani bidiyo a shafinsa, lokacin da ya yi aski na ƙarshe, kuma ya ce ba zai ƙara yin aski ba har sai Manchester United ta lashe wasa biyar a jere.
A wancan lokacin ya tambayi ƴan tsirarun masu bibiyar sa, yaushe suke ganin zai yi aski na gaba: a 2024, 2025 ko 2026?
Daga cikin mutum 27,000 da suka amsa tambayarsa, kashi 90 sun ce a 2026.
Bayan canjaras ɗin da West Ham ta yi da Manchester United (1-1) a ranar Talata, wannan ɗan taliki zai ci gaba da jira.
A yanzu Ilett na da mabiya sama da miliyan 2.3 a shafinsa na sada zumunta sannan ya gabatar da shiri kai-tsaye a shafinsa na YouTube a lokacin wasan West Ham da United a ranar Talata, inda a wani lokaci sama da mutum 100,000 suke kallo kai-tsaye.
Lokacin da ya yi magana da BBC, bayan kwana 365 da yin aski na ƙarshe, Ilett ya ce 'ba aski' idan 'babu nasara' wani abu ne da ya fara domin faranta wa magoya bayan Manchester United rai a daidai lokacin da ƙungiyar ke cikin ƙalubale.
"Kawai so nake yi na kawo wa magoya bayan Manchseter United farin ciki a wannan lokaci da ƙungiyar ke cikin wani hali," in ji shi.
Ilett ya ce tun asali bai ɗauki abin a matsayin wani abu babba ba - kawai dai wani abu ne na raha a lokacin da ƙungiyar take faɗi-tashi.
''Na zaci cewa abin ba zai wuce wata uku zuwa huɗu ba," kamar yadda Ilett ya shaida wa BBC. "Abu ne kawai na raha, shi ke nan. Ashe na yi kuskure a hasashena."
Lokaci na ƙarshe da Manchester United ta yi nasara sau biyar a jere shi ne tsakanin watan Janairu da Fabrairun shekara ta 2024.
Ilett ya ce "kamar jiya na fara wannan abin."
Lokaci na ƙarshe da ƙungiyar United ta daɗe ba ta yi nasara a wasa biyar a jere ba, sai da ta kwashe kwana 902, inda ta karya ƙwarin a watan Janairun 1999.
"Na yi tunanin cewa ƴar matsala ce kawai ta ƴan kwanaki, musamman ganin cewa United ta lashe kofin ƙalubale a watan Mayu. Ban yi tunanin cewa abin zai yi ta ƙara muni ba har ya yi tsawo haka," in ji shi.
Yayin da watanni suka fara tafiya ba tare da United ta samu nasara biyar a jere ba, sai batun ya fara shahara. Abin da aka fara shi kamar wasa, sai ga shi ya zama wata alama ta halin ha'ula'i da ƙungiyar ke ciki.
Aka riƙa yaɗa yadda gashin Ilett ke ci gaba da taruwa, a matsayin tunatarwa a kowane mako kan yadda ƙungiyar ta lalace.
"Taruwar gashina wata alama ce ta cewa Man Utd na a wani matsayi da bai dace da ita ba, na san hakan ne ya sanya ƙungiyar ba su min magana ba - amma ina ganin yayin da lokaci ke tafiya kuma ake samun kyautatuwar al'amura ƙila su tuntuɓe ni," in ji shi.
Yayin da yake ci gaba da samun shahara, hakan ya kawo masa alfanu na kuɗi da sanayya fiye da yadda ya yi tsammani.
"Yanzu ba abu ne na ni kaɗai ba, akwai mutane da yawa da ke bibiya. Saboda haka ba zan iya dakatawa ba," in ji shi
A yanzu Ilett na da jami'in karɓar tallace-tallace kuma ya haɗa gwiwa da manyan kafafen sadarwa, inda yake samun kuɗaɗe masu tsoka.
Haka nan yanzu yana da kamfanin da ke kula masa da hulɗa da gidajen jarida.
Lokacin da aka tambaye shi ko a ina yake sa ran yin aski idan lokacin ya zo, Ilett ya shaida wa BBC cewa wuri ɗaya yake tunani a ransa.
"Idan har za su amince min, zai yi kyau a yi askin a filin Old Trafford, kuma sannan ya kasance ɗaya daga cikin yan wasan ƙungiyar ne zai yi askin, amma dai za mu ga yadda za ta kasance idan lokacin ya matso," in ji shi.