Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amorim ya kafa tarihin cin ƙwallo sama da biyu a wasan farko a Old Trafford
Manchester United ta doke Everton 4-0 a wasan mako na 13 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.
Marcus Rashford ne ya fara cin ƙwallo tun kan hutu, na shida da yake da hannu a cin Everton daga karawa ta takwas kenan.
Bayan da suka koma zagaye na biyu United ta karasa zura uku a raga ta hannun Joshua Zirkzee, sannan Rashford ya ci na biyu kuma na uku, sai Zirkzee ya kara na huɗu kuma na biyu a wasan.
Wannan shi ne karon farko da sabon koci Ruben Amorim ya ja ragamar United a Old Trafford a Premier, bayan maye gurbin Erik ten Hag, wanda aka kora cikin watan Oktoba.
Kenan Amorim ya zama kociyan United na farko a wasan Premier a gida da ya ci ƙwallo sama da biyu, karon farko da United ta zura 4-0 a bana a gasar.
Tun kafin nan ya fara jan ragamar United a Premier da ya je ya tashi 1-1 a gidan Ipswich ranar 24 ga watan Nuwamba.
Haka kuma kociyan ya ja ragamar United ta doke Bodo Glimt 3-2 a Europa League a Old Trafford ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba.
United tana ta tara a teburin Premier da maki 19, bayan cin wasa biyar da canjaras huɗu aka doke ta karawa huɗu daga fafatawa 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ranar Laraba 4 ga watan Disamba United za ta je Emirates, domin buga wasan mako na 14 a Premier League.
Daga nan za ta karɓi bakuncin Nottingham Forest a Old Trafford a dai gasar ta Premier League ranar Asabar 7 ga watan Disamba.