Maguire ba zai bar Man Utd ba, Al-Ittihad na son Salah

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan tsakiya na Nottingham Forest Morgan Gibbs-White zai bar ƙungiyar inda Aston Villa ke ganin ya dace da ita. (Teamtalk)

Ɗanwasan baya na Ingila Harry Maguire, mai shekara 32, ga alama sai sabunta kwangilar a Manchester United. (Mail - subscription required)

Real Madrid na neman ɗanwasan baya kuma kaftin Tottenham Cristian Romero shi take farauta. Ana kuma alaƙanta ɗanwasan na Argentina mai shekara 27 da Barcelona da Atletico Madrid. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Kungiyar Al-Ittihad na son ɗanwasan gaba na Liverpool da Masar Egypt Mohamed Salah a wannan bazara. (Foot Mercato - in French)

Bayern Munich ta fara tattaunawa da ɗanwasan gaba na Ingila Harry Kane kan sabuwar yarjejeniya kuma tana da tabbacin zai sanya hannu. (Sky Sports)

Liverpool na kan gaba wajen farautar matashin ɗanwasan Bournemouth mai shekara Eli Junior Kroupi. (Caught Offside)

Leeds na son lale fam miliyan 30 domin ɗauko golan Manchester City mai shekara 23 James Trafford. (Teamtalk)

Brighton ta amince da tayin Nottingham Forest a Janairu kan ɗanwasan baya na Ingila Lewis Dunk amma ya nuna ba ya son tafiya. (Sky Sports)

Crystal Palace ta rage farashin ɗanwasan Faransa Jean-Philippe Mateta na fam miliyan 30 yayin da Manchester United ta nuna tana so. (Football Insider)

Manchester United da Chelsea na hamayya kan ɗanwasan baya na Tromso da Gambia Abubacarr Sedi Kinteh. (Mail)

Juventus da duk wata ƙungiyar Serie A sai suna fuskantar cikas kan albashin ɗanwasan tsakiya na Newcastle United Sandro Tonali. Kungiyoyin Italiya ne ke farautar ɗanwasan haɗi da Manchester United da Arsenal. (The Athletic)