Ba ma tilasta wa kowa shiga jam'iyyarmu — APC

Asalin hoton, Facebook
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi martani ga gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, game da zargin da ya yi mata na amfani da ƙarfi wajen tursasa masa komawa cikinta.
A baya-baya nan ne aka jiyo gwamnan na PDP na cewa APC na bin wannan hanya wajen jan ra'ayin sa kamar yadda ta yi wa wasu gwamnoni da aka ga sun koma jam'iyyar.
A cewar jam'iyyar ta APC, abin mamaki ne yadda gwamna Mutfwang ya bayyana abin da babu shi a zahiri, da zummar karkatar da hankalin jama'a daga gazawar gwamnatinsa wajen sauke nauyin da al'ummar jihar suka ɗora mata.
APC ta ce bai kamata jama'a su gaskata abin da gwamnan ya faɗa ba na cewa ana ƙoƙarin yi masa dole, duk da ƙarfin da yake da shi a matsayinsa na gwamna.
Malam Bala Ibrahim, shi ne daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar APC a Najeriya ya shaida wa BBC cewa, basu tilasta wa kowa shiga jam'iyyar ta su.
Ya ce," Abin muke yi shi ne muna nunawa jama'a irin abubuwan alkhairi da jam'iyyarmu ke yi kamar yadda dimokradiyya ta tanada, to wannan shi ke kwadaitawa masu komowa jam'iyyar su ga cewa ya kamata su rabu da jam'iyyarsu su koma APC.
Malam Bala Ibrahim, ya cem"Ba bu wanda ke matsawa wani musamman ace ma gwamna,kuma shi wanda ya ce ma ana matsa masa ya kawo hujja, wannan magana ce ta mutum na son shigowa jam'iyyarmu amma ya ke tayar da kura domin ya gwada kwanji ya ga cewa idan ya koma APC za a karbe shi ko akasin haka."
To sai dai duk da wannan ikirari na APC, wasu makusantan gwamnan na Filato irinsu Nuru Shehu Jos, na ci gaba da jaddada abin da gwamnan ya faɗa.
Ya ce," Kowa ya sani a fadin Najeriya APC na matsawa gwamnonin jam'iyyar adawa da lallai sai sun koma jam'iyyarsu ta APC, to idan aka samu jajirtattun mutane irinsu Muftwang, babu wata barazana da zata sa ya bar jam'iyyar PDP."
"Idan aka duba yadda gwamnoni da 'yan majalisu ke komawa jam'iyyar APC to ai an san akwai wani abu a kasa."In ji shi.
Ba gwamnan jihar Filato ne kaɗai ke zargin APC da amfani da ƙarfinta a matsayinta na jam'iyyar mai mulki wajen tursasawa mutane shiga cikinta ba.
A yayin da ake tsaka da wannan tababa dai, wasu majiyoyi na cewa akwai ƙarin wasu gwamnoni da 'yan majalisa da ke kan hanyarsu ta komawa jam'iyyar APC, ko da yake galibinsu na bayar da na su dalilan da suka sha bam-bam da wannan.











