Amfanin gwanda ga lafiyar jikin ɗan'adam

Gwanda

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Itacen gwanda na da alfanu sosai - kama daga ganyensa, ƴaƴansa har ma ga ɗaukacinsa.

Gwanda ya fito ne daga dangin itatuwa na Caricaceae masu kama da lemu, ƴaƴansa cikinsa kuma baƙaƙe.

Turawan mulkin mallaka ne suka kawo itacen nahiyar Afrika da kuma Indiya, kamar yadda masana suka bayyana.

A cewar kwararru, itacen gwandar na da nau'in miji da mace.

Nau'in mace ne na itacen ke samar da ƴaƴa masu daɗi wanda muke ci.

Amfanin gwanda ga lafiyar jiki

Gwanda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Launin gwandar na kasancewa kore - inda yake komawa ruwan ɗorawa idan ya nuna

Launin gwandar na kasancewa kore inda yake komawa ruwan ɗorawa idan ya nuna.

A wannan lokaci ne ake cin ƴaƴan itacen kuma yana da daɗin gaske.

Ruwansa yana da ɗanɗano mai daɗi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Itacen na ɗauke da sinadarai masu gina jiki.

A cewar ƙwararru, gwanda na ɗauke da wasu sinadarai da ke sanya jiki aiki yadda ya kamata.

A cewar Alfred Kanssou, wani ƙwararre kan abinci mai gina jiki a Cotonou, ya ce gwanda mai nauyin kilogram 100 na ɗauke da sinadaran gina jiki da yawa.

"Ba na buƙatar ci gaba da sayan sinadarin Vitamin C, gwanda na ɗauke da sinadarin sosai a cikinsa wanda shansa yadda ya kamata zai wadatar a jiki. Itace ne da na kan yawan bai wa mutanen da ke neman Vitamin C cikin abinci su ci," in ji wani mai suna Uncle Charles.

Ƙwararru kan ɓangaren abinci mai gina jiki sun yi iƙirarin cewa mutum zai iya samun yawan vitamin C da yake nema wajen cin gwanda.

Itacen na kuma ɗauke da sinadarin vitamin A, wanda yake da muhimmanci musamman ga mata.

Har ila yau, itacen gwanda na ɗauke da sinadarin vitamin E, B5, B9 da kuma sinadarin potassium.

A cewar Dakta Kanssou, yana da kyau a bari har sai gwanda ya nuna kafin a sha shi, domin more alfanunsa, musamman sinadarin vitamin E.

"Shan gwandar da ta nuna, na taimakawa mutum yin bahaya cikin sauki, kuma ƙwararru sun ce yana kare mutum daga kamuwa da cutar kansa. Shi ya sa a kodayaushe nake son kasancewar wannan ɗan itace a gida na," a cewar Charles.

Gwanda na da alfanu ga masu ciwon suga

Itacen gwanda na da alfanu ga masu ɗauke da cutar suga - wanda bai wuce mataki na biyu ba.

Carotenoids da ke cikin itacen na taimakawa wajen yaƙi da ciwon suga.

Amfanin ganyen gwanda

Gwanda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Itacen gwanda yana a matsayin magani na wasu ciwuka.

Ganyen gwanda na taka muhimmiyar rawa wajen magance gajiya saboda wasu abubuwa da ganyen ke da shi.

Ana amfani da ganyen ne ta hanyar saka wani adadi a cikin ruwan zafi don shan shayinsa.

Ana shan shayin sau uku a rana.

Ana amfani da ganyen kuma wajen yin magani.

Yana warkar da ciwuka kamar cizon sauro ƙaiƙayi da kumburin ƙafa.

Samun itacen gwanda a gida abu ne mai muhimmanci, a cewar ƙwararru.