Me ya sa Rasha ke ɗaukar nauyin horar da ƴanjarida a ƙasashen Afirka?

A promo for RT Academy with the tagline, "Become part of RT."

Asalin hoton, RT Academy website

Bayanan hoto, Ɗaruruwan ƴanjarida da masu amfani da kafofin sadarwa na zamani ƴan Afirka sun shiga cikin shirin samun horon wanda kafar watsa labarai ta Rasha RT ɗin ta shirya.
    • Marubuci, Global Disinformation Unit
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

A bayaninsa na gabatarwa ga ƴanjarida daga Afirka da suka halarci taron horo na musamman, daraktan kafar watsa labarai ta RT, wadda gwamnatin Rasha ke ɗaukar nauyi, ya ce: "muna ɗaya daga cikin kafofin da ke kan gaba wajen bin diddigi, kuma ba a taɓa samun mu da yaɗa labarin ƙarya ba."

Jawabin, wanda aka nuna wa ɗaruruwan ƴan jaridan ta intanet, na cikin jawaban da aka gabatar wajen horar da ƴanjarida na ƙasashen duniya da kafar watsa labaran ta Rasha ta shirya a bara.

Wani ɗan jarida na BBC ya shiga cikin masu samun horon domin bin diddigi tare da binciken yadda za ta kaya.

RT kafa ce da aka kora daga turai da Amurka, kuma aka ƙaƙaba wa takunkumi saboda yaɗa labaran ƙarya.

Yadda kafar RT take nuna duniya

Burtaniya ta danganta kafar da "kafar yaɗa farfagandar Rasha" sannan an hana ta watsa labarai a Burtaniya da Canada da Turai da Amurka bisa yaɗa labaran ƙarya game da yaƙin Ukraine, kafar ta RT (wadda a baya ake kira da jaridar Russia Today), sai ta assasa horo na musamman ga ƴanjarida daga kudu maso gabashin Asiya da China da Afirka.

RT ta ce shirin horar da ƴanjaridan na Afirka shi ne mafi nasara, inda ƴan jarida sama da 1,000 da masu amfani da kafofin sadarwa na zamani daga ƙasashe 35 suka halarta. Ba mu tabbatar da adadin mahalarta samun horon ba, amma mun ga sama da mutum 300 a tashar Telegram da aka buɗe domin horon.

Ɗanjaridan BBC ya samu shiga cikin horon, wanda aka ɗauki wata ɗaya ana yi ta intanet.

The list of course trainers included dozens of RT correspondents, among them the RT General Director, who is sanctioned by some Western governments for promoting Kremlin propaganda.

Asalin hoton, RT Academy website

Bayanan hoto, Masu horar da ƴanjaridar sun ƙunshi gomman wakilan kafar RT, ciki har da babban daraktan kafar, wadda ƙasashen yamma suka hana watsa labarai saboda yaɗa labaran ƙarya da farfaganda game da yaƙin Rasha a Ukraine.

Bidiyoyin horon - kusan guda 30 - an nuna ƙwarewa wajen naɗarsu, kuma a ɗakunan shirye-shiryen RT aka ɗauke su, inda a ciki manyan wakilai da manyan manajojin kafar suka horar da mahalarta.

An horar da ƴanjarida tun daga yadda za su tattauna da baƙi da nemo labarai da kawo rahoto da labaran kai-tsaye da aiki a wuraren rikici - inda suke suke ƙarƙafa ɓangaren Rasha tare da yin amfani da rahotannin RT a matsayin misalai.

A wurin kawo misalin ɗauko labarin kai-tsaye, an haɗa da rahoton RT daga garin Mariupol da aka mamaye, inda a ciki aka bayyana sojojin Ukraine da suke miƙa wuya da "maƙiya Yahudawa kuma masu tsattsauran ra'ayi."

A wani darasin, wani wakilin RT ya danganta labaran "kafofin watsa labarai na yamma da amfani da labarai a matsayin makamin yaƙi."

An kuma horar da mahalarta taron yadda ake gano labaran ƙarya.

The RT report from Russian-occupied Mariupol, where Ukrainian soldiers were labelled "neo-Nazis and radicals of all shapes."

Asalin hoton, RT website

Bayanan hoto, An nuna wa mahalarta horon rahotannin RT, ciki har da wanda aka ɗauko daga Mariupol da aka mamaye, inda a ciki aka bayyana sojojin Ukraine da suke miƙa wuya da "maƙiya Yahudawa kuma masu tsattsauran ra'ayi."

Masu gabatarwa sun sha maimaita labaran da suke goyon bayan Rasha.

Wani mai horar da ƴan jaridan ya ce harin ƙare-dangi da aka yi a Douma da ke Syria a 2018, wanda gwamnatin Bashar al-Assad wadda ke samun goyon bayan Rasha, "labarin ƙarya ne."

Sai dai ya yi kunnen uwar-shegu da binciken ƙwaƙwaf da hukumar yaƙi da amfani da makaman sinadari masu guba da ta tabbatar da harin, inda rahoton ya ce jirgin heliƙwaftan sojin Syria ne ya jefa sinadarin, wanda ya kashe mutum 43.

Haka kuma mai gabatarwar ya ƙaryata labarin kisan kiyashin da dakarun Rasha suka yi wa Ukraine a garin Bucha a 2022, inda ya bayyana shi da "sanannen labarin ƙarya."

Sai dai akwai tabbatattaun bayanai da suke tabbatar da kashe fararen hula a Bucha, wanda sojojin Rasha ne suka aikata, bayan hukumomi masu zaman kansu ciki har da hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi.

A still from the RT training course shows the RT instructor who repeated Kremlin falsehoods during a seminar on debunking fake news, falsely denying Russia's mass killing of Ukrainian civilians in Bucha.

Asalin hoton, Telegram channel RTschool

Bayanan hoto, Mai gabatarwar ya sha nanata labaran da suke goyon bayan Rasha, sannan ya ƙaryata labarin kashe fararen hula a Bucha.

Sai dai da alama wasu ƴanjarida da suka halarci taron ba su damu da labaran ƙarya da jami'an RT ɗin suke yaɗawa ba.

A wata tattaunawa da BBC, Dereje Yiemeru, wani ɗanjarida daga Habasha wanda alamu suka nuna yana ƙaunar shugaban Rasha - hoton Vladimir Putin ne a shafinsa na kafofin sada zumunta - ya amince da RT, inda ya ce labarin kisan kiyashin Bucha, "tsararren labari ne".

Ya ce ya shiga horon ne domin sanin yadda RT ke gabatar da shirye-shiryenta, da kuma abin da ya sa ta bambanta da sauran.

Shi ma Ishmael Koroma, wani ɗanjarida daga Saliyo, ya ce duk da yana ganin labaran ƙarya a matsayin matsala babba, ya yi amannar kowace kafa tana da nata ƙa'idojin.

BBC ta tuntunɓi RT game da manufar horar da ƴanjaridan, da kuma ƙarin bayani kan wasu bayanai da masu horon suka yi. Sai dai ba su amsa tambayoyin kai-tsaye ba, sai dai sun ce, "mun horar da ƴanjarida hanyoyin da za su gane farfaganda cikin sauƙi."

Mayar da hankali Afirka

A ƙarshen shekarar 2024, babban editan RT, Margarita Simonyan ya bayyana yadda "ƙasashen yamma suke cin mutuncin kafar RT a matsayin dalilan da suka fara mayar da hankalinsu da kuɗaɗensu zuwa wasu wuraren." Kasancewar RT ba ta da damar watsa shirye-shiryenta a ƙasashen yamma, sai ta fara neman hanyoyin da za ta gudanar da ayyukanta cikin kwanciyar hankali.

Kafar watsa labarai mallakin Rasha ta ruwaito cewa yanzu RT na watsa labarai a aƙalla ofisoshi bakwai a ƙasashen Afirka, sannan ta shiga yarjejeniya da aƙalla tasoshin talabijin na Afirka sama da 30 domin watsa shirye-shiryenta, da kuma ƙara faɗaɗa hanyoyin samun labarai daga ƙasashen Afirka.

Bayan watsa labarai da Ingilishi da Larabci, kafar RT ta kuma sake haɓɓaka sashenta na Farasanci domin ƙasashen Afirka masu amfani da yaren.

A promo graphic for RT’s program Lumumba’s Africa, which “focuses on past and current issues affecting the African continent.”

Asalin hoton, RT website

Bayanan hoto, Bayan hana ta rawar hantsi a ƙasashen yamma saboda yaɗa labaran ƙarya, RT ta ƙara ƙaimi wajen kutsawa ƙasashen Afirka

Da haɗin gwiwar fadar gwamnatin Rasha, RT ta shirya haska wasu shirye-shirye na musamman da ta yi game da Rasha a ƙasashen Afirka.

Shirin farfaganda mai taken "abin da ya sa na koma Rasha" ya nuna yadda Amurkawa suke bayyana dalilansu na komawa Rasha, inda a ciki wani ya bayyana cewa makarantun Amurka sun zama sansanin koyar da "haƙƙin jinsi" duk da cewa bai bayar da wani dalili ba.

Screenings of the pro-Russian RT documentary Why I Moved to Russia in Tanzania and Mali.

Asalin hoton, Telegram channel Rossotrudnichestvo

Bayanan hoto, Gwamnatin Rasha ta ɗauki nauyin haska shirye-shiryen na musamman a Tanzania (hagu) da Mali (dama)

'Hanyoyin isar da saƙo'

Ba RT kaɗai ba ce ta ke ɗaukar nauyin wannan horo ga ƴanjaridan na Afirka ba. China ta daɗe tana ɗaukar nauyin horar da ƴanjarida, inda take yawan gayyatar ƴanjarida zuwa ƙasar. Kafofin ƙasashen yamma - ciki har da BBC ma sun dade suna horar da ƴanjarida.

Philip Obaji Jr, wani ɗanjarida ne daga Najeriya wanda yake bincike game da ayyukan Rasha a Afirka, ya ce horon na cikin yunƙurin Rasha na canja yadda ake kallon ƙasar a nahiyar.

Bayan kammala horon, an yi alƙawarin za a nemi mahalarta taron duk lokacin da RT ɗin take neman ma'aikata.

Yevhen Fedchenko, shugaban ƙungiyar bin diddigi ta StopFake ya ce samun abokan hulɗa na gaskiya ta hanyar horar da ƴanjarida na cikin sabon tsarin Rasha.

"Za ka iya amfani da su (waɗanda aka horar) wajen yaɗa abubuwan da kake so, da canja tunanin mutane. Hakan zai sa su zama wakilan yaɗa bayanai game da Rasha."